← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 79

Sashe 31

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To lallai, ai dama kyan ɗa ya gaji ubansa. Matuƙar mutum ba zai iya adalci ba gara ya yi ɗayan."
"Haka ne, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar yana dariya da sosa kai tare da yin hanyar bangarensa.
Bayan ya biya Nahlin karatunta ya kalle ta lokacinnda take ƙoƙarin miƙewa ta tafi."Je ki kira Jannah ta fara karatu."
Jim ta yi kamar ba ta so aiken ba, sai kuma ta ije alkur'anin ta tafi sashin Hajiya Baaba.
Sallama tare da ƙwanƙwansa kofar ta yi."Uban mene ne za'a dame ni da sassafe?" Hajiya ta tambayeta ko gama wassakewa ban yi ba.
"Allah ya ba ki haƙuri, ina kwana."
"Da ban kwana ba za ki ganni, kinibibabbiya."
Cikin ƙubula ta kalle ta dama kamar ta san hakan zai faru shi ya sa ba ta so aiken ba."Ni fa bana son faɗa, Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu."
"Lallai yarinyar nan, kin raina ni. Ki kalli tsabar idanuna kice mini mafaÉ—aciya? Ko da yake ba laifinki ba ne, na san maganin abun ku..."
Maganar ta maƙale tunawa da ƙarshen abin da ta faɗa."Kika ce Ajmal ya ce a kira wa?"
Cikin rashin shakku ta furta bayan ta gyara tsayuwarta."Jannah."
"Oh, dukan da ya yi mata bai ishe shi ba, sai ya tsiri koya mata karatu don ya kashe saboda ba shi da uwarsa ba su da asara ko? To kije kice babu buƙatar hakan, ai yasan ni ɗin ba jahila ba ce zan koya mata. Wuce ki bani guri shashasha kawai."Juyawa ta yi tana hararta.
"Ɗan banza mara ta ido kawai." Ta ce tare da mai da ƙofar ta rufe, amma ba ta sanya key ba.
"Ya Ajmal, Hajiya ta ce ba za ta zo ba."
Miƙewa ta yi yana faɗin,"Ok." Ya yi sashin na ta.
Murɗa ƙofar ya yi ya shiga daidai lokacin da ta fito tana banbami."Ke Hafsatu, wallahi ki fita idanuna kin ji na gaya miki, ƙae dawowa ki ka yi kenan?"
Turus ta yi ganin wanda yake ƙoƙarin shigewa ɗakin Jannah."Wata uwar harara ta zabga masa.
Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu."Ma za zo ka fita, tun muna sheda juna, kafin muyi uwar watsi da kai."
"Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar yana nufar ɗakinta.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 13-14*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar tare da kai wa ƙofar wata uwar duka.
Cikin tsanannin tsoro ta miƙe daga baccin da take yi tare da zabga uban ihu domin ita a tunaninta ɓarayi ne suka zo, jin muryar Hajiya Baaba tana bambami ya sa hankalinta ya kwanta.
"Na shiga uku! Ashe gari ya waye ban yi sallah ba." Da sauri ta ƙarasa ƙofar ta buɗe daga ita sai figigiyar rigar bacci. Miƙa ta yi tana faɗin,
"Ni wallahi kin takurawa rayuwa kuma, gashi na buɗe bari na yi salla.." Maganar ta maƙale mata ganin mutum tsaye gefen Hajiya yana kallonta da take ta tsiya.
Ganin haka sai ta tsaya cikin tsoro tana zare ido, sai kuma ta janyo hijabinta ta sanya daidai lokacin da ta kalleta tare da zabga salati tana tafa hannu.
"Oh ni jikar mai gishiri, dama ba ki yi sallah ba, duk tashin da na rinƙa miki, kuma haka kike kwana sirara, so kike aljanu su shiga jikinki?"
"Haba Hajiya, ta ya ya za ki ce tsirara ba ki ga rigar bacci a jikina ba" Ta ce cikin ɓacin rai tana tura baki.
"Dalla gafara can, ina maraban dabbe da faɗa. Wannan yadin ƙyallen tatar kike kira kaya? "
"Ma za ki canza kaya ki fito daga yau karatu za ki fara da asuba, kuma minti goma na baki. Ya ƙarashe maganar zai juya ba tare da ya damu da abin da Hajiya Baaba take faɗi ba.
ÆŠago idanunta ta yi ta watsa mishi."Karatu kuma da asuba bayan na islamiya? Ni fa wallahi.."
"Ke shaye-shaye kike?"Ya tambaya cikin tsananin mamakin ganin yadda idanunta suka yi ja.
"iInna lillahi! Shaye-shaye kuma? Allah ba bu abin da na ke sha." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.
"A'a Jannatu, biri ya yi kama da mutum. Kalli idanunki kamar an zuba jar bula, ki faÉ—i gaskiya tun kafin na sa ya canza miki kammanni don ba zan zauna da yar nanaye a gidan ba."
