← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 79

Sashe 28

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

"Eh na ji kuma ta amince?" Ya ƙarashe maganar da tambaya.
Abby ya ce,"Ta amince da ƙyar, amma dad bai bata goyon baga ba, sai dai ka san in har ta amince babu wanda ya isa ya canza mata. Cikin satinnan zan je India na wakilce ta kan kasuwancinta."
Ajmal ya kalle sa yana faɗin,"Tana burge ni mace ce kamar maza, samun ta a ahalinmu abin alkhairi ne. Sai dai 'yarta sam ba ta ɗauko ɗabi'unta ba. She doesn't have table manners and she is so cheeky. Ga shi hajiya ta ƙarashe sangarta ta."
Aby da ya ji an tsokano masa inda ke masa ƙaiƙaiyi ya gyara zama yana faɗin,
"Yauwa, dama na bari ka dawo ne. Ka san yarinyar nan, ta daina zuwa islamiya? Har makarantar ta je ta mari malamin don ya duke ta."
Shiru ya yi, a ransa ya ayyana da zata iya fiye da haka, amma a fili ya ce,"Kai Hajiya sai addu'a. To yanzu bata zuwa kenan?" Aby ya ce,
"Eh, ta dage sai dai a canza mata wata makarantar, ko a ɗauko mata malami a gida. Kuma wallahi mahaifiyarta ta roƙe ni akan na bata ilmin addini. Don Allah ka yi wani abu." Ya yi shiro ko zaice wani abu, amma sai ya ga bai ɗauki maganar da mahimmanci ba, sai bin karatun kur'anin da ya kunna yake yi, wanda ganin hakan ya ci gaba da cewa,
"Ba zai yiwu na zura mata idanu ba, mahaifiyarta amana ta ba ni. Don haka dole na kula da ilminta kamar yadda zan kula da naku, kuma ko Halimatu ba ta da rai ni me riƙe ta ne. Daga yau na ɗora maka kula da ita."
Da sauri ya kalle sa jin aikin da yake son É—ora masa."Ni fa sam bana son shiga lamarin su, kasan Hajiya, ni kaina ba ta barni ba, da na yi magata zata fara mini gori a gabanta salon ta raina ni."
"Ya za ka yi, hakanan zaka jure ka yi don Allah, ai wani lokacin tana shakkarka " Jinjina kansa ya yi, don ya san aiki ne a gabansa.
Kasancewar ranar Juma'a suka yi maganar, don har ya manta a ranar sati, sai da ya ga Nahlin ta fito da zubbulelen hijabinta za ta tafi hadda ya tuna, har ta wuce shi ya dawo da ita ta hanyar ƙwala mata kira.
"Na'am Yaya, barka da hutawa." Ta ce tana ƙoƙarin ƙarasawa inda yake.
"Ke Nahlin ma za ki ce wa Jannah ta fito kuje hadda." Ta É—an yi jin sai kuma ta ce,
"To." Ta juya sashin Hajiya Baaba.
Ta same ta a ɗakinta ta kunna waƙa sai tiƙar rawa take yi.
"Ya Ajmal ya ce ki shirya muje hadda." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba da ita take yi ba. Tsawa ta daka mata wanda ya sa ta miƙe tare da tura baki.
"Haddar me? Babu inda zani." Ta ce cikin ƙunƙunai.
"Oho, ni dai tsaƙo aka aiko ni." Sai ta fara buga ƙafafunta tana faɗin,"Ni fa Allah ba zan koma islamiyar nan ba, wannan ai salon a raina ni ne, ina babban yarinya."
Mugun kallo ta yi mata sannan ta furta.
"Ki iya bakinki, wallahi Yaya ba sa'an yinki bane. Don haka ki natsu ki san wanda za ki yi wa, in ba haka ba sai ya canza miki halitta."
Ta turo baki."Tun da ga ubana ba." Jinjina kai kawai ta yi ta fice, tana mamakin tsaurin idanunta.
