← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 79

Sashe 68

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ri na wuce anjima zan turo Kamal ya kawo muku kifi, saboda yau za a kwashe ba ki ga girman da suka yi ba, Mushiirat na ta mamaki don ba ta É—auka za su yi wannan girman ba."

"Masha Allah muna jira, duk da wanda aka kawo mana ma bamu gaba amfani da su basuna frij, ai gaskiya hannunka na da kyan kiwo ji kajin da aka kwashe wancan satin."

"Sun yi girman mamaki, ai albarkan da kuka sa mana ne." Ya ce tare da fara tafiya.

"Ai ko zamu ci gaba ka gaida Mushirat, ka ce na gode da tsaƙo Allah ya yi mata albarka, karka manta ka shiga ka gaida Hajiya Baaba."

"To." Ya ce tare da ficewa amma kuma bai shiga ba wanda tana ganin motarsa, da shigarsa tashinta har ya gama abin da yake yi, ya fito ya fita har leƙensa ta yi yana ta hararar shashin ya fice.

"Ni kake ma wannan wulaƙancin saboda zanyi maka aure, za ku ci ƙaniyarku da ga kai har ita." Ta ce tare da ɗaga waya ta kira wayar Aby wanda cikin rashin sa a ba ta same shi ba.

Fita ta yi ta bawa Musa Direba kuÉ—i ta ce,"Ka je ka siyo mini goro da tabarmai masu kyau da tsada ko nawa ne karka damu."

"To Hajiya, yanzu kuwa." Ya karɓi kiɗin yana mamakin me za ta yi dasu.

Bai jima ba ya dawo wanda ta karɓa ta adana su tana ta maganganu da habaici a sashinta wanda babu wanda ya jita don Ammy kwanciya ta yi.

Da daddare Aby ya dawo Hajiya Baaba ta yi kiransa wanda duk ciwon kan da yake fama da shi dole yazo.

Ganin uban goro da tabarmi sai da gabansa ya faÉ—i.
"Ah, Hajiya Baaba, waɗannan kayan fa? Na san na gaya miki iyayen manemin Nahlin sun roƙi abar maganar aurenta zuwa yaron ya dawon London ƙaro karatu da gurin aikinsa suka tura shi."

"Ba na son iskanci Muhammadu, nufinka Nahlin ce kawai mace budurwa a gidannan sauran ƙwailoli ka ɗauke su?"

"A'a Hajiya, na ga dai ita ce da muka san da maganar ta wani yana nemanta." Harararsa ta yi.

"Ka manta da maganar auren Jannnatuu da Adamuu, ko ka É—auka wasa nake?"

Ji ya yi gabansa ya ƙara faɗi."Na dai ɗauka kin yarda sai ita jannar ta yi nisa da karatunta shi kuma matarsa ta haihu ko ɗaya ne." Ya ce cikin rawr murya.

"Matarsa ta haihu aka ce maka haihuwar za ta yi, saboda inda haihuwar za ta yi da ko wata É—aya ba za ta yi ba yi ba za ta fara laulaluyi, tun da yanzu amaren yanzu kamar da cikin suke shiga, sai ka ga aure bai yi shekara ba an haihu hu. Matarsa juya ce ba haihuwa za ta yi ba."

Ya kasa magana sai kallonta yake yana mamakin ƙarfin halinta da maganar da take faɗi sai ka ce ta san gaibu, wanda ganin hakan ya sa ta ci gaba da cewa,

"To ban amince ba ta zane shi ko ta kashe shi in za ta so."

Kansa ya dafe ya duƙa ƙasa da gwuiwowinsa."Hajiya Baaba, ki wa girman Allah ki bar maganar nan zuwa wani lokac.."

"Ka fita idanuna Muhammadu, ka daina dawo mini da hannun agogo baya domin uren nan babu fashi. Ga ka kayan sa ranar nan, ka san na gaya maka ni zan yi komai, ko ƙwandalarku ba na son ku kashe, dama kuɗin da nake tarawa ban san me zan yi dasu ba, gara na yi aikin lada na samu lada, na sani ƙila ma shi ne zai sa na shiga al'jannah."

Shiru ya yi yana kallon kayan don ya rasa me zai ce.

"Za ka yi magana ne Muhammadu, ko ka mai da ni taɓaɓɓiya. Ka gaya mini nawa ne sadakin sai na biya."

"Na yi tunanin sai an zauna da yaran da kuma iyayen Jannah, musamman mahaifinta don bai kamata mu yi abu gabagaɗi ba, saboda yana da haƙƙi, kin ga dole ya gaya mana wanda zai naɗa waliyin Jnanh mu ne mu aurenta."

"To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka haka."

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 32-33*

*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*

*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka kace ina zuwa." Waya ta É—auka ta danna numbobin dad wanda yake zaune yana cin abinci.