Haushin maganar da ta faɗi ya sa ta saki kukan da take ƙoƙarin mayar wa.
"Na gaya miki ba na shan komai, energy drink ne fearless, don na rinƙa kallo da daddare saboda bacci ba ya barina kallo. Kuma ko Adal za'a tambaya don shi yake siyo mini."
"Wane irin kallo kike yi da har sai kin sha fearless, ke da kike shirin exam and do you know its side effects at this your age kina shan waÉ—annan abubuwan?"
"Me kenan take sha, ko dai kayan mayen ne? Su Jannah an yi kyan É—an maciji."
"A'a ba kayan shaye-shaye ba ne sai dai wani abu take sha don ya hana bacci, kuma yana da matuƙar illa a jiki. Ma za ki ɗauko wayarki na ga irin kallon da kike yi." Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan.
"A nan dai, kare ta kawai kake yi amma ka fito fili ka gaya mini tana kodimo. Kuma kallon da take yi na wasu mutane ne, da suke faɗin kucauu-kucauu na rantse ko ita ban jin ta san me suke faɗi. Ta yi ta sheƙa dariya tsakar dare ta hama ni sukuni, don ko hira ba ta yi dani sai dai ta barni kamar mayya." Ta ƙarashe maganar tana addu'ar Allah ya sa ya ƙwace wayar.
Juyawa ta yi ta shiga ɗauko wayar tana zabga mata harara sai ta ɗauko wayar ta miƙa masa tana zuɓɓura baki.
"Korian films ne, kuma ina fahimta don akwai subtitle da.."
"Can't you shut that mouth of yours?" Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan." Bai karɓi wayar ba ya juya ya fita yana faɗin,
" Ki tabbatar kin goge duk wani afilms dake wayarki. Ma za ki zo."
"Taɓ! Sannu ubana. Aikin banza kawai to goge ka yi, ai wallahi saina ɗauko ba kuɗi ba kuɗi ke aiki ba. Wayyo Allah har na ji tsoro kar ya ga chatts ɗina da Bud, yau da na shiga uku.
Galla mata Hajiya Baaba harara ta yi wacce take tsaye kamar tana son karanta abin da take faÉ—i a ranta.
" To 'yar zuga to babu abin da ya yi mini, na lura gabaki ɗaya kin daina sona." Ta ce cikin ɓacin rai za ta shige ɗakinta.
"A kan me zan so wacce ba ta san ciwon kanta ba? Ko ji dake da na ke albarkacin son da nake wa mahaifiyarki ne ya jawo haka, don gani nake kamar ita ne a gabana."
Ba tace mata komai ba ta ruga bayi tuna minutes É—in da ya bata. Wankan aguje ta yi sallar da ina aka tsareta ba za ta iya faÉ—in abin da ta karanta ba.
"Muje na raka ki, ba zan bari ya cutar mini dake ba amana ka bani."
Sai ta ji daɗin jin abin da ta ce don haka ba ce mata komai ba suka fice da ga falon.Guri ta nema ta zauna riƙe da jarbi tan ja.
"Ina kur'ninki?" Kallon shi ta yi jin abin da ya ce."
"Ba ni da shi, bari na É—auko app É—in a wayata." Ta ba shi amsa ciki-ciki.
Tsananin mamaki ya kamasa ganin tana musulma amma babu kur'ani ko É—aya a wayarta.
"Anty Jannah, ga kur'anina kiyi karatun da shi." Cewar Adal yana miƙa mata. Ƙarɓa ta yi tare da riƙewa batare da ta buɗe ba.
"Ke wai ina wasa dake ne? Za ki buÉ—e inda kike ki karanta." Ya daka mata tsawa yana faÉ—in haka.
Ni gaskiya, it been long I recited Kur'an. So I can't, just recite it to me kawai." Ta ce cikin kunkunai
"Jannah fa ƙasurgumar jahila ce, bana jin tana karatun sallah daidai, don duk lokacin da na takura mata sai ta yi ta motsa bakinta, wai ba ta iya karatu a bayyane ba."
" Please! Ni fa gaskiya ki daina kirana da Jahil.."
"Rufe mini baki banza kawai! Ƙarya na yi? Ai ni wallahi na ga sakarcin Halimatuu, da ta yi rainon ki kamar na tunkiyoyi, babu abin da kika sani sai fitsara da rashin kunya."
Ta buÉ—e baki za ta yi magana jin abin da ta ce ya daka mata tsawa ta yi shiru sai ruwan hawaye dake tsiyaya. Ta fakaici idanunshi ta zabga mata harara.
"Ban ga ana hararata ba sai idanu sun faɗi ƙasa." Ta ce tana jijjiga ƙafafunta ta ci gaba da jan carbinta.
Cikin ɓacin rai ta fara karanta suratul Amma da baƙinta da bai gama zaunawa a bakinta ba.
Chapter 31 · 0% Book details