← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 79

Sashe 32

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Kwashe da dariya 'yan É—akin suka yi ban da Hajiya Baaba da Ajmal
"Inna lillahi! Anty Jannah, da ma ba ki iya karatun akur'ani ba, ƙatuwa da ke? Ko ni na izifina ishirinnda biyar?"
"Kai rufe mini baki banza kawai." Ta ce masa tare da kai masa duka.
"Wallahi kika ƙara dukansa sai na haɗa ki da gini ai gaskiya y faɗa. Jahilar banza kawai. Babu abin da kika sani sai iyayi da taƙama." Cewar Hajiya Baaba.
"Kin dai gani ko Hajiya, kin ga wacce kike karewa har kika tsaya don kar na bige ta?" Ya faÉ—a cikin takaici da mamaki.
"Tashi zan yi ni kam yanzu. Ka koya mata karatun, in ta ƙi ka yi mata dukan mutuwa ka ga tafiyata." Ta fice daga sashin.
"Ke kam kin ji haushi da auren mace irin ki gara zama gwauro. Ke Nahlin ki ɗauko mata bagadadi ki rinƙa koya mata. Na ba ta wata biyu ta gama. Duk ranar da ba ta yi ba, just inform me I will just seize her phone.
Kuka sosai ta saka harda su share majina ko tari ba ta yi ba ganin wacce take goyon bayanta ta kware mata.
Tsawar da ya daka mata ya sa ta yi shiru ta bi Nahlin da taje É—auko bagadadi don ta koya mata.
Wunin ranar babu wanda ta kalla don ɗakinta ta kulle ta yi zamanta. Ko abincin rana ƙinci ta yi, babu abin da ya fi ƙona mata rai irin dariyar da suka yi mata. Ga shi ko da ta dawo haka ta sata a gaba da habaici da waƙe-waƙe.
Ta kira wayar dad ya fi sau nawa amma bai É—aga ba, don haushi ko kallon numbar mom ba ta yi ba, don tana ganin duk ita ta ja mata wannan tozarcin.
Duk irin gargaÉ—in da ya yi mata ba ta ji. Ko da Nahlin ta fara koya mata ganin hankalinta ba shi gare ta share ta kama aikinta, wanda hakan ya yi mata daÉ—i ta ci gana da kallonta.
Washegari da asuba Nanlin ta zo ta tashe ta ko sallah ba ta yi ba suka tafi cewar inta dawo za ta yi. Ko da ta je babu abin da ta iya sai zare ido wanda hakan ya baƙanta ransa.
Bulala biyar ya yi mata sannan ya ce," Ma za ki shiga É—akina ki gyara mini, it is you funishment."
"Ban iya ba." Ta ba shi amsa ba tare da shakku ba tana sosa inda ya duke ta.
"Allah ya isa mugu azzalimi, in sha Allahu sai an rama mini akan yaranka." Ta faÉ—a a hankali yadda ba zai ji ba.
"Je ki koya mata sannan ta gyara É—akin da kyau. Kuma wallahi gobe in ba ki iya ba sai na lahira yafi ki jin daÉ—i."
"Ni fa gyaran ne I can't cus I don't know how to do chores."
"Ok." Ya bata amsa yana kallonta domin ya gama fahimtar 'yar rainin wayo ce.
"If that is the case then you will collect another cane." Ya ce yana ƙoƙarin ɗaga bulalar.
Da gudu ta ruga ta ɓoye bayan Nahlin ta ce,"I will don Allah kar ka ƙara dukana." Sai ta bi bayan hanlin da ta riga ta shiga ɗakin domin tare za su yi.
Suna shiga ta tsaya a ƙofar ɗakin tana toshe bakinta."I really hate this guy with my whole being. Had I know I will face this I should have not came back to Nigeria. Sam ba shi da imani, I know he has his intentions for threating me, and very soon zan bar gidan nan."
"Haba kar kice haka. Shi É—in É—an'uwan ki ne, kuma he is doing all for you onw good, you will enjoy it in the meantime. So please let's bare it ok?"
"Oh please don't change the topic. I beg you pardon for saying that. Believe me, he has his reasons. Ni wallahi na ƙosa ya yi auren mu huta."
Dariya Nahlin ta yi ta fara kakkabe Saman gadon tare da yaye bargon ganin ba ta da ninyar farawa.
