Sashe 22
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta same ta zaune a falo tana shan fura. Gallah mata harara ta yi, tare da kai ludayin furan bakinta. Dariya ta yi tana faÉ—in,
Allah ya bar mini kakata." Sai da ta kammala shirya cikin riga da wando ta fito tana rolling É—in É—an siririn veil É—inta.
"Hajiya zan je shopping me zan siyo miki?"
"Kin san an gaya miki, ki daina mini isakancin turancin nan na ki? Tun da ba ji na ke ba, in ba haka ba zan shuka miki rashin mutunci."
"Allah ya ba ki haƙuri. Siyayya za ni me kike so."
"Ban sani ba, umma ta gai da ashsha." Ta faɗa a ƙubule.
"To shikenan, sai mun dawo." A gajarce ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa.
Ganin da gaske take sai ta ƙwala mata kira ta ce."Dawo mana shalele, maimakon ki rarrashe ne sai ki tafi? Ni fa tsiyata da ke ba ki da kirki. Abu mai daɗi za ki siyo mini."
Dariya kawai ta yi ta fice sai da ta kai ƙofa ta ce.
"Sai jarabar faÉ—a da kwaÉ—ayin tsiya."
"Abby ya fita da motarsa. Ammy kuma tana gurin aiki, sannan motar ya Ajmal ko da tana nan ta fi ƙarfinmu, nan ga ni, nan bari. Don haka dole mu shiga motar gida."
Kallon wulaƙanci ta yi wa motar tana yatsina fuska.
"Kai dole mom ta saya mini mota, ba zan iya wahala ba."
"Lallai aiko da wuya Ya Ajmal da Abby su yadda. Za ki shiga aji shida na sakandiri ne za ki rinƙa driving? Ki sani Nigeria ba kamar London ba ce."
Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarinn shiga cikin motar ganin Musa direba ya shiga ya kunna.
A shopping Mall sai da ta yi wa kanta ƙarƙaf sannan hankalinta ya kwanta don ta jido kaya masu tsananin kyau har Nahlin da Ummita ta siya wa sai Hajiya da ta siya mata ƙwalama.
Suna shirin fita daga mall É—in ta hango wata doguwar riga mai tsananin kyau.
"Wow Anty Nahlin! Kalli wannan rigar ta tafi da ni, bari na duba app É—ina na palpay kamar ina da kuÉ—i na sayi rigar nan.
"Kai Jannah, na lura ke money monger ce, duk irin kayan da kika siya, amma ba su ishe ki ba?"
"Allah ta yi kyau ne." Ta ba ta amsa.
Hankalinta bai kwanta ba sai da ta sayi abayar suka je gurin biya. Tana ƙoƙarin transferring ɗin kuɗin ta ji muryar namiji ta bayanta ya na faɗin,
"Yauwa Mufid! Ma za ƙaraso yau Allah ya haɗa ni da ɓarauniyar da ta yi mini sata a filin jirgi." Ya faɗa yana tafa hannunsa cikin tsananin farin ciki tare da kallon abokinsa.
Da sauri ta waigo cikin tashin hankali take idanunta suka ciko da ƙwallah. Ba tare da ta san ta yarda rigar dake hannunta ba.
Kallonsa ta yi tana tunanin kamar sun taɓa haɗuwa don fuskarsa ya yi mata kama da wanda ta taɓa gani.
"Like I knew you before?" Ta furta cikin tantama.
Sai ya ɓata rai tare da kai key ɗin motarsa kusa da fuskarta kamar zai taɓa ta da shi.
"Ban sa ni ba, kin bar ni da tunaninki babu dare babu rana. Haka ma za ki ce mini? Alamun kin manta da ni." Ya ƙarashe maganar tare da ƙara ɓata fuskarsa.
War ta yi da idanunta domin ta gane saurayin da suka haÉ—u a filimg jirgi wanda yake yawan faÉ—o mata a ranta.
"Haba kyakykyawa understand me. I wanna build and development a health relationship between us.
A jiyar zuciya ta yi mai ƙarfi, domin tun haɗuwarsu ta lura da irin kallon da yake mata, amma ina sam ba ta shirya ba. " Na gane ka, buddy ne wanda muka haɗu a airport."
"Jannah ki zo mu tafi kin ga dare yana yi, kuma Ammy ta ce kar mu daɗe." Nahlin ta furta tare da kama hannunta suka shiga mota, ganin kamar zaƙewarta na kula shi ta yi yawa, duk da cewar ita ma ta gane shi.
