← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 79

Sashe 23

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ta yi ƙara alamun ana kiranta ta whatsapp. Da sauri ta ɗauko wayar tana dubawa. Ganin Jannah ce ya sa ta ɗauka da sauri tare da kanga wayar a kunninta.
"Hello mom, Ina buƙatar kuɗi."
"Haba Jannah! What I have done to you to deserved this? Kar ki manta ni fa mahaifiyarki, you should respect me." Cikin muryar son kuka ta ƙarashe maganar.
Ƙin amsa mata ta yi sai ta ce a maimakon ta amsa tambayar. "I desperately need money. Ba kin ce saboda ni kika hana kanki hutu kike neman kuɗi ba? So do send me I wanna enjoyed."
"Amma ya kamata ki tambaye ni cikin girmamawa da sanin darajat.."
"To in har saboda ni ne, ina son ki siya mini braded car. Ki kuma tura mini kuɗi a account. Ki kuma yi wa mahaifiyarki magana, domin ta addabi rayuwata ta hana ni shan iska wai sai ta koya mini aiki. Ki sanar mata a haka kika tarbiyartar da ni, ban taso ina yin chores ba. I think is not bad, don kina gaya mini cewar nice wacce kika fi so, na tabbata ba za ki ɓata ni ba ko?" Ta furta cikin gatsali da rashin kunya.
Sai ta ji wani irin ƙululun abu ya toƙare mata ƙirji har sai da ta dafa mota. "Na yi kuskuren da na barki kika girma tamkar sakakken kashi, na kasa tsayawa na ba ki kulawa. In sha Allahu zan gara, zan zamo uwa wacce kowa yake fatan samu."
"Kina jina?" Ta tamabayeta jin ta yi shiru. "Eh, shikenan zan yi mata magana, kuma zan siya miki duk motar da kike so. Fatana ki damu da ni, ki so ni ko rabin son da kikewa mahaifinki. Ina matuƙar sonki, wallahi na fi kowa sonki. Sai ta yi ƙasa da wayar tare da fashe wa da kuka.
ÆŠif! Ta kashe wayar da jan tsaki tana faÉ—in,"Kyaji da shi, haka kawai ki É—ora wa kanki wahala, sai kin tara kuÉ—i kin kula da al'umma, bayan gidanki kin kasa kula da shi wai ke joy giver ko."
Nahlin da ta yi mutuwar tsaye ta kasa ce mata komai na 'yan daƙiƙa si kaɗa kanta take tamkar ƙadagaren kutu.
"Are you high?" Ta yi nasarar tamabayarta cikin tsananin mamaki sannan ta É—ora da cewa,"WaÉ—annan mugayen kalamai kike jifar mahaifiyarki da shi? Kin kuwa son wace ce ita, kuma wane irin É—ubbin nasara kike da shi da kika zo a 'ya guda É—aya da ta mallaka."
Wani banzan kallo ta yi mata mai kama da raini ta ce, "Na san dole sai kin yi maganar. Haba Anty Nahlin komai na yi sai kin ce ban yi daidai ba." Ta ƙarashe maganar a fusace tare da toshe kunninta ganin ta buɗe baki za ta yi magana.
Bin ta da kallo ta yi domin ta gama karamtar ta 'yar rainin wayo ce da rashin kunya. Sai ta sanya a ranta za ta daina mata magana akan duk abin da take yi, domin kamar yadda ta ce mom ce ta ba ta wannan tarbiyar haka ne, don su suka bata gurɓatacciyar tarbiya. Sai ta saka a ranta daga yau ba za ta ƙara mata magana ba don haka ta miƙe za ta fice daga ɗakin, wanda ganin hakan ya sanya ta miƙe da sauri ta riƙe ta.
"Am really sorry Antyna. Idan kika yi fushi da ni ya zanyi. Ba za ki gane wace ce mom ba. Sam ba ta girmama mahaifina agaban idanuna take daka mishi tsawa. Ta mai da shi kamar É—an da ta haifa, sannan ba ta zauna a gida ta ba shi kulawar da aure ya sharanÉ—a ba."
"Yarinya ce ke ba za ki fahimci komai ba. Don't be dummy and think logically. Mahaifiyarki abin alfahari ce ga rayuwarki, ke har da ta al'umma domin ita ɗin jigo ce ga al'umma. Kin san gidan marayu nawa take da shi a Ƙasar nan da ma ƙetare? Don haka ki tausasa kalamanki, kar kiyi nadama a lokacin da ba shi da amfani."
"Ok, from now on I will take note." Ta ce sannan ta fice ba tare da ko kalami É—aya ya yi tasiri a gareta ba ta koma ta zauna.
Murmushi ta saki ganin maƙudan da suka shigo akawunta. Sai ta mirgina tana ƙoƙarin kiran dad, daidai lokacin da kiransa ya shigo. Jikinta har rawa yake ta amsa.
"Jannah, ke ce kika buƙaci mahaifiyarki ta siya mota? Kin san fa Nigeria ba kamar London bane."
"Eh, ina son na tuƙa, kuma siyen shine kwanciyar hankalinta wacce take trending." "Ho yarinyata rigima. To shikenan, in sha Allahu cikin satinnan motarki za ta iso branded kuwa." Wani irin ihu ta sanya tare da kashe wayar ta fice don ta yi wa Nahlin albishir.
