Sashe 59
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ji na tsani kaina domin hatta iskan da nake shaƙa a duniyar ba na jin daɗinta. Sai kawai na yanke shawarar mutuwa kawai na sadu da iyayena, amma da mutum baya mutuwa sai lokacinta ya yi, kan dole na haƙura da jiran mutuwa na ci gaba da rayuwa ina bara ina cin abinci, don ba zan iya kashe kaina ba saboda na san hukuncin wanda ya kashe kansa.
Watarana ina cikin tafiya kawai na tsinci jaridar mai ɗauke da hotonki da sunan ƙungiyarki. Take na gane ki duk da cewar kin canza ba sosai amma ba zai hana na gane ki ba.
Na yi murna sosai domin ban ɗauka ƙungiyar ta ɗaukaka kuma tana aiki ba, wanda cikin farinciki na yi bara na haɗa kuɗina na taho Abuja, amma kwasam aka sanar mini da cewar ba kya Ƙasar wasu ne suke tafiyar da ƙungiyar.
Na yi baƙincikin ba zan iya ganinki ba. Duk irin yadda mahukutan ƙungiyar suka nuna mini za su iya taimaka mini ko da ba kya nan, sai na ƙi na gwammace na rayu a haka in har zan warke na yi rayuwa ni kaɗai babu wanda na sani.
Ganin halin da na shiga wani namiji ya sanar mini da akwai yiwuwar dawowarki Ƙasar saboda kin tsaya takarar Minister, wanda na yi matuƙar farincikin hakan na saka a raina zan jira dawowarki, ko har zan mutu ba ki dawo ba."Ta ƙarashe maganar cikin matsanancn kuka.
Gabakiɗaya ɗakin suke hawayen tausayinta ba kamar Hajiya Baaba kuka shaɓe-shaɓe har da su majina.
"Kin ga rayuwa Mujee, na tausaya rayuwarki haƙiƙa ya cutar dake. Allah sai ya saka miki Allah ya jiƙan iyayenki. Da ace na san kina cikin wannan halin da na dawo Nigeria ko da mutuwa zan yi a cikinsa, saboda ni ma ba daɗi ya sa na bar Ƙasata ba. Abubuwa da dama suka faru wanda ba na son na tuna domin komai ya wuce." Ta ƙarashe maganar tana kallon dad da ya sunkuyar da kansa jin abin da ta ce.
"Na yi miki alƙawarin nemo Kham, matuƙar ina raye sai na hukunta shi akan laifin da ya yi miki, sannnan ki zauna a gidana har ƙarshen rayuwarki, domin na san zalincin da ya yi miki abu mai wuya ne, ki ƙara aminta da wani ɗa namijin."
"Har abada ni da aure mun yi hannun riga, na gode ai kuwa in har kika kamo shi kika hukunta shi babu abin da za ki yi mini bayan wannan, domin burina na ga an hukuntashi ta girbi abin da ya shuka."
"Mene ne amfanin ƙungiyar in har ban share miki hawaye ba? Karki manta da kamar wasa ƙungiyar ta kafu kuma da taimakon ku. 'Yancin mata.." Ta furta da ƙarfi tana ɗaga hannunta.
"Shine burinmu." Mujee ta ɗaga hannuntan tana faɗi da ƙarfi.
Murmushi mai kama da kuka suka fara tare da rungume juna lokaci guda memerories na shekaru suka fara dawo musu.
Ummu ta buɗe ƙofar ɗakin da Jannah take ciki ta shigo a ranta tana jimamin halin rayuwa da Mujee ta shiga.
"Jannah, don Allah ki tausaya wannan matar, ba ki ji halin ƙuncin da ta shiga ba." Sai ta fara ba ta labarin cikin tsananin tausayawa.
"Leave me alone with that story ni ko kaÉ—an ba ta burge ni, saboda ta yi ruwan munafukai, na tabbata labarin nan fabrications ne.
Miƙewa ta yi a zafafe ta fice ba tare da ta kalli inda take ba domin ta ci ka kafiya da rainin wayo.
Sakamakon strike da aka fara mom ta roƙi abar Ummu da Jannah har da Nahlin su ɗan yi mata hutu, wanda Jannah ta ji daɗin hakan domin ba ta gama ganin dad ba. Jin za su zauna Hajiya Baaba ta dire kan ba za ta tafi ba sai lokacin da za su tafi, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ba mom ba.
A maimakon ta zauna a gidan ta basu lokacinta, amma sam inta fita tun safe sai dare take dawowa, kasancewar abubuwa sun yi mata yawa. Ga siyasa ga ƙungiyarta wanda dawowarta mutane sai zuwa suke sosai.
Duk iya ƙoƙarinta na son ta samu lokacin kanta ta zauna da mutanen gidan, amma abin ya ci tura! Saboda ko da safe ba sa ganinta kafin su tashi ta fice.
Ta san cewar hakan zai ƙara bakanta ranta, amma sai dai ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce hakan.
Ta dawo gida da ciwon kai mai tsananin zafi sakamakon wunin yau a meetings ya ƙare.
A maimakon da ta sha maganin ta kwanta, amma sai ta miƙe tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar zai rabu gida biyu.
Files biyu ta É—auka ta nufi É—akin Mujee, amma ba ta nan sai ta nufi kicin don tunaninta tana can.
"A Halee, yanzu nake son bada umurnin abin da za a girka na shigo mu na yi miki sai da safe.
"Ok, don't worry ni ma na dawo da ciwon kai na so nake na huta, but I have to give you this."
Karɓa ta yi ba tare da ta duba takaddun ba."Subuhanallahi! Am sorry Halee, but did you take meds? I know you don't like taking it."
