← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 79

Sashe 45

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun yi hadda suka dawo bacci suka koma sai gurin sha biyu suka tashi saboda jiya sai ƙarfe uku suka kwanta.

Suna zaune a falo suna kallo Nahlin ta ƙara shigo wa."Kenan kun sa zan rinƙa safa da marwa tsakanin sashin Hajiya da namu. Ku ba kwa tunanin sai an yi muku. Sai ku zo na koya muku abinci. Ina ga kawai mu yi shi a matsayin abincin rana."

"Lallai m Anty Nahlin, É—an abincin da zamu koya wanda bai wuce na gwangwani biyu ba, shi ne za ki wahalar damu. Gaskiya ya haka Yaya ce ba."

"To shikenan, marasa son moriya ke Ummu wallahi kin shiga uku, da bakinki kike faÉ—in hakan. Na ji nice baiwa a gidan nan, mu je na koya muku kaÉ—an ni sai na yi abincin gidan. Mijina ya huta kuna ganin wahalar da kaina nake yi ko?"

"Mu ma na mu ai bai ce miki wahala zai sha ba tun da akwai restaurant Kuma da kuÉ—i." Jannah ta ce tare da canza tasha zuaa wanda suka ga ana kallo.

"Hmm, Allah ya kaimu lokaci zai nuna. Kun É—auka zaman auren film ne, da daÉ—in bakin da suke muku ko."

Shiru suka yi ba su ce mata komai ba.

"Mu je kicin É—in Hajiya Baaba ba sai mun je sashinku ba." Cewar ganin sun yi hanyar fita Jannah tare da nufar kicin É—in.

"Kin san halin Hajiya Baaba kar ta samu da masifa."

"Muje mana ba iyayenmu suka tsiya ba? Ni wallahi ko kaÉ—an bana tsoronta." Bin bayanta suka yi suka nufi kicin É—in

A kicin É—in ta dage sai yi musu bayani take yi amma hankalinta ba shi a kanta yana wayarta da take duba chatts da Huzaifah ya yi mata.

"Jannah kina jina? Don na lura you mind isn't here." Nahlin ta furta.

Ije wayarta ta yi ta ce," Anty Nahlin stop waisting your time for the explanation. Kin san with the advanced of technology everything is easier. So you don't need to explain just give me the recipes."Ta ƙarashe maganar tana ɗora tukunya.

Baki Ummu ta buɗe cikin mamakin ƙarfin halinta."Uban me za ki dafa, wallahi kin san kika haɗawa Hajiya gobara ko kika ɓata mata kayan abinci za ki sani. You that when we were in hostel ba ta taɓa girki ba."

"Then wait and see, I will search everything on YouTube and watch. Yau za ki ci abincin da baki taɓa ci ba. Believe me sis, you will really enjoy it" Ta ce tare da balla mata harara.

Baki ta taɓe tana faɗin,"I see, yau mata za su yi girki. I can wait to see."

"To shikenan, if you insist. Bari Ummu sai muje sashinmu ta yi acan." Ta ce tana ƙoƙarin fita don ta ba ta haushi.

"Su waye a kicin É—ina ba na hana shiga ba don wallahi ban yadda da ku ba, saboda tun da kuka dawo ake mini satar nama. A da sai na yi sati da miyata cike da nama, amma yanzu ko kwana É—aya ba ya yi."

"Allah ya kyauta mun fi ƙarfin satar naman miya sai dai muci."Ummu ta ba ta amsa lokacin da ta ƙaraso.

"Gaya mata sis." Ta ce lokacin da take ƙoƙarin kuna gas.

"A keee! Dakata karki haÉ—a mini gobara. Uban me za ki yi?"

"Girkin da kullum kike mini gori zan fara daga yau, saboda bana son na yi aure ki bini gidan mijina ki rinƙa mini tereren ke kike wa mijina abinci."

"Au to rasai, amma ba da kayan abincina ba ko?" Ta tambayeta jin abin da ta ce.

"Kin ga Hajiya Baaba, ki ƙyale ni karki ki sanya na manta abin da na kalla kuma."

"Yau na ga lukutar matsifa, ke da ba ki iya ba shine za ki ce rana tsaka za ki koya? To bari mu gani in tusa na hura wuta, an gaya miki girkin wasan yara ne. Kuma kika ɓata mini kayan abinci aljihun uwarki zai yi kuka." Ta ce tare da juyawa ta koma falo.

Bayan fitarsu ta gama ƙarewa gas ɗin kallo amma ba ta ga inda zata kunna ba.

"Talatu." Ta yi kiranta cikin raÉ—a tare da yafito ta da hannu.

"Na'am ga ni Hajiya." Ta ce lokacin da ta shigo kicin ɗin bayan Janah ta rufe ƙofar.

"Ki kunna mini gas ɗin nan." Ta miƙa mata ashana.

"Ai ba da ashana ake kunnawa ba, ashanar na kunna gawayi ne da Hajiya Baaba ke sanya turare."

"Oho, kunna mini to." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Talatu da take mata wami irin kallo ba.

"Kin ga yadda za ki yi nan Hajiya, ya kamata ki koya ko don nan gaba."

"Please don't lecture me, cewa kawai na yi ki kunna mini. Ce miki akai kuku nake karanta. Zan nuna ma mutanen gidan nan ni É—in na iya kawai ba na son na yi ne. Allah na tuba girki har wani wahala yake da shi. Na san is so simple as eating food. Dallah ni in kin kunna fita ki bani guri." Ta daka mata tsawa tana faÉ—in haka.

"Allah ya ba ki haƙuri." Ta ce tare da ficewa da sauri.

Ba ta ce komai ba ta ɗaura tukunyar tana 'yan waƙe-waƙenta da rawa.

