← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 79

Sashe 34

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jannah ta dage tare da saka ɗamarar koyon karatun. Kullum cikin dare ba ta bacci sai da ta ga taniya haɗa baƙin sosai ya zauna a kanta. Haddar ne tasha matuƙar wahalansa saboda ko ta fara sai ta ji ta gaji, amma da ta jajirce sai ga shi cikin wata biyu ta basu matuƙar mamaki. Washegari da safe, duk tashin da Hajiya Baaba ta yi musu ba su tashi ba, sai misalin bakwai saura minti goma. Jannah sallah ta yi wana tana sallame wa ta ɗauki bagadadi ta fara karatu, sakamakon ba su da karatun asuba saboda ya yi tafiya. Ummu ta yi sallah bayan ta idar ta yi karatun alkur'ani da azkar sannan ta koma ta kwanta don har yanzu gajiya bai sake ta ba, ga shi ba su yi wani baccin kirki ba. Cikin lokaci ƙalilan ta shayar da kowa ruwan mamaki, domin ta nuna musu sa kai ya fi bauta. Sosai ta iya karatun shi kansa Ajmal mamakinta yake yi, wanda ya gane iskanci ne da rashin mayar da hankali ta sanya wa rayuwarta, wanda ganin hakan ya fara mata harda daga baƙara, kuma tana ƙoƙarin kawo masa daidai iyawarta. Dawowar Ummu sai ya ƙara mata jin daɗin zaman gidan. Kusan halayen su ɗaya, sai dai Ummu tana aiki kuma da don ita take yi wa kanta komai, saɓanin Jannah da sai dai ta ci tasha ta kwanta tana kallo ko ta hau ynar gizo. Sun yi matuƙar shaƙuwa tamkar 'yan tagwaye suke. Ummu ta bata shekara ɗaya amma in ka gansu sai ka ɗauka shekarun sun fi haka, don ita tana da jiki, yayin da Jannah ba ta da wani jiki siririya ce sosai. Tun Hajiya Baaba na kauda ido akansu har aka kai mizanin da ta kasa haƙura ganin shaƙuwarsu, don ba ta ƙaunar hakan wanda ya sanya ta fara ƙorafi. Duk lokacin da Jannah ta tafi sashin su za ta bita ta taso ƙeyarta bayan ta yi ƙorafi da zage-zage, amma kuma ba shi zai hana anjima ta koma ba, wanda har ta gaji ta zura musu ido domin daga baya sashinta suka koma da zama gabakiɗaya. Ranar lahadi bayan sun taso hadda suna har suka iso cikin gidan. Kai tsaye sashin su Ummu suka nufa sakamakon yunwar da suka dawo da ita. Tsaki Ummu ta yi tana faɗin,"Kai na san Anty Nahlin ce, da wannan kinibibin tsiyar ta yi mana gudun kurna. Wallahi na tsani abun nan." Taɓe baki ta yi bayan ta buɗe kular."Taɓ, ni fa ban taɓa ci ba, ranar da Anty Nahlin ta yi sai dai na sha tea." Ta mayar da kular cikin ƙyanƙyani. "Let's go to Hajiya's kitchen to see what she cooked. I'm starving to dead." Ta furta tare da jan hannunta suka kama tafiya sashin ta. "Allah ya kyauta! I can't eat that concoction." "Ok, then let's go and cook." Ta faɗa tana rufe ƙofar kicin ɗin. "Allah ya sa ta yarda Hajiya is so abrasived." Dariya Ummu ta yi ba ta ce komai ba suka nufi sashin, wanda kai tsaye kicin Ummu ta wuce yayin da Jannah ta zauna a kan kujera. Harara Ummu ta sakin mata tana faɗin" What this sis, kamata ya yi ki biyo ni kicin ki gyara kayan miya kiyi blending, ko kuma mu jajjaga zai fi ko?" Ta ƙarashe maganar cikin sigar tambaya. "Allah na tuba! Muje dai na taya ki hira, amma ni har yanzu ban gama sanin kalar kicin ɗin nan ba, ballantana na yi girki don ban iya ba." "Wai da gaske kike?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki sosai. Jinjina mata kanta ta yi suka nufi kicin ɗin. "Ban ga laifin ki ba sis, ai duk wanda ya samu rana ya yi shanya. Rayuwar hutu daɗi ne da ita. Ke ɗin babbar yarinyace, Allah ya tarfawa garinki nono." Ta ɗauki tukunya ta ɗauraye sannan ta kunna gas tana kallonta."Lokacin da na ji mom na neman minister I was very happy. Allah ya yi miki tagomashi da ya ba ki uwa irin mom." "No, please stop saying that. A kan mom kike cewa na ji daɗin samun ta a matsayin uwa, kin san wace ce ita? Ai ni mamaki na ji da take neman wannnn kujerar matar da ta kasa kula da gidanta za a ba wannan muƙamin! Initially, I was thinking my dad wasn't aware of this and he won't support her, amma kin san ta Mai da shi rakumi da akala." "You don't support you mom in to politics, do you?" Ummu ta ce cikin tsananin mamaki abin da take fadi. "Absolutely, I do not." "A lallai na raina wayonki, kin san kuwa wace ce ita.." "Oh, please. I don't wanna talk about her now, understand? Kawai na ije ta a matsayin bankina, in ina buƙatar kuɗi ta turo mini. That what she is to m.." Jin abin da ta ce ta kuma canza fuska sai ba ta ce komai ba suka ci gaba da ɗor girkin bayan sun gama suka dawo falo suna kallo. "Innalillahi na shiga