"Hello Jabiru, maganar auren Jannah da Adamuu ne, waliyin da za ka na É—a nake tambaya saboda ina son asa rana."

Shiru ya yi ya rasa me zai ce a ransa yana tunanin ta dai na ce sai an yi auren nan.

"Ka yi shiru ko ba ka jina ne?"

"Abby ya zama waliyinta na ba shi wannan damar."Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinta.

"Saboda iskanci ya kashe mini wayaa ina sirikarsa ya manta lokacin da ya yi mini ƙarfa-ƙarfa aka ɗaura masa aure da Halimatuu, ashe babu daɗi ramuwar gayya."

Ta ƙarashe maganar tana kallon Aby da ya rasa bakin magana.

"Ai ka ji abin da ya ce ko sai na ƙra maimaita maka."

"A, a na ji ina son na kira abokina ya nema wa Ajmal auren."

"Shikenan, kira shi yanzu don ba zan tashi ba sai an saka rana ga sadaki da komai ayi mini kuɗin tsiya na biya, duk da mara kunyar ba tsada za ta yi ba saboda fitsararta, don duk wanda aka ba shi cutarsa ma aka yi, Adamun da yake ɗan gidane shi ya sa, saboda hannunka baya ruɓewa, ka yanke ka yar."

Shi dai baice komai ya É—aga waya ya kira shi sannan ya kalle ta bayan ya kashe waya.

"Hajiya Baaba, ya ce ga shi nan zuwa, bari na je na sha magani na ci abinci kaina ke ciwo."

"Ka je ina? In kaga ka jirka an sanya ranar nan ne, bari na É—auko maka maganin ciwon kan da abinci in da su. Yau abin da kafi so na girka gudun kurna, na gane wayon ka salon ka tafi a zuge ka ba."

Bai ce mata komai ya zauna har ta kawo masa abincin wanda ya kasa ci duk sonsa da gudun kurna sai dai ya sha maganin y koma ya zauna ya na tunanin lamarin.

Bai ɗauki tsawon lokaci ba Alhaji Umar ya shigo ya same su, zaune jugum-jugum babu mai magana sai Hajiya Baaba, da take kaɗa ƙafa fuskarnan babu ɗigon rahma, domin kamar ta fuskanci Aby ya yi masa text kan ya zo ya ba ta hakuri.

Jiki a saɓule ya samu guri zauna yana kallon Aby, da yake ƙyafta masa idon akan ya gwada sa arsa ganin yadda jikinsa ya yi sanyi.

Hajiya Baaba, ƙuta ta yi tana kallonsu ta gefen ido a ranta take faɗin,"Munafukai ku gama ina kallonku."

"Barka Hajiya Baaba, mun same ku lafiya."

"Alhamdulillahi, lafiya lau kamar yadda ka ganni, sai abokin na ka yake ciwon kai." Ta ce a daƙile ba tare da ta kalli inda yake ba.

"Ashsha! Allah ya kawo afuwa."

"Amin" Suka amsa da shi sai ta gyara zama ganin yana gyara baki da tunanin ind zai fara.

"Abokin na ka ya gaya maka komai ko. Maganar auren duk bana son ya wuce wata uku, saboda ni da za a yi cikin satin nan zanfi murna."

"Ki yi haƙuri dai abi sannu tun da ba sauri ake kuma, kuma Hajiya da kin ƙara duba lamarin."

"Dakata, na ce ka dakata wato kun haÉ—a baki ko? To babu ruwanka da shiga harkan zumunci, za ka sanya ranar ko ni na saka da kaina tun da uban 'ya ya amince."

"A'a ba za ayi haka ba, kai Umar sanya ranar kawai, amma don Allah ki yi haƙuri asa ta yadda Jannah za ta kai aji uku a makaranta."

"Wata uku na ke so kuma haka za a sa. Na ga kuÉ—aÉ—ena za su yi ciwo ba na ka ba, don haka ina ruwanka don an saka ko gobe ne."

"To shikenan, Allah ya ba su zaman lafiya." Ya ce tare da kama hannun abokinsa suka fita daidai lokacin da Hajiya Baaba ta amsa da.

"Amin." Sai ta ci gaba da cewa,"In ma ba su zauna lafiya ba, za su gaji su zauna domin auren nan mutu ka raba... Sai dai, ina mutu ku raba su, kuma ina sha Allah ina duniya har sai na ga jikokinsu." Ta ƙarashe maganar tana hararar ƙofar da suka fita.

Wayarta ta É—auka wanda bugu É—aya Halima ta É—auka saboda tun da ta tafi ba ta kirata ba, kuma ko ta kirata sai ta mula ta mulmule take amsawa shi ma iya gaisuwa ta katse wayarta

"Hello, uwata ta kaina macen da ta fi ko wace mace a duniya." Ta amsa tana mata wannan kirarin
Chapter 68 · 0% Book details