Zama ta yi tare da ƙara toshe hancinta."Kai this smelling is awfull. Gaskiya ƙazami ne sosai, wari nake ji, wannan matar shi ta bani da ƙazanta Allah. Ji ɗakin is not well organized."
Tsananin mamakinta ya sa ta kasa cewa komai sai da ga baya ta ce," Kai anya na taɓa ganin 'yar rainin wayo kamar ki? Ƙamshin tsadaddan turaren na sa kike cewa wari."
"Eh ni dai wari yake mini, daga jin ƙamshin outdated ones ya ke amfani da shi."
in gyaran muryarsa kamar zai shigo yasa ta miƙe da sauri ta fara taya Nahlin gyaran. Kusan aikin ita ta yi don babu wani abin kirkin da ta yi.
"Na gama." Ta ce mishi tare da marairaice fuska ita a dole ta yi aiki ta gaji.
"Sai ki fita gobe in kin ga daɓa kar kiyi kayana na nan sai ki wanke, kin ga kuɗina ya huta. Daƙiƙiyar banza kawai." Fita ta yi cilin ɓacin rai tana ƙunƙunai
Tan shiga sashinta ta sa kuka." Wallahi na tsani zaman gidan nan, na ƙosa na gama kama hostel, ni gidan nan kowa haushinsa na ke ji."
Tsaki Hajiya Baaba ta yi tana faɗjn,"Ni ma na ƙosa ki tafi na huta da ala ƙaƙai da kunna mini waƙoƙin arna. Ke na fahimci iyayenki gajiya suka yi da jarabar ki suka tattaro ki suka kawo mini wahala." Jin abin da ta ce yasa ta ƙara sakin wani kukan.
"Allah duk mom ce ta janyo mini wannan musifar ba zan yafe miki ba."
"Kyaji da shi, shashashar banza uwar tanki ma ba ki darajata ba ballantana wani. In kin gama kukan shagwaɓar ga abincin ki can da aka gama barbaɗe shi an kawo miki kwaɗayayya kawai.
"Oh dai, ni dai ba zan ci wannan jagwalgwalon na ki ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar kwanon abinta ta shige ɗakinta.
Da ta tasa abincin kasa ci ta yi babu abin da ke mata yawo aka sai dariyar da suke mata da kalmar jahila da daƙiƙiya da suke ce mata sai maimaita kansu suke yi.
"Zan ba su mamaki sai na nuna musu ni ba jahila bace, zan dage na koyi karatu sai muga jahili a tsakaninmu, kamar ni da nake É—aukar distinction a makaranta za su kira ni jahila."
ÆŠakin Nahlin ta nufa inda ta same ta tana zaune a kan gadonta tana danna waya. Kaanciya ta yi kan gadon har sai da ta gama wayar sannan ta juyo ta kalle ta.
"Anty Najhlin please ki koya mini karatu, so na ke cikin wata É—aya na iya karatu, zan nuna masa ba nahilci ba ne kawai bana son karatun ne."
"Ok, ba ki da matsala zan koya miki, kin ga Ummu ta ci gaba koya miki in ta dawo. You will like her she is outgoing and loquacious"
"Really." Ta ce tana murmushi wanda ta ɗaga maka kanta tare da miƙewa.
Dariya ta yi jin abin da take faɗi,"You really crack me up. Ni ma zan so hakan." Kin ga direba ya tafi ɗauko Ummu-Kursum, kuma na ji Aby yana faɗin kamar makarantarku zai mayar da ita saboda kidnappers sun kai ma makarantar su hari. Kin ga sai ta rinƙa koya miki. Ki shirya an jim in mun yi lunch ki raka ni makaranta zan je screening.
"Wow! I can't wait to see me in to tertiary, it will be like.. Cus I wanna chill. I Phone 15 zan rike."
"A lallai ba karatun za ki yi ba, kin san ni Jami'a ba baƙuwa bace a gare ni, saboda sai da na yi diploma, yanzu two hundrent level za ni."
"Anty Nahlinnnnn!" Suka ji muryar Ummu da ta sheƙo zuwa ɗakin tana kiran sunan cikin ƙaraji.
Nahlin tankama hannun Jannah suka fito tana faÉ—in,"Oyoyo, yar'uwata."
FaÉ—awa jikinta ta yi suna juya cikin tsananin farin ciki." Am so happy to see you Antyna." Ta furta tare da juyawa tana kallon Jannah da ta sagale hannunta tana kallon su cikin sha'awa.
