← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 79

Sashe 67

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan, I will do the viser." Ya ce tare da ficewa ransa na ƙuna.

Nahlin da Ummu sai ta ba su tausayi sun sani duk wani abin da take yi da É—aurin gindin iyayenta da suka yi sakaci da rayuwarta.

Kuka take sosai kamar ranta zai shiɗe tana ganin sam iyayenta ba su da buƙatar haihuwarta, wannan dalilin ya sanya da suka haifeta suka tsaida haihuwar gabakiɗaya, domin rashin lokacin da za su kula da yayan, duba ga ita kaɗai da suka haifa sun yi wa rayuwarta riƙon sakainar kashi tana watangaririya cikin duniyar rayuwarta, saboda da sun tsaya sun kula da ita har yaushe za a laƙa mata wannan ƙaddarerrren auren

Ganin kukan ya ƙi ƙarewa ya sa Ummu ta ƙarasa gurin ta kama tana matuƙar jin haushin Hajiya Baaba da ta kafe sai anyi auren domin duk ita ta jagula komai, suna rayuwarsu cikin farinciki da annashuwa.

"Please sis, stop crying. Kina sa na ji kamar na yi. Kyakkyawar fahimta ya kamata ku yi tsakaninki da iyayenki." FaÉ—awa jikinta ta yi.

"Me zan fahimta ba sa sona kawai, dad ne kuma shi ma gashi za ta yi nasarar raba mu, honestly dad, is after money ba ya son ya bi zaɓina mom ta rabu da shi ya yi rayuwar talauci."

"No, don't say dad." Cewar Nahlin ta riƙe hannunta.

"Anty Nahlin mu bar gidannn yanzu zuciyata tana mini zafi, na tsane su ba na son zama a gidansu."

"Ki yi haƙuri mu bari zuwa goben." Ta ce tare da kama hannunta suka zauna.

Lallaɓata suka yi ta ci abinci Ummu ta shirya mata kayanta wanda dama duk iskancin da take yi da ya ji ba za ta koma Zariya ba sai da ta ci babu daɗi tana tunanin yadda za ta saba da tashinta.

Duk kiran da mom take mata ta ƙi ɗagawa sai dai suka yi waya da Nahlin da Ummu. Ta tura musu maƙudai suka je shoping, wanda ko tsinke ba ta ɗauka ba sai Ummu da in ta ɗauki abu, ta ke siya biyu tun da dama komai iri ɗaya suke sanyawa.

Washegari suka koma Zariya wanda Jannah tun da suka hau jirgin ba ta ce ƙala ba, tana ganin kiran dad da ya dame ta da text har da hotonsa ya turo masa da ya isa amma ba ta kalla ba.

Adal da Ummita suka rugo da suka rungume su suna faÉ—in,"Oyoyo Anty Nahlin, Ummu da Jannah."

Wani irin zabura Hajiya Baaba ta yi domin duk da ta san cewar su Nahlin za su dawo ba ta san da ita za a dawo va, sai Aby da Ammy kawai suka sani.

"Kamar su nan Jannah na ji an ambata a gidannan?" Ta ce tana kallon su Adal da suka ruga da gudu suna rungume su da suke fitowa daga cikin mota.

"Ke! Uban me ya dawo sake daga gidan?" Ta ce mta cikin tsawa.

Jannah da ta fito daga motar fuska kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa kallonta ta yi ba ta ce komai da troley É—inta za ta nufi sashinta.

"Tsaya na ce, ina za ki ai ba dai sashina ba?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai tana girgiza.

"Kin ga Hajiya Baaba, ki matsa mini na shiga babu ruwanki da ni."

"Akan me saboda ina jin tsoronki ko? Ko gidan iyayenki ne da kika raina kowa ba kya ganin kowa da gashi?" Ba ta ce mata komai ba ta matsa ta gefenta za ta wuce.

"Kin san Allah in kika ga kin shiga cikin ɗakin nan, sai dai in bani a gurin nan. Daga zuwa gidanku kika rinƙa suka mini rashin mutunci kala-kala ke mai iyaye. Shi ne yanzu kun ɓata kin sassaɓo jiki kin dawo gani tsohuwar banza na karɓe ki ko? To ba za ki zauna a ɗakina ba, sai in ki nemi wani gurin ko ki zauna da su Bimbo, ai dama idanu na zuba miki saboda iyayen na ki har wasu iyaye ne da za a yi togiya da su. Mutanen da basu da buri sai kuɗi. Ki ji da kyau auren da zan yi miki da Adamuu wallahi gata na yi miki, domin ba ki da kowa sai shi don haka ki yi masa biyayya."

Tsaki ta yi ta ƙara matsawa za ta shige.

"Au kin ɗauka wasa nake miki, bari ki gani."Ta ce tare da janyo ƙofarta ta rufe.

"Ƙyale ta Jannah, kin ji zo mu koma shashinmu da zama."

"Eh, can gasu gada, zomo ya ji kiÉ—an farauta. Ba dai É—akina ba fitsararriya kawai." Ta ce jin abin da Ummu ta ce.

Tafiya suka yi ba tare da ta ce mata uffan ba domin a mood É—in da take ba za ta ji kalmomi ma su daÉ—i ba in ta ce za ta kula ta.

Suna shiga sashin Ammmy ta rushe da kuka wanda Ammy ita ta zauna ta rinƙa rarrashi har ta yi shiru ta ci abinci.

Hutun kwana biyu suka yi na gajiyar dadowa suka koma makaranta da ake karatu babu kama hannu yaro don exam suke shirin farawa har ana ƙara fito musu da sabon time table.

