← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 79

Sashe 51

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin ta nufi na ta tare da mayar da ƙofar ta rufe. Bayi ta shige ta ɗauro alwala ta fito har ta zauna a ɗakin za ta fara karatun kur'ani, sai ta miƙe ta fasa karantawa a ɗaki ta koma falo.

Ganinsa zaune da kur'ani amma ya kasa karantawa ya sa ta ji matuƙar haushinsa, domin ya karya alƙawarin da ya yi mata na cewar duk abin da yake damun ɗayansu za su kashe su rufa.

Zama ta yi akan kujera maimakon inda yake zaune wanda ya ware don karatu wanda ya ke cike kur'anai da littafan addini.

Cikin murya mai sanyi ta shiga rera karatu da ƙira'ar hafsi, yayin da wani lokacin take satar kallonsa da ya riƙe kur'anin ya lula duniyar tunani.

Idanunsa suka canza tuna maganar auren da Hajiya Baaba take son ƙababa masa na yarinyar da sam ba ta dace da rayuwarsa ba. Da ya kalleta yadda ta kame tana karatu cikin natsuwa sai ta ba shi tausayi, domin ya san duk inda macen ƙwarai take ta kai saboda duk da kasancewarta nurse bai taɓa mata ƙorafi akan rashin kula da cikinsa ko haƙƙinsa da tsafta ba. Sosai take dagewa gurin faranta masa rai, wanda yake ganin bai kamata ace mar'atussaliha kamarta za a yi mata kishiya ba.

A hankali ya fara karatun cikin muryarsa mai daɗin gaske. Mushiirat sai ta ji ta kasa cigaba da karatun domin muryarsa ta tafi da tunaninta da duk wata natsuwa ta shi. A kullum tana godewa Allah Ubangiji da ya ba ta shi a matsayin miji, domin shi ɗin mijine na nuna wa tsara wanda ya iya tattalin mace da ba ta duk wata kula da take buƙata. Babu abin da yafi burgeta a gareshi yadda yake da addini da kamun kai, komai na shi cikin tsari da natsuwa da koyi da Annabi. A kullum burinta Allah ya ba su 'ya'ya masu albarka wanda za su tashi cikin koyi da ɗabi'un mahaifinsu.

Ganin ta yi nisa cikin tunani ya sanya shi rufe ku'anin bayan ya yi addu'ar, gama karatun yayin da ya ji dama da sauƙi a zuciyarsa ya ƙarasa gabanta wanda ba ta san ya iso ba.

Saukar kiss ta ji a fuskarta wanda ya sa ta saki ajiyar zuciya tana kallon shi.

"Am sorry." Ya furta cikin jan hankalinta da wata irin murya.

Sai kawai ta tsinci kanta da fashe masa da kuka ta faɗa jikinsa."Please, na roƙe ka da karka rinƙa ɓoye mini abin da ke damunka zauji, in ba haka ba za ka yi sanadin rasa n.."

"Shiiiiit!"Ya ce tare da saka É—an yatsarsa ya toshe mata baki.

"Waya gaya miki zan iya rayuwa in babu ke? Har yanzu ba ki yadda da ce miki da na yi kece mace É—aya wacce na ke jin zan iya rayuwar aure dake ba? Kina girmama ni sam bakya mini rashin kunya sannan mace ce ke wacce ta ma sunanta ta kuma isa ta É—auke hankalin ko wane É—a namiji."

Murmushi ta yi tare da faɗawa jikinsa tana sunne kai. Kiss ta kai mishi a bakinsa ta ce,"Ina matuƙar son ka ya Sheshk!"Ta kira shi da sunan da in har ta kira za ta gaya mishi abu maimahimmanci ne.

Ƙara rungumeta ya yi yana faɗin,"Ni ma haka rayuwata." Sai ta ji wani matuƙar sanyi ya lulluɓeta lokaci guda ta manta komai suka shiga faranta ran junansu.

Bayan ya dawo daga sallar isha a masallacin gidansa tana falo cikin riga da siket da ya kamata sosai tana jera masa abinci a dining ya shigo.

Da sauri ya ƙarasa gurinta ya karɓi filet ɗin ya zuba abincin, tare da zaunar da ita kan kujera y gama gyara dining ɗin sannan ya zuba musu abincin ya fara ba ta a baki.

Sai kallonsa take yi lokacin da yake bata labarin abin fa ya faru a tafiyarsu da nasarar da suka samo. Tuni ya manta da komai domin zuciyarsa ta gaya masa wasa take yi, don haka bai yi ƙasa a gwuiwa gurin watsar da komai ya ci gaba da tarairayar matarsa da ya yi mising ɗinta mara misaltuwa.

Washegari da safe bayan Aby ya dawo daga masallaci ya shiga É—akin Hajiya Baaba don ya gaishe sa. Tana zaune a cikin É—akinta tana jan carbin da sai gyangyaÉ—i take yi.

