← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 79

Sashe 41

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kansa Aby Hajiya Baaba ba ta barshi ya rintsa ba, don ya gode wa Allah da ya sanya na shi a garin abin ya faru da bai san halin da zai shiga ba.

Dad ya shiga matuƙar damuwa sosai, musamman da in ya kira wayarta ta gama ringin ba za ta ɗauka ba, wanda ya san dole akwai abinnda ya faru da ita, don ko hushi ta yi da shi duk inda ya yi kira biyu ba ta ɗauka ba to ana uku za ta ɗauka tana mita, amma har kira wanda bai san adadi ba ba ta ɗaga ba.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 17-18*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Ɓai taɓa tunanin yana da ƙarfin da zai iya tunkarar mom ya yi mata masifa ba. Ya kuma rantse in har wani ya samu 'yarsa ba zai ƙyale ba. Shiru ta yi masa don a yanayin da take ciki ba ta da lokacin da za ta kula shi. Ta san Ajmal ba mahaukaci ba ne da zai cutar da ita. Ko kaɗan ba ta ji zafi sosai ba, domin ta tsallake iya ta shiga har gidan mata ta mareta kuma ta nemi kashe ta saboda tsaurin ido da rashin kunya irin nata.

Washegari dole Aby ya dawo gida ganin yadda gidan yake ciki hankalinsa ya ƙara tashi sosai, domin da Hajiya Baaba da Ummu sun kwanta ciwo reras.

Ko hutawa bai yi ba ya bazama neman Ajmal. Kamar yadda ya rantse sai da ta kwana ta wuni sannan ya suka dawo gidan

Yana buɗe ɗakin da ya kaita Mushiirat ta sa ihu." Innalillahi! Na shi uku bab. Kar fa ka jawo mini ƙiyayyar dangin miji, kalli halin da take ciki."

Shi kansa ya matuƙar tsorata domin ta ɗauke dif babu numfashi. Kamata ya yi ya sanya a mota sai asibiti.

Drips aka ɗaura mata wanda ko minti biyu bai yi da fara shiga ta buɗe ido." Wayyo Allah! Dad, mom, na shiga uku. Wallahi ya Ajmal ba shi da imani." Ta ƙarashe maganar tana sakin gigitccen kuka.

"Ke ma za koma ki kwanta. Da ga yau sai ki gane bakin rijiya ba gurin wasan yara bane, don matata ba sa'ar ki ba ce. Mara kunya kawai." Ya daka mata tsawar da sai da ta ji 'yan hanjinta sun kaÉ—a, wanda ba bu musu ta koma ta kwanta sai ruwan hawaye ta ke.

Wani irin mugun tsanarsa ya kamata ji ta yi tamkar ta saka mishi guba ya ci a abinci ya mutu.

Sai da ruwan ya ƙare ya siyo mata abinci ta ci wanda ya yi mata dole ta ci. Ganin ramar da ta yi ya sanya ya ƙi mayar da ita gida, domin ya san in har Hajiya ta gan ta sai ta yi bandar namansa.

"Hello Ajmal, kana ina wane hali Jannah take?" Ya jera mata tarin tambayinsa.

"Muna asibiti ana ƙara mata ruwa."

"Ka san Allah in wani abu ya faru da yarinyar nan, sai ranka ya ɓace. Kuna da manya mai ya saka za ka ɗauki hukunci da kanka?"

"Aby, ka yi haƙuri yarinyar ba da ta tarbiya, ba ka ga yadda ta fasa mata kai ba, har sai da aka yi ɗinki."

Shiru ya yi don ya rasa yadda zai ɓullo ma lamarin don haka ya kashe wayarsa ya miƙe.

"Muje asibiti tana can ana ƙara mata ruwa." Ya fice da sauri gurin mota yana jin Hajiya na faɗin,"Mugu azzalimi, idona idon shi sai ya raina kansa."

Ko da suka je sibitin ba su same shi ba sai doctor Irfan da ya nuna musu É—akin da take.

Tana gainsu ta sanya kuka." Hajiya Baaba, kashe ni ya so ya yi, ba ki ga dukan da ya yi mini ba."

"Ki barshi da ni, daga yau babu ni ba bu har abada. Na tsani matarsa babu ruwana da shi. Dubi yadda kika rame da ke ma jiki ba."

Ummu ta rungumeta cikin muryar kuka, amma sai ta ture ta daga jikinta.

"Ni ƙyale ni, babu ruwana da ku. ba zan ƙara zama da ku ba, hostel zan koma."

"Haba shalele, don Allah kar ki gudu ki bar ni, ki tsaya kika matakin da zan É—auka."

Turo bakinta ta yi ba ta ce komai ba amma daga yau ta gama zaman gidan.

"Hello Sham, zan yi squatting a É—akinki kafin na samu nawa."

Cikin murna ta ce,"Are you saying the truth, za ki dawo hostel? Inda gaske ne sai kin zo, kuma akwai wata friend É—ina she is married woman, mijinta ya hana ta zaman hostel ya kama mata gida a gari, don haka zan yi mata magana duk da na san akwai waÉ—anda suka yi mata magana, amma ba za ta hana ni ba."