Tana isa gurin shi da yake ƙoƙarin shiga mota."Ya ta ce ba za ta je b.."
"What?" Ya katseta yana tambayarta da ƙarfi tare da daka mata tsawa wanda ya sa ta matsa cikin tsoro. Fitowa daga cikin motar ya yi ba tare da ya kashe ba."Lallai yrinyar nan ba ta da kunya zan koya mata hankali."
Buga ƙofar ya yi da ƙarfi ya shigo ga mamakinsa sai ya ganta a falo da remote a hannunta tana canza tasha, wanda ganinsa ta fara ƙunƙunai tana turo baki.
Ajmal ya tsaya cikin mamaki yana kallonta aransa ya ayyana da zaginsa take ganin yadda bakinta ke motsawa. Cikin fusata ya ce,
"Ke zagina kike yi don ubanki?" Mari ya kai mata a fuska tauu! Wanda ta ji shi har tsakiyar ƙwaƙwalwarta. Ta takura iya ƙarfinta ta canyara ƙara tare da kiran sunan Hajiya Baaba, wacce ta fito da gudu har tana tuntuɓe.
"Na shiga uku! Shalele, maciji ya sare ki, ko kunama?" Turus! Ta yi tana ƙarashe ɗaura zaninnta ganin wanda yake falon.
Da gudu ta koma bayanta ta ɓuya. "Hajiya Baaba, ya kashe ni mari hamsin ya yi mini. Wayyo na mutu! Dadddyyy."
Hajiya Baaba ita kanta ta san ƙarya take yi domin da haka ne wataƙila da wata maganar ake ba wannan ba, amma saboda rashin son gaskiya ta kurma salati da ihu tana faɗin,
"Kan uba, uban me ta yi maka da za ka fara dukanta kamar ka samu jaka?" Ta tamabaye sa cikin tsananin ɓacin rai tana girgiza.
"Gaya masa Hajiya Baaba, ko iyayena ba sa duka na ballantana wani ban.."
Ransa ne ya ɓace lokaci guda idanunsa suka canza zuwa wani kala, ganin tana shirin zaginsa a gaban Nahlin wacce ko magana yake ba ta iya kallon shi, sai kawai ya zare belt ɗinsa ya shiga zuba mata ta ko ina kuma iya ƙarfinsa.
Cikin azama Hajiya ta kai masa cakuma tana faÉ—in,"Ai ko yau sai na ga uban da ya tsaya maka da za ka duke ta."
Ture ta ya yi har ta buge da center table, amma ko kula ta bai yi ba, wanda ganin haka ya sa ta É—ora hannu aka ta yi tsakar gida tana ihu tare da faÉ—in,
"Na shiga uku, na lalace an kwaso mini dangin jaraba! Kai kan Muhammadu sam ba ka yi sa'ar zuriya ba. Jama'a ku kawo mini É—auki."
Ammi da ta fito daga sashinta da makullin mota tana sauri domin ta yi latti ta ji abin da take faÉ—i wanda ya sa ta yarda makullin tare da rugawa sashin cikin tsanin tashin hankali.
Wasu irin zafafan mari ta sauke masa."Ashe ba ka da hankali 'yar'uwarka za ka kama da duka haka saboda ga jaka ko?" Ta ce cikin zafi.
"Ai ko yau za'a yi ta a gidanan, wallahi sai ka yi sana-sanin dukanta." Cewar Hajiya.
Wani irin ƙululu ya ji ya taso masa cikin tsananin ɓacin rai ya kalli Hajiya Baaba yana faɗin,
"Kin yi kuskuren fifitata da kika yi akanmu, ki sani in ban yi ajalinta ba to sai na naƙasata." Ya juya zai fice daidai lokacin da ta ce,
"Za ka iya, ai zuciyarka kamar ta fir'auna take."