"Zan sha saboda ya zamar mini dole, ina jin ciwon kan har kwanyata." Ta ce da fuskar da ke bayyana ba ta da lafiya.
"Sorry, wishing you quik recovery."
"Amin ta ba ta amsa." Tana cewa,"Ki duba takaddar mana ba ki abu kin riƙe kawai."
"Oh! Sorry ciwon kanki ya tada hankalina."
"Oh my God! Offer na aiki a ƙungiyarki?" Ta tambayeta cikin tsananin mamaki.
"Eh, ai kin cancanta Mujee, ko da can ai ke kika nuna bakya buƙatar zama a Arewa, wannan dalilin ya sa na haƙura. Sannan waɗannan takaddun na shedar karatunki ne, da na ƙoƙarta na samo miki su"
"Haka ne, ga shi yanzu rayuwa ta yi mini kamun kazar kuka na dawo." Ta faɗa sai hawaye suka wanke mata fuska sosai ta rungumeta cikin matuƙar farinciki.
"Haƙiƙa kin cika uwar marayu! Allah ya ci gaba da buɗa miki da haskaka rayuwarki, ya ba ki nasarar lashe zaɓe."
"Allah dai ya shige mana gaba. Bari na je na kwanta sosai kaina yake takura mini, gobe sai ki kasance cikin shiri tare zamu tafi. Ke ce Sakatariyar Hajiya Turai."
"Ma sha Allah."Ok, sai da safe Allah ya ƙara sauki."
Har ta nufi sashinta sai kuma ta dawo." Wai ni kam Mujee, har yanzu skills na ki na yin turaren wuta yanan?"
"Eh, ban manta komai ba, don ko a can na tambayi Kham na ci gaba ya nuna baya so."
"In sha Allahu zan yi miki transfer na kuÉ—i, sai ki je kasuwa ki siyo komai ki fara haÉ—awa. Zan yi magana a nemo miki shago da waÉ—anda za su zauna, zama babu sana'a ga 'ya mace akwai matsala. Mu tashi lafiya." Ta ce tare da saurin shigewa don ba ta son godiyar da za ta yi mata, ta barta baki buÉ—e tana share hawayen farinciki.
Washegari da safe bayan ta tashi saboda ciwon kan da har yanzu bai daina ba sai ba ta yi fitan sammako ba.
Bayan ta yi wanka ta saka doguwar riga ta fito falo don ta karya saboda tun da ta farka take jin yunwa.
GabakiÉ—aya mutanen gidan suna falo sai Mujee da take kicin da masu aiki.
"Yauwa Halimatuu, ma za ki zo gida zan koma saboda sam ban ga amfanin zamana a gidanki ba. Sam ba ki da lokacin da za ki zauna mu yi hira, kar ki manta wata uwa duniya kika tafi na tsawon shekaru, amma tun da kika dawo bana tunananin mun yi zaman minti talatin dake. Kullum sai dai ki barmu da arnar da kika cika gidanki da su wai masu aiki, su yi ta mana yare."
Ƙarasowa ta yi ta zauna gefenta."Kiyi haƙuri Hajiya Baaba, na san ban kyauta ba, amma wallahi rashin lokaci ne. Ga shi ina son na tafi Ingila zan yi sati biyu acan."
"Ki bar suya? Allah ya kyauta kin san Allah gobe ina Zariya ba zan iya zaman kurame ba. Kullum gida tsit kamar an yi mutuwa gabaki É—aya kin sa neman kuÉ—i a rayuwarki."
"Ba ki ga komai ba Hajiya Baaba, in dai mom ce, sam ba ta damu da kowa ba sai neman kuÉ—i. Ni dama saboda dad É—ina na zauna."Cewar Jannah.
"Ni kam tafiyata ya zama dole saboda na gaji da zama shiru, ai sai wata cuta ta kama haka kawai."
Ta ce tana harararta sannan ta ci gaba da cewa,
"Gobe na gaya miki zan tafi inya so ki tafi gaba da Ingila ba ta shafe ni ba."
"To Allah ya kaimu saboda ko na ce miki zan samu lokaci hakan ba zai yiwu ba, domin abubuwa sun sha mini kai, amma sai ki bari nan da kwana biyu, sai ki shiga kasuwa ku sayo komai. Su Jannah kuma in an janye yajin aikin sa dawo."
"Su yi ta zama zama ni dai ba zan iya ba. Na gaji da abincin arna, kuma na'urorin da kika sa a kicin tsoro suke bani. Gara na koma na rinƙa cin dabbu da fate da gauda. Ranar nan da na ce a yi mana dabbu wani iskancin dabbu aka yi har da su kayan ciki, gabakiɗaya bai yi kama da dabbu ba."
"Hmmm! Su Hajiya an saba da cimar wahala." Cewar Jannah tana dariya.
"Eh, na ji a haka na haifo masu kuÉ—i ba."
"Ki yi ta mana gorin 'ya'yanki masu kuÉ—i an gaya miki a tsiyace za mu rayu."
"Oh ban sani ba kuma yarinya ta yi mini rashin kunya yanzu zan huce haushin uwarta akanta."
Dariya ta yi sai kuma ta yi shiru ba ta ce koma ba don ta san tana iya sakar mata dundu.
"To maganar auren Jannah, ya kamata a saka rana ina komawa zan yi magana da Aby, duk yadda muka yi zan sanar muku."
Tsiri-tsiri suka yi da ido suna son amsawa, suna tsoron yadda Jannah ta yi musu wuri-wuri da ido, tana son jin me za su ce, wanda ya sa suka yi shiru sai kallon juna suke yi.