"Ok, ba ni da lafiya ana ƙara mini ruwa, kije ki tamabayeta sai na tura miki kuɗin." Ta kashe wayar.

Sai da ta yi kwana biyu sannan aka ba ta sallama. Duk yadda Hajiya Baaba ke rarrashinta kan ta yi haƙuri, amma ta ƙi ta tattara kayanta.

"Yanzu shalele guduwa za ki yi ki barni? Don Allah kiyi haƙuri ki bari kiga matakin da zan ɗauka."

"Kyale ni dama na gaji da zaman gidan zuwan Ummu ya sa na fasa, amma yanzu babu wanda ya isa ya hana ni."

Hajiya ta fusata ainun ganin tun safe take rarrashinta amma kamar tana tunzurata.

"To shikenan kifi ruwa gudu, Allah ya raka taki gona." Ta ce tare da balla mata harara ta wuce ɗakinta.Taɓe bakinta ta yi alamun ko a jikinta.

Ganin ta kwashi kaya sai ta fito ta saka kuka."Na shiga uku na banu! Adamuu ya raba ni da 'yar Halimatuu da nake ganinta tamkar uwarta. Allah ba zan yafe masa ba."

Ummu ta kama troley É—inta."Please don't go anyway, you know I can do without you."

Balla mata harara ta yi tare da janye troley É—in.

Sosai Hajiya Baaba ta riƙe jakar ta rantse babu inda za ta sai dai su tafi tare.

Ganin haka Aby ya ja ta suka shiga cikin ɗaki." Kiyi haƙuri ki kyaleta, inta huce za ta dawo. Kuma kin san zamanta a nan ba zai ɗore ba. Gidan Halima an gama komai, kawai dawowarsu ake jira. Kinga dole gidan iyayenta za ta koma.

"Ba bu yadda zan yi ne, amma wanann mara mutuncin ya cuce ni."

Kafin ma su fito ta fice wanda hankalin Ummu ya tashi ta saka a ranta ita ma dole ta koma zaman hostel don ba za ta iya rayuwa babu ita ba.

Tun da lamarin ya faru ta ƙi ɗaga wayar mom domin gani take duk ita ta ja mata shiga wannan halin. Ta yi kiran duniya amma ta ƙi ɗauka, haka ta tura mata tsako ko kallon numbarta ba ta yi.

Sai zaman hostel É—in ya yi mata daÉ—i. In suka dawo daga lecture library take wucewa ta yi karatu sai yamma take dawowa. Abinci kuwa ba ta girkawa sai dai ta siya.

Ko sati ba ta yi ba Ummu ta haÉ—a kayanta ta biyo ta, wanda ta yi murnar hakan don ita ma ta san fushin da ta yi da ita na É—an lokaci ne, amma she could not do without her.

Karatu suke yi sosai babu kama hannun yaro domin they have future accomplishment and they want to accomplish it."

Zaman hostel É—in ya sa suka É—auki wasu É—abi'u suka É—ora ma kansu. Zuwa party da kitson attach. Hijabi kuwa sai dai in za su yi sallah, don wani lokacin hakanan za su sha gayu su É—auki littafansu su tafi hostel babu mayafi, don cin kararsu suke babu babu babbaka.

Shirye-shiryen jarrabawa da ya tunkarosu suka mai da hankali babu dare babu rana, kullum cikin kratu suna library.

Cikin sa'a suka kammala jarrabawar. A tunanin Ummu Jannah za ta biyo ta su je hutu, amma sai ta ji saɓanin hakan. Ta kafe kan Zey za ta bi hutu zuwa gida.

Hankalinta ya tashi ƙwarai don haka ta ɗauki wayarta ta sanar da gida abin da ke faruwa.

Aby cikin ɓacin rai ya kira wayarta, wanda tana ɗauka ya fara magana cikin ɓacin rai,"Hello Jannah, in har ba kya son ranki ya ɓace, kafin na dawo aiki na ganku a gida ke da Ummu."

ÆŠif ya kashe wayar ya barta sagale da ita. Kallon Ummu ta yi ta banka mata uwar harara.

"Munafuka na san ke kika faÉ—a masa." Ta ce mata tana jan troley É—inta.

"Haba sis, ke ma kin san bai kamata ace ga gidammu ba kin tafi wata uwa duniya hutu."

"Kiyi mini shiru tun da kin haÉ—a ni da shi sai ki tashi mu tafi burinki ya cika."

Dariya ta yi tare da miƙewa ta ja troley ɗinta suka fito.

Ba ƙaramin frin ciki Hajiya Baaba ta ji da ta ganta ba. Har da kukan murna ta rungume ta.

"Ba ki da kirki kwata-kwata har ciwo na yi amma ba ki zo ba."

Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba don har yanzu hushi ta ke yi.

Tun tana bonewa har ta gaji ta saki ta kama harkanta.

Hutun ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba musamman yadda take nan nan da ita, kuma tun da ta sawo ba su yi faɗa ba.

Suna zaune ana hira Hajiya Baaba na gefenta da goro a hannunta. Ɓalla ta yi ta saka a bakinta, sannan ta ɗauki lakasera ta kurɓa ta ije tana kalloon Jannah da take ɓata fuska tamkar za ta yi amai.
Chapter 41 · 0% Book details