Jannah da ta ji duka rungume ta ta yi."Na shiga uku! Don Allah ki kira mom ta yi mini viser na koma ma London, if not he gonna kill me."
"Babu inda za ki, sai dai mu bar musu gidan. Shakuruminki shalele." Ta ba ta masa tana shafa bayanta.
Aby da ya shigo cikin falon a lokacin da zai fice wanda hakan ya sa ya fasa yana ajiyar zuciya a kai a kai.
"Yauwa, ma za shigo, ai sai da na gaya maka ka ja mana layi a tsakaninmu kaƙi, ga shi yanzu zai kashe mini shalele. Dole mu bar gidan nan, daɗin abin mahaifiyarta za ta iya siya mana duk irin gidan da muke so mu zauna ko a ketare ne."
Lamarin sai ya rikita kansa ya rasa ta ina zai fara." Tashin hankalin da kake so ka ja mini kenan Ajmal da sunan gyara? Kana jin mahaifiyata za ta bar gidana saboda kai."
Takaici sun na shi magana juya wa ya yi ya fice daga falon ba tare da ya ce komai ba, domin matuƙar ya ci gaba da kallonta, ƙila nan da minti uku, sai dai ayi maganar kai jana'izar gawarta . Zuciyarsa ta ɓace tsananin tsanarta ya ƙara shiga ransa sosai.
"Tashin hankali na nawa? Ai aikin gama ya gama. Barin gida ya zamar mini dole, ko kwana ba zan ƙara yi ba a gidannan."
Jannnah da ta ji duka ƙwaƙwarar motsi wahla yake mata. Ta kwantar da kanta kafaɗar Hajiyan Baaba da ko zama ta kasa yi, sai famar jijjiga take yi.
"Ya zama dole ka É—auki mataki in ba haka ba, watarana sai ya jawo mana tashin hankalinn da ba mu yi tsammann.."
"Rufe mana baki! Munafukar Allah. Ai duk tarbiyarki ce, da kika raini 'ya'yanki sakaka kamar kashi, ba kya iya tsawata musu. Ni da na isa da ɗana, kin ga ina ije kara ya tsallake? Ai ni an haɗa mana jini da jaraba." Ta ƙatse Ammy da take maganar.
"Ki yi haƙuri Hajiya maganar ba ta kai haka ba." Cewar Aby. Harara ta gallah masa."Ta ma wuce." Ta ba shi amsa.
Kamata ta yi suka nufi É—aki tana faÉ—in,"Shakuruminki kin ji shalele, babu inda za ki. Sai na ga uban da ya isa ya kai ki islamiyar."
Ganin ta É—auki waya tana neman numba ya yi saurin shan gabanta."Don Allah, kar ki kira Halima. Ni ma ina da iko a kanta, kar ki manta ciki É—aya muka fito."
"Sai na bari ya kashe ta ina gani ko?" Ta tambaye shi cikin ɓacin rai tare da shigewa ciki ta banko ƙofar da ƙarfi.
Dafe kansa ya yi, yana dana-sanin gaya masa, domin gashi yanzu ya ɓata goma biyar ba ta gyaru ba. Juyawa ya yi ya fita ganin kowa ya tafi ya barshi shi kaɗai.
Ajmal yana shiga ɗakinsa ya shige bayi. Ba tare da tuɓe kayansa ba, ya buɗe ma kansa shower yana ƙoƙarin tuɓe kayan, ya yin da ransa yake zafi zuciyarsa ke tafarfasa kamar za ta yi tsalle ta fito waje.
A maimakom ya yi hushi ya ƙyaleta sai ya saka a ransa sai ya ƙuntata rayuwarta don ya baƙanta mata da Hajiya Baaba da ƙiri-ƙiri take fifita ta akansu. Idon don kuɗi ne, ko kuɗin da yake da shi ba na Aby ba ya isa ta daina yi musu gorin sun ci da arzikinta.