Tun da suka dawo ba ta nufi shashin Hajiya ba kamar yadda ita ma babu ruwanta da ita domin da gaske fashin take da ita, amma ko muryarta ta ji sai ta leƙa ta ganta.

Bayan sun dawo da sati É—aya suka fara exam wanda hankalinsu ya koma kan jarrabawar gabakiÉ—aya ba su da lokacin kansu.

Zaman su ya yi daɗi sosai duk wani rashin kunya da iskanci da ta ke musu ba ta yi wanda kuma ba su nuna mata komai ba suka cigaba da zamansu lafiya. Nahlin ce wani lokacin ba ta shiga sabgarta don kar ta ƙara raina na.

Ranar laraba dukanninsu suna zaune a falo suna hira bayan sun kulle kansu a É—aki sun sha karatu na exam É—in gobe.

Ajmal ne ya yi sallama ya shigo fuskarsa a sake ganin Ammy zaune a tsakiyarsu ana hira da ita.

Jannah dake zaune kusa da Ammy kamar za ta shige jikinta ta É—ago daga kallon wayarta da take daddananwa ta kalle shi ta watsar.

Shigowarsa ya sa suka daina hirar da suke yi suna gaishe shi ban da ita da ta yi kamar ba ta san wata halitta ya shigo ba kuma yana lura da ita.

Zama ya yi gefen Ammy." Kwana biyu shiru har zan fara cigiyarka." Ta ce tana murmushi ganinsa.

"Eh wallahi Ammy, am on the go. Abubuwa sun cuÉ—emini ba ofis ba karatutttukan da nake da shi."

"Allah Sarki Ubangiji ya dafa ya yi albarka."

"Amin." Ya amsa cikin farinciki yana kallon 'yan ƙanninnasa da suka rame saboda exam.

"Ya exam kun ga yadda kuka rame kuwa?" Ya ce daidai lokacin da idanunsa suka sauka akan Jannah, wanda sai da ya ɗan saki dariya ganin yadda ta rame sai idanu zuru-zuru, domin abu abubuwa da dama suka ramar da ita, wanda rashin magana da dad shi yafi komai ƙara ramar da ita, amma saboda kafiya ta ƙi amsa calls ɗinsa duk lokacin da ya kira.

Sai ya tsinci kansa da kallonsa yana mamakin irin ƙarfin hali na Hajiya da ta danganta ta da shi, wai a matsayin matarsa, saboda in banda rashin mutunci mai zai yi da ita kamar sanda wanda ko ƙirjinsa ya ɗora mata sai ya karairayata. Shi ya ma manta da ita da maganar aurensu soyyayyarsa kawai yake sha da amaryarsa, don sai ya yanzu da ya ganta.

Wani uban harara ta zabga mishi har da sakin siririn tsaki domin wani mugun haushinsa take ji.

Ransa ne ya ɓace ya buɗe baki zai yi magana amm so Ammy ta yi mishi nuni da kar ya kulata da idanunta, wanda ya sa kan dole ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma zuciyarsa na tafarfasa.

Jin duk 'yan ɗakin sun ji tsaki da hararar da ta gi masa sai ta miƙe ta shige ɗakinsu domin t ji kunya da suka gani musamman Ammy da take biye mata tana taɓararta yadda ta ga dama, don har kwanciya a jikinta take yi.

"Ammy, kina ganin abin da yarinyar nan ta yi mini, amma kika yi mini nuni da na ƙyale ta."

"To kasheta za ka yi Ajmal? na ganta amma dole haƙuri za ka yi, domin karka manta shiga sabgarta da kake yi duk ya janyo aka maƙala maka aurenta."

"To ina gani sai ta yi ta zuba rashin kunya da fitsara, yanzu ki gani kamar ni za ta harara ta yi mini tsaki. Wallahi in ta ƙara saina tattaka ta sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita kanta Hajiyar yanzu saboda fitsararta korenta fa ta yi, amma saboda ni ba ni da gata za ta laƙa mini, ina zaman lafiya da mamata ta kawo mini jaraba, ita kanta ta san bamu dace ba."

"Ba ka da abin yi ban da wanda ya wuce addu' da fatan Allah ya zaɓa abin da yafi alkhairi, domin tun da ta furta sai wani ikon Allah."

"Kin san Allah Ammy ina ji ina gani ba zan yarda ta kawo mini jaraba da matsifa gidana ba, in kuma ta tilasta aka É—aura auren da kanta in ta gaji da zamanta za ta zo ta kwashi tsiyarta, saboda kallon banza ba za ta ishe ni ba."

"Akan me tana matsayin matarka kana malami haƙƙinta za ka ɗauka?" Cewar ta cikin ɓacin rai.

"Ba ni nace ina son auren ba dole za a yi mini." Ya ba ta amsa tare da miƙewa domin hirar ta gimshe shi.

"Ka dai yi abu da hankali ka rinƙa aunawa da mizanin hankalinka. Jannah yar'uwarka ce, ko babu aure akwai zumunci tsaka.."

"Ammy, zan wuce gida dama na zo kiyi mini addu'a akwai tafiyar da zan yi kuma khairan in sha Allah." Ya katseta yana faÉ—in hakan domin ya gaji da hirar.

"Ok, masha Allahu. Ina maka addu'a da neman buɗi da ɗaukaka a dukkan rayuwarka. Ko akan wananan maganar ce?" Ta ƙarashe maganar da tambaya.
"A,a ita ma tana kan hanya aci gaba da mana addu'a."

"Kullum babu dare babu rana muna yi fatan nasara."

"Amin." Ya amsa tare da ciro damin kuÉ—i ya ije kusa da ita.
Chapter 67 · 0% Book details