Jin muryarsa ya sa ta daina gyangyaÉ—in tare da gyara zama tana kallonsa.

Har suka gama gaisawa zai miƙe ba ta ji ya yi maganar jiya ba, wanda ya sa har ya miƙe ta ce,

"Dawo ka zauna ina son magana da kai."

Gabansa ya faɗi a ransa yana addu'ar Allah ya sa ba zancan jiya za ta yi masa ba, amma sai addu'arsa ba ta karɓu ba domin tun kafin ya gama zama ta fara masa maganar.

"Na ɗauka yanzu za mu yi maganar auren da shirye-shirye, ka san lokaci fa ba ya jira. Ko so kake sai Halimatuu ta dawo sai ayi maganar? Ka ji na rantse maka tun da na faɗa auren babu fashi. Karka manta a lokacin da za ka yi aure ka mini alƙawarin daga wannan lokacin ba za ka taɓa saɓa mini ba."

"Eh Hajiya, don Allah ki daina tuna baya ai ba na ƙi auren bane, ina dai hangen abin da zai je ya dawo ne."

"Babu abin da zai dawo sai lkhairi. ÆŠanka za ka ja ma kunne karya sake ya bugar mini ita, don ba zan lamunta ba."

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 23-24*

*BOJUWA HERBAL'S*

*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅

*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*

*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Allah ya kyauta! Hakan ma ba zai faru ba, saboda yana da sani ba zai tasa matarsa da duka ba."

"Oho, jan kunne dai domin rigakafi yafi magani."

Zama ya ƙara yi cikin murya mai sanyi ya ce,"Don Allah Hajiya Na ji na amince ayi auren, amma ki bari matarsa ta ɗan ko haihu ɗaya ne, ita kuma Jannah ta yi zurfi a karatunta, kin ga kafin lokacin ma ta ƙara hankali tun da duka guda nawa take."

"A summa take ko ba a haife ta ba. Lokacin da na auri ubanka ko irgan dangi ban yi ba, kuma amma haka na rinƙa zaro ku sai da na yi takwas don dai ba su tsaya bane."

Ta ja numfashi tana kallonsa ko zai ce wani abu amma sai ta ji ya yi shiru cikin jimami don haka ta ci gaba da cewa,

"Kuma da kake cewa matarsa ta mutu in ta so, ai dama shi mijin mace huɗu ne ko alƙawarin ba zai yi mata kishiya ya yi ba. In an yi auren ta gungure ta faɗi ta mutu don kishi."

"To shikenan, za a yi duk bin da kike so Allah ya sa mu ƙulla alkhairi." Ya miƙe jiki a sanyaye tamkar kazar ƙwai ya fashe mata a ciki zai fice.

"Khairan zan ƙulla in sha Allahu duk wannan iskancin za su gaji su zauna dole, don rabuwarsu sai dai in bana raye." Ta ci gaba da jan carbinta tana gyangyaɗi.

"Wayyo Alllah na gode maka! Yau addu'ata ta karɓu Halimatuu za ta dawo gida. Allah na gode maka da ka bani tsawon lokaci na ga wannan lokacin. Ta furta daidai lokacin da ta kashe wayarta da suka gama magana wanda ta sanar mata.

"Dole na kira malamai su yi saukar Kur'ani da addu'oi akan Allah ya tsareta da mugun gani da ji." Ta ce tare da É—aukar wayar tana neman numbar Aby.

Jannah da Ummu suka yi sallama suka shigo cikin yanayin na matuƙar gajiya, kasancewar da ga makaranta suke. Turus suka ja suka tsaya ganinta tana rawa a tare suka kalli juna sai suka ɗauke kai.

Wucewa ta yi ta zauna ba ta ce mata komai ba, domin tun da ta yi maganar auren ta da Ajmal ta É—auke mata wuta suke zaman kurame wanda ko a tsummar gyalen Hajiya Baaba.

Ummu kuwa gabanta ya shiga dukan tara-tara tsoronta kar a kan maganar auren ne take rawa, domin ta san ba banza ba za ta rinƙa tiƙa rawa haka. Gabaki ɗaya sai ta ji ranta ya ɓace, yunwar da ta shigo da ita ta neme ta ta rasa, domin ta tsani maganar auren. Gani take tamkar takurawa rayuwar Jannah za ta yi, gara Ajmal yana da wata matar.

Kallon su ta yi ta watsar sai kuma ta fara magana bayan Aby ya É—auki kiran da take masa.

"Kuna ina ne Muhammadu? Da gaske kake yanzu Halimatuu na gabanka a Nigeria? Oh Allah mahaƙurci mawadaci."

A tare suka kalli juna mamaki ya kamata ta jin har ta iso Nigeria, amma dad bai sanar mata da yau za su zo ba, duk da cewa ta san ta yi hakanne don su yi suprising É—inta.
Chapter 51 · 0% Book details