Yana fitowa ya saka milk colour na jallabiya tare da ƙarasawa frig ya rinƙa banka ma cikinsa ruwan sanyi ko ya ji salama, amma da ya tuna abin da ya faru sai ya ji komai ya zaman masa sabo.
Wayarsa dake ƙara tun da ya shiga wanka ya ɗauka cikin ɓacin rai."Kin dame ni." Ya furta tare da daka mata tsawa.
Da sauri ta kashe wayar saboda tsabar tsoro jikinta har rawa yake yi."Na shiga uku! Wa ya taɓa shi?" Ta furta cikin jimamin tsawar da ya daka mata.
"Allah ya ba ka haƙuri. Ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni." Ta ce tare da ije wayar ta ci gaba da kwaɓin cincin ɗin da take yi.
"Hello Halimatuu, kina jina?" Hajiya Baaba ta furta."Eh in jin ki, Allah ya sa lafiya? Don na ji muryarki ta canza." Ta ce kamar ba ta san abin da ya faru ba, don Aby ya yi mata text É—in komai kafin ta kira wayar.
"Ina lafiya, an saci zanin mahaukaciya. Gida za ki canza mana ni da Janaatuu, wannan azzalimin yaron ya tashi..."
"Hajiya Baaba, na ce ki daina ce mini Jannatu. Kowa sai kin ɓata ɓasa suna?" Ta katseta cikin masifa cikin kaukausar murya.
Takaici ya kamata matsawa da wayar ta yi tana faɗin,"Ka ga mini ja'irar yarinya fitsarrariya! Ina neman miki mafita, amma sai kin nuna halinki, ai na gaya miki albarkacin 'yata kike ci da na bari ya miki dukan tsiya wallahi, na watsawa karnikan gidan ƙasusuwanki."
Murguɗa bakinta ta yi ta gyara kwanciyarta tare da ci gaba da kuka da ƙarfi da sheshsheƙa ta yadda mom za ta ji yo ta.
Mom da ke jin faÉ—an da suke yi sai ta shiga girgiza kanta a ranta tana tunanin za ta canza halinta na fitsara kuwa, ganin ko uwarta ba ta ragawa ba.
Tun lokacin da Aby ya sanar mata ta yi matuƙar murna da hamdala, domin ta fahimci tana buƙatar wanda zai gyara mata kuskuren da ta aikata, kasancewar ta gama raina su duka.
"Yauwa ki nema mana gida wanda zamu zauna daga ni sai ita."
Ajiyar zuciya ta saki tana jin yadda take shiga take fita da zage-zage da jawo masa jifa'i tamkar ba matsayinsu É—aya ba a gurinta wanda hakan bai yi mata daÉ—i ba, don ko ita ta ji wani iri ina ga kuma shi da iyayensa.
"Kiyi haƙuri Hajiya, su ɗin duka matsayi ɗaya suke a gurinki, kar ki sanya tsana ko rabuwar zumuncin su. Zan yi magana da Aby sai..."
"Ban san ke shashasha ba ce Halimatuu! Anya kuwa nonona kika sha? 'Yarki É—aya tal wacce Allah ya ba ki ake shirin kashewa shi ne sai kin yi shawara da ubansa? To shikenan, ki bari ya kashe ta, inya so kuÉ—in da kuÉ—in da kike tarawa, kinga sai ki bar ma duniya su..."
Fisge wayar ta yi daga kunninta don tana jin abin da take cewa.
"Na san ba kya ƙaunata. So I don't want you to prove it. You know? I'm not under age, and my dad has money so I can handle myself." Ta yanke kiran cikin ɓacin rai.
Baki ta buge mata."Ke kam ban san lokacin sa kika zama haka ba! Mahaifiyar taki kike wa tsawa tamkar 'yar cikinki?"
"Kyale ni, Hajiya ba ta sona ban taɓa yin abu na burgeta ba."
Chapter 28 · 0% Book details