uku! Dan ubanku gobara kuke son ku haɗa mini, kashe ni kuke son yi ko? Waton na mutu na bar muku duniyar ku ci ta da tsinke."Hajiya Baaba take faɗi tana fito .daga ɗakinta, wanda jin abin da ta ce suka kwasa da gudu zuwa kicin ɗin domin sun mnta sun ɗora girki. "Mun shiga uku! Ya ƙone." Cewar Ummu da ta kashe gas ɗin ta buɗe murfin tukunyar tana kallon haɗaɗɗiyar tliyar da suka dafa ta ji bashshshen kifi sai ƙauri take yi. "Taɓ! Ai wallahi ba zan yi asara ba haka kawai. Ban ci nanin ba nanin ta ci ne. Na rantse iyayen ku za su biya. Ma za Jannatu ɗauko mini wayata a ɗakina na kira uwarki ta siya mini tukunyata, ke kuwa Kursumu ubanki zai biya ni abincina." "Ki kwanatar da hankalinki daɗin abun mu ɗin ba matsiyata bane da sai kin kira iyayenmu kiyi kuɗin tsiya na biya ki." "To ƙaramar mara kunya fitsararra. Ai dama na san ke za ki fara magana. Fita a kicin ɗin tunkafin na yi ball dake, tund ba ubanki ya saya mini gidan ba. Kin ji da kan ki kamar tsandar rake." "Aby da mom uwa ɗaya uba ɗaya suke, don haka nima ina da iko da gidan." "Ok haka kika ce ko? To ba ri na zo kusa dake zan fi gane maganarki, don kamar ba da yaran da na sani kike magana ba." Ta ƙarasa maganar tare da ɗauko muciya ta yi kanta, wanda gain haka ta kwarma ihu ta yi waje. Kan Ummu ta yi da take tsaye tana mamakin tsaurin idanunt do ko Ya Ajmal ba y gaya mata magana ya kwana lafiya. "Fita daga kicin ɗin nan, kema wallahi na ƙara ganinki sai na canza miki kamanni." "Taɓ! Ai in dai Jannah tana sashin nan, sai dai kiyi haƙuri ko ki barta mu koma sashinmu za mu fi sakewa." ta ƙarashe maganar tare da zurawa da gudu, Jannah ta rufa mata baya tana faɗin, "Muje kin ji ni ma ba zan ƙara dawowa ba, na huta da tashina da asuba da take yi kamar me kashin kwance." "Oh Allah na ga ta kaina! Ni kam an haifa mini jikoki sun zamar mini ƙadangarun bakin tulu. Da na yi magana ɗaya sai sun mayar mini da goma." Jarrabawar makarantarsu yake ta matsowa na fita daga sakandiri. Hnakalinsu gabaki ɗaya yana kai ba kamar jannah da ko abinci ba ta iya ci sosai kullum karatu duk ta bi ta rame. Inda suka ɗan samu natsuwa da ana saura kwana goma su fara za a yi bikin Ajmal sai kuma aka ɗaga sakamakon mahaifin Mushiirat da ba shi da lafiya an fita da shi waje. Cikin nasara suka gama zana jarrabawar wanda har sai da ta kwanta ciwo bayan exam ɗin sai hankalinsu ya koma kan bikin Ajmal da za a yi wanda aka ƙara wata biyar. Tun kafin ya matso suke shiri da murna da tsare-tsaren shagalin da za su yi ranar auren. "Na ɗauki nauyin haɗa paty da ƙawayenmu ranar auren don murnar zai bar mana gida muci karenmu babu babbaka. Wayyo Allah har na ga irin rayuwar da zan yi, ga shi lokacin mun shiga higher institution, kai akwai bidiri." Jannah ta ce wa Ummu da take kwance a kan kujerar da Jannah take zaune. "Habawa ke dai bari. Allah dai ya kai dare ga hawara, ko bai ci ba ya yi birgima.Kin san Allah in yaya ya bar gidan nan, akwai kankaro mutunci. Wani irin shiga zan rinƙa yi na mata masu class ina zuwa makaranta." "Ki dai bari kawai! Duk na ƙosa Jamb ɗinmu ya fito. Dole mu hau mota masu kyau, kuɗin mom zai yi kuka." Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa sannan suka fice daga falon zuw ɗakinsu. Suna zaune suna kallo Hajiya Baaba ta shigo da kwanon fura a hannunta ta ce, "Ke Jannatu, maza ki kaiwa yayanki Adamuu hurar nan, yau isasshen ya tuna da hurata mai daɗi." "Ni fa Hajiya kin san ban cika son aike ba, haka kawai ga 'yan aiki sai kin wahalar da ni, kuma kin san halin jarabben mutun nan so kike na je ya ce n yi masa wani abu..." "Ta shi ma za kije, sai kin kai mishi banga damar aiken wani ba sai malalaciya kawai, ke Ummu ta ki rakata." Miƙewa ta yi tana zumɓura baki kamar za ta zubar ta fice. "Ke kin san Allah ba zan raka ki ba, yau ikin da muka yi masa daban ne, ka wo wayarki ki same ni a sashinmu."Ta wuce ba tare da ta tsaya ta ni ƙorafin da take mata. Da siririyar sallama ta shiga cikin falon amma ganin ya juya baya yana waya bai ji ta ba sai ta ja ta tsaya tare da maƙala kunninta sosai yadda za ta jiyo shi jin ya rage murya. Cikin salo da jan hankali duk wata 'ya mace yake waya. Dariya ya saki mai sauti yan lumshe idanu, wnda ya ba ta matuƙar mamakin jin yana da irin muryar. Hankalinsa gabaki ɗaya ya tattara akan wayar don har wani takun ƙasaita yake yi a hankali a tsakiyar falon. Cikin wata irin murya ta ji ya ce,"Buɗe bakinki na
Chapter 34 · 0% Book details