"Umh, kamar na ga fa ta soya kayan miya ko?" Ta yi wa kanta tambayar a bayyane. Gnain ba ta tuna ba ya sa ta ƙara kunna video.

"Wayyo Allah ta soya kuma wallahi ni kam ba zan tsaya jira ba saboda am eager to start watching queen of tears, ga wan can jarababben ya sa mu hadda."

Sai kawai ta diddila mangyaÉ—a iya son ranta tare da kayan miyar ta kwara ruwa.

"Bari na saka mangyaɗa da magi yawa saboda nawa yafi na Ummu daɗi." Ta ce tana rawa da ƙafarta. Ta zuba magi da yawa gishiri ne ba ta cika ba.

Ruwan na tausa ta ibi shinkafar da tafi ƙarfin ruwan ta zuba ta juya ta mayar ta rufe tana shaƙar ƙamshin girki da ya ji uban spices har da wanda tea Hajiya take haɗawa da shi.

Mintinan da ta ga wacce ta yi girki a yourtube ta bawa girkinta ta iba sannan ta kira Talatu ta kashe mata gas É—in ba tare da ta duba girkin ba.

"Na shiga uku Hajiya Jannah, kar dai har kin gama."

Wata uwar harara ta banka mata."Ni fa na lura dake muguwar munafuka ne, don ina zargin ke kike ƙara haɗa ni da Hajiya Baaba a gidanan, saboda shekaranjiya a gabanki na ibi nama yanka tara."

"Innalillahi! Don Allah kiyi haƙuri wallahi ba ruwana. Sam ba na shiga sabgar 'yan gida. Na dai tambaye ki ne saboda na ga ko kifin da kika sa na wanke bai isa dahu ba, ballantana naman kayan ciki masu tauri."

"To sannu 'yar iya sai ki koya mini girki ni da na koya a yourtube, kuma awannin da ta yi amfani da shi da shi na yi nima. Ke da kike baƙauyiya dake ji be ki fa, har wani girki za ki koya mini."

"To ai gas É—in kaÉ—an-kaÉ—an kika saka yake ci fa."

"Dallah ni fita kiban gurin tun da kin gama mini amfani." Ta daka mata tsawa tana faÉ—in haka.

Bayan ta fita kuma sai dawo da ta hankalinta tare ta tuna yadda gas ɗin mi girkin yake ci. Da sauri ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe tana kallon shinkafar da ta tokare tukunya ta yi cikin shige ga mai shanana.

"Na shiga uku." Ta faɗi tare da mayar da murfin tukunyar ta rufe. Leƙawa ta yi za ta kira Talatu daidai lokacin da su Ummu suka shigo kicin ɗin.

"By the looked on your face, I guessed you cooked delicious food." Cewar Ummu cikin tsokana tana ƙoƙarin ƙarasawa gurin tukunyar.

"I can't wait saboda tun ina waje nake perceiving the aroma ina ta salivating."

"Oh yes I do, ki bari I will serve you."

"Wai me kika dafa? Na ga ko Ummu da te girka taliya har yanzu ba ta gama ba, mun bar wa Jummala ta kula da shi?" Nahlin ta tambaya cikin mamaki.

"Fried rice na yi."

Tare suka haÉ—a baki gurin faÉ—in,"Fried me?"

Ummu ta ƙarasa cikin mamaki ta buɗe tukunyar.

"Kan uba, yau ke da Hajiya Baaba wannan abinci da kika tokare tukunya da s.."

Maganar ta tsaya mata a maƙoshi sakamakon ɗanɗana shinkafar da ta yi. Da gudu ta ruga sink ta buɗe famfo tana watsa ruwa a bakinta bayan ta furzar da abincin ta wanke bakinta.

"Haka ake girki? Aiko da tuni mun mutu. Jakar magi kika juye?"

Tsaki ta yi tana faÉ—in,"Ban sani ba." Ta tureta daga gurin tukunyar.

"Taɓ! Duk wanda ya ci abincin nan sai dai ya kwana a cikin bayi."

"Jannatu, wane irin girki kike yi? Gida ya cika da ƙarnin nama."

"Girki mai daÉ—i Hajiya Baaba, ma za shigo kar ayi babu ke yau mata sun yi girki, in dai kika ci wannan girkin sai kin suma." Nahlin ta ba ta amsa.

" Allah ya tsareni girki ko shiririta dai." Cewarta ta tana buÉ—e tukunyar.

"Innalillahi! Ni jikar maigishiri wannan tsunburen da kike yi fa? Ai wannan albazaranci ne. Ni dama na san babu abin da za ki tsinana shegen kafiya ce dake."
"Ni fa ba ni da laifi iya yawan da nake so na shinkafar na zuba, shinkafar ne ta kubburo."

Kwashewa da dariya suka yi." Wai yanzu sis kina nufin baki san in aka aka dafa shinkafa kubburowa take yi ba taɓ?!" Cewar Ummu.

"Oh ni kam na ga abin da girmi kakata an dai yi zuwan zomo kasuwa." Hajiya ta ce tana salati.

Wiƙi-wiƙi ta yi da idanu daga ganin ta kasan ba ta da gaskiya don ko ita ta san girkin bai yi ba duba ga yadda ya yi cikin shega ya tsunbure. Kuka ta saka sosai.

"You know what? Let me take pic and send it to him, so that he can give you mark."

Da sauri ta ɗauke tukunyar ta ɓoye a bayanta tana zare ido.

"Ni wallahi an tsane ni a gidan komai na yi kuce bai yi ba, kum ku ci ba da degrading ɗina, to ba zan ƙara yin girkin ba ya bar ni idan na yi aure aka koro ni ba shi da asara."
Chapter 45 · 0% Book details