Sashe 13
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bayan ta É—auki tsawon lokaci tana watsawa kanta ruwan sannnan ta fito daga cikin bayin ta sanya dogon riga kawai ba tare da ta shafa mai ba ta fito daga cikin É—akin.
Kai tsaye kicin ta wuce in da take jin motsin Hajiya baaba tana kwarafniya da tukane.
"Yauwa shalelena kin fito? Yanzu nake son na shiga na yi miki magana jin kin daÉ—e a bayi. Ko ke ma kin É—auki halin mahaifiyarki na watsa da ruwa lokacin wanka?"
Dariya ta yi mata Jin abin da ta fadi."Wai Hajiya har yanzu ba ki daina rigimar yi wa kanki girki ba?" Ta maida maganar tsigar tambaya.
"Ato ni hauka nake na rinƙa bari ina cin abincin da zai cutar da ni. Haka kawai ba za a ci abinci mai kwayu ba, sai kullum a rinka cin wata cimar da aka ɗauko daga wata Kabila can. Shi ya sa nake girki da kaina. Kin ga ma za je ki zauna yanzu zan kawo miki abinci, saboda ke na yi tuwon shinkafa miyar taushe, duk da na san ke ma ba'a iya miki."
Jannah ta yamutsa fuska jin abin tace mata."A haba Hajiya na yi duguwar tafiya sai ki rasa abin da za ki ba ni sai tuwon shinkafa. So kike cikina ya yi nauyi na kasa bacci?" Sai ta fice daga kicin din tana faÉ—in ni ba abinci zan ci ba tea kawai zan sha na kwanta bacci, sai bayan na tashi zan ci abinci, amma ba tuwo ba."
Hajiya ta biyo tana tana salati. " Haba Jannatuu so kike su yi mini dariya, tun da mahaifiyarki ta gaya mini za ki zo kwana na yi ban rintsa, don Allah kar ki watsa mini kasa a ido." Dariya kawai ta yi ta kwanta akan doguwar kujera daidai lokacin da Nahlin da mahaifiyarta suka shigo yayin da Nahlin take ɗauke da turen abinci, ganin haka Hajiya Baaba ta harari kwanon tare da ɗauke fuska bayan ta taɓe baki.
Murmushi kawai suka yi tare da shigowa. "Sannu da hutawa Hajiya." Mom ta furta da sauri ganin zata shige kicin.
"Ba aiki nake yi ba kamar yadda kike gani." Shiru ta yi ba tare da tace komai ba har ta shige kicin É—in tana bambami.
Nahlin ta sauke tiren kwanon abincin tana bin bayanta da harara. Ba ta yi ninyar gaishe ta ba kamar kmar yadda tasan ba zata amsa ba.
Da sauri ta sauka daga kan kujera ta durƙusa." Mom barka da fatan na same ku lafiya?" Ta furta cikin jin kunya da girmamawa domin Allah ya sanya mata jin kunyar Ammy da ƙaunar ta.
Shafa kanta ta yi cikin so da ƙauna."Lafiya lau ya maihaifiyar ta ki."
"Daddy yana lafiya."Ta ce cikin basar da tambaya.
Murmushi ta yi kawai sannan ta miƙe tana faɗin."Bari na barki da Nahlin, in kika huta da fatan za ki shigo shashin nawa."
"Eh Amym ai a É—akin Nahlin zan zauna." Ta furta domin ta É—auki aniyar ba zata zauna a É—akin Hajiya Baaba ba.
Akan me za za ki zauna a É—akinta bayan tun kafin ki zo na sanya aka gyara mana É—akinki." Ta ji muryar ta tana mata tambaya.
"Gaskiya ba zan zauna a ɗakin ki ba, kiyi ta damun mutane da surutu da labarin sa bai shafe ni ba, har da na matattu fisabilillahi ina wanda zai kwanta bacci za a bashi labarin mattatu salon na yi mafarkin fatalwa." Ta ƙarashe maganar cikin shagwaba.
"Jakar uban nan!" Ta furta ai kuwa in har ba za ki kwana a É—akina kin É—auko ruwan dafa kanki, domin magen da kike tsoro na É—aura miki a jiki, jiya kasa bacci na yi ina murnar za ki zo, amma sai ki watsa mini kasa a ido, ai gara ki dawo hankalinki tun kafin ruwa ya kare wa É—ankada." Tana gama maganar ta wuce É—akinta.
Dirama sosai aka yi akan inda za ta zauna ganin ta ki cinyewa da kanta ta zaɓi ta zauna a sashin Hajiya Babaa.
"Da dai kin hutar da kan ki. Haka kawai an mallake mini É—ana, kuma wanann 'yar gudaliyar za'a haÉ—a da ita. Ina wallahi uban kuturu ya yi kaÉ—an. "
Ita dai Ammy ba ta ce komai ba. Ajiyar zuciya ta saki, sannan ta fice daga ɗakin. Nahlin ta yi ƙunƙunai wanda ba za ka gane me take cewa ba zata fice daga ɗakin, wanda hakan ya kubular da Hajiya Baaba ta wawuri mafici ta jefa ta da shi. Nahlin ta ruga da gudu tana dariya.
Jannah ta yi shiru duk irin surutun da take ba ta da labarin yadda ta mallake mata ɗanta. Sam ba saurara take yi ba domin hankalinta ya yi nisan kiwon dan saurayin da ta ji ba ta kyauta masa ba, ya kamata ace sun yi exchanging contact if possible su rinƙa gaisawa.