"Jannah kin fi kyau a bayyane, gaskiya kina da kyau sosai."
"Don Allah?" Ta ce mata tana murmushi.
"Wallahi, kuma irin sosai É—in nan, please let's take pics."
Murmushi ta yi ba tace komai ba daidai lokacin da Ummu ta kama hannunta suka shiga ciki bayan sun gama É—aukar hoton.
Ko cikakken minti goma ba ta yi da dawowar Ummu ba suka ɗinke tamkar irin ƙawayen da suka daɗe ba a haɗu ba, saboda Ummu mutum ce mai shegen surutun tsiya da tsokana. Ga ta da son wayewa da hutu da ƙarya, kusan dai halin su ya kusan zama ɗaya.
Abin da ya ƙara sa ta saki jiki da ita yadda ta ga shigar ta yi rolling gyalen abayar da ta saka ba kamar Anty Nahlin da kullum take cikin hijabi kamar matar liman ko ƙonannniya ba.
"Please sis, punch me your number. Hope you do Whatsapp, Facebook, Twitter, TikTok and Instagram?"
"Dariya ta ji jin abin da ta ce,"Including snap chat and telegram." Sai suka yi dariya mai shewa suka tafa.
"Wow! Ki ce kema you are so socialized. Please ki ba ni labarin London, ina ta addu'a Allah ya sa Ya Ajmal ya bar Aby ya kaini Ƙasar waje na yi karatu I like going outside Country."
"Kar ki damu sai kin gaji." Ta ce mata tana jin daÉ—in samun 'yar'uwa mai kalar rayuwarta.
A tare suka ci abinci suk yi sallah. Suka yi wanka sannan suka wuce sashin Hajiya Baaba a can suka wuni. Ko rakiyar da Jannah za ta yi wa Nahlin tare aka je da Ummu duk da gajiyar da ta kwaso jin Jannah za ta ta dage sai ta bisu.
Ba su kwanta ba sai misalin biyu da rabi. Tare suka yi kallo a wayar Jannah, bayan sun gama suka yi karatu sannan suka kwanta.
"Ashe kema ƙwararriyace gurin kallon Korian films?Anty Nahlin da na tura mata ta ƙyar ta kalli season one penthouse" Ta tambayeta cikin mamaki.
"Eh ina kallo ina zo hutu, kuma suna da daÉ—i, amma na fi kallon Nigerian film. Ai Anty Nahlin 'yar islamiya ce kuma matar ustazu, ba ki ji ba ta rasa wanda za ta so sai Malam Amir za ta aura ba"
Zare ido ta yi cikin tsananin mamaki."Don Allah da gaske!"
"Eh, sun daÉ—e tun kafin ta kammala diploma, har maganar ta shigo gida kuma naji kamar Aby yana cewa bayan na Ya Ajmal, babu jima wa za a yi maganar na ta, yana son ta É—an yi nisa da boko ne."
"Innalillahi" Ta ce tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi."Amma ta sanya ni a kwana. Ranar ya buge ni a gabanta na gama zage shi tatas, har ina faɗin gemunsa ya yi kama da jikin bushiya."
Dariya ta kwashe dashi har tana faÉ—owa saman gado."To what did she say."
"You know what? She just smile and she didn't say a word."
"Ai ba za ta ce miki komai ba Anty Nahlin akwai kawaici. Aby ya yaba da shi sosai bokin Ya Ajmal ne tare suka yi koyarwa a islamiyarmu. Yanzu lecturer ne A.B.U department of geology."
"Tab! Ai ta ba ni mamaki. Sis mai zai hana ki dawo sashin Hajiya Baaba, mu rinƙa kwana zan sa mom ta gyara mana ɗakin sa mana kayan kiɗa."
"Sashin Hajiya Baaba, za ta barni? Ni fa ba na wani shiri da ita don ta cika takura."
"Ba dolen ta ba, ni kaina ai ban so zama a gurinta ba, amm ta dage. Na yi mamakin yadda akai ba ta zo ta tasa ƙeya ta ba. Mu gwada inta ƙi saina tattaro kayana na dawo nan."
"Ok, shikenan, mu gwada mu gani." Ta bata masa tare kwanci sakamakon jin idanunta sun fara zafi.
Chapter 32 · 0% Book details