"Jannah." Ya furta a hankali yana shafa gemunsa da wani irin tsadadden murmushi a fuskarsa. Ganin direba ya tada motar ya sanya ya rugo da gudu a gefen da take.
"Haba Jannah, kar ki zama mace mai son kanta. Tun da kika ga mun yi haɗuwa biyu tabbas a kwai ɓoyayyen lamari a tsakaninmu. Yanzu haka za ki tafi ba tare da na san inda zan gidanku ba?" Ya yi tambayar cikin marairaicewar fuska.
Kafin motar ta fara tafiya ta leƙo da kanta ta ce. "Jannah Jabir Ingawa." Ta ɗaga masa hannu tare da mayar masa da ƙayatatten murmushin da yake mata. Zuciyarta cike da tsananin farin cikin sake ganin buddy ɗinta.
"Jannah Jabir Ingawa da ma ita 'yar family É—in ce?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki domin sai ya ce faÉ—uwa ta zo daidai da zama don a kwai abokinsa a family É—in.
Sunan da ta faɗa mishi ya san ta faɗa masa ne akan ya yi searching ɗinta a social media don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ciro wayarsa tare da kunna data ya rubuta sunan wanda take ya fito masa har da ɗauke da hotonta tana riƙe da teddy.
Murmushi ya saki tare da rungume wayarsa domin shi kaɗai ya san tsananin farin cikin da yake ciki. A gurin ya tura mata da friend request wanda ko minti ɗaya bai yi ba, ta yi acceptin da tura mishi da stiker masu ɗauke da hoton abota. Sai ya ƙara sakin murmushin jin daɗi ya buɗe motarsa ya shiga tare da tada ta ya ja cikin farin ciki.
"Huzaifah." Ta furta sunan kamar yadda ta gani a rubuce. "Huhm! You are so humorous buddy."
Ganin murmushin ya ƙi ɓacewa daga fuskarta. Nahlin ta gyara maza tana kallonta. " Kamar shine saurayin da kuka haɗu a filin jirgi, kuma na ga kamar sonki yake? Ina gargaɗinki da karki faɗa tarkon namiji ki fara relationship at this age. Kin ga ko ni sai da na shiga Jami'a sannan ya Ajmal ya barni nake kula samari."
"Haba Anty Nahlin! Why all this questions and statements? Kar ki kai ni inda ban kai ba. Babu komai a tsakaninmu, shi É—in abokina É—auke shi."
"Humh." Ta ce sai kuma ta kalle ta tare da yin dariya. "Idan kin ɗauke shi ba aboki, shi ba'a haka ya ɗauke ki ba. Kin dai san soyayya ba ta ɓuy.."
"Then I will make him understand ok? Yawancin abokanan na maza ne. So banga komai ba."
"It is just a piece of advice." Cewar Nahlin.
"Thanks." Ta ce ta maida hankalinta kan wayarta tana reply É—in messages É—in da ya yi mata.
Mom zaune a kan kujera ta zabga tagumi yayin da idanunta suke cike da ƙwallah tana sauraren Fedris da take ta yi mata bayanin abubuwan da suke buƙata. Kuɗin Ƙasar ta ciro daga jakarta masu tarin yawa ta ije a kan teburin dake gabanta.
"Take this and if there is need of it, please contact me. I wanna leave this country tomorrow." Ta furta cikin muryarta mai sanyi tana gyara É—aurin gyalenta. "Thank you ma'am and I wish you safe trip." Jinjina mata kanta ta yi sannan ta fice daga ofishin.
A ranar da ta dawo, sam ba ta fita ko ina ba tana hutun gajiya, har sai da ta yi kwana biyu. Sosai dad ya ji daɗin yadda ta dawo cikin farin ciki, domin ya samu sausauci a tsakaninsu, har da yi masa hira da ba shi labarin ɗubbin nasarar da ta samu, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba, ya rinƙa ji da ita.
Washegari da safe ta shirya zata fita tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta ya shigo ganin ta cikin shirin fita, ya sauya fuskarsa daga fara'a zuwa ɗaurewa.
"Haba Halima, kamata ya yi ace sai kin yi sati kafin ki fara fita, kina cika wa kanki aiki. Ki tausaya mini ni fa mijinki ne, kuma ina da haƙƙi mai girma akanki."
"Please Injiniya! Kar mu fara tun yanzu. Ba rayuwata ba ne? I have ambition and I want to do everything humanly to accomplish my goals." Lokaci guda fuskarta ta canza ta É—auki jakarta ta fice ta bar shi tsaye sororo.