A hankali shaƙuwa mai tsananin gaske ta shiga tsakainta da Huzaifah wanda take matuƙar daɗin hakan. Domin kaso cikin tamanin na damuwarta ya rage sosai. Maganin da take sha sai ta manta kwana biyu ba ta sha ba, kuma ba tare da ta ji canji ko wani alamu ba.
Da fari abota suka fara duk da cewar shi ba haka ya so ba, don ya so kai tsaye ya bayyana mata soyayyarsa. Sai dai, zana masa tarin burikan da take da shi da yadda take son tsarin rayuwarta ya sa ya fasa hakan, saboda burinkanta sun girmi tunanin sa da ƙwaƙwalwarsa. Rashin sanin abin yi ya sa ya haƙura, amma kullum cikin bayyana mata yake a zahirince wanda take pretending akan ba ta fahimta ba.
Huzaifah mutum ne wanda ya taso cikin 'yanci da kulawa da kuma gata. Mahaifinsa Janar ne daga baya ya koma shahararen É—an kasuwa. Sai tsarin rayuwarta bai wani dame shi ba, domin yana son rayuwar yanci da hutu.
A haka suka yi ta soyayya da sunan abota kullum suna maƙale da juna. Yana matuƙar tsarinta, zubinta da surarta musamman kalar fatarta da ke tafiyar da hankalinsa. Burinsa kullum Allah ya mallaka masa ita sai ya ce ya fi ko wane ɗa namiji sa'a a duniyar. Kasancewarsa yana matuƙar son mace mara ƙiba, shi ya sa ta dace da tsarinsa.
Kasa jurewa ya yi don kar wani ya yi masa ƙafa ko late comer ya yi wuf da ita. Sai ya sanar mata da irin tarin ƙaunarta dake faman ɗawainiya da rayuwarsa, wanda hakan sai da ya sa suka yi faɗa har na tsawon sati ɗaya ta ƙi ɗaukar wayarsa. Sakamakon hakan, hankalinsa ya tashi har rama ya yi. Ita kanta ta wahala, amma tsabar girman kai da son cika burikanta ya sanya ta ƙi nemansa.
Ranar da ta ɗauki wayar ya cika da murna sosai ya bata haƙuri suka shirya. Ba bu yadda zan yi don tafi ƙarfinsa, amma she kansa ya san she was interested on him. Sam! Bai yadda akwai wata soyayya tsakanin mace da namiji in dai ba ta aure ba. Sai ya ɗauki hakan a matsayin yarinta becouse she was so young. Sam ba ta da wata magana sai ta maganarsa. Kullum cikin posting ɗin hotunansa take a shafinta. Da ga chatting, video call, and voice, babu wanda ba sa yi. Short video na sa da hotonsa jibge a wayarta. Wanda haka the same with him. Ita kanta ta san ya shallake mizanin buddy ya koma wani bangare mai girma na daban.
Jannah ta fara zuwa makarantar boko mai tsadar haske, da islamiyar da su Nahlin suke zuwa har da hadda, amma ba ta mai da hankali. Ko islammiyar ta je hankalinta na kan wayarta tana chatting. Ko ta sanya earpiece ta yi kamar tana jin karatun. Da ta dawo gida ba ta ƙara waiwayan karatun da aka yi mata sai in za ta koma islamiyar. Hajiya Baaba ta yi ta ƙorafi tana magana, amma sam ba ta kula ta domin ta yi mata wani irin raini. Wani lokacin ita ce take shakkarta.
Kullum malamai cikin ƙorfi suke yi. Abby da kansa ya yi mata magana, amma ta ƙi ji. Gabakiɗaya ta mai da hankalinta kan boko babu dare babu rana. Wani lokacin ko baccin kirki ba ta iya wa, domin horan da mom ta yi mata na cultivating reading culture ya yi matuƙar tasiri a rayuwarta. Burinta kullum shi ne ta zana jarrabawa ta fito da distinction.
Ganin suna barazanar dukarta sai ta dena zuwa wanda kan dole Aby ya je da jansa ya ba da haƙuri. Ita gani take takura mata islamiyar take yi, don a lokacin da ta dawo daga school za ta huta ta yi waya da Buddy, sai kuma a dame ta da maganar islamiya. Sati da lahadin ma ba hutu hadda. Ga Hajiya Baaba da ta addabi rayuwarta kan sai ta yi karatun da aka yi mata a gida.

Ranar da ta je islamiyar tana zaune a ciki ajin ana yin karatun hadisi, amma hankalita na kan waya suna chatting.
"Ba ni wayar." Ta ji mutum a tsaye akanta ya furta cikin tsananin fushi. Da sauri ta miƙe tana zare ido.
"Ni babu abin da nake yi da ita, kawai na riƙe ne." Ta ce cikin shagwaɓa da sangarta wanda hakan ya ƙara baƙanta ran Malam Aliyu sabon malamin da aka ka wo musu, sai kawai ya zula mata bulala da ƙarfi.
Wani irin ihu ta yi sai ga ta a ƙasa warwar! Babu numfashi, amma ko kaɗan hankalinsa bai tashi ba, domin ya tsani rashin kunya a rayuwarsa.
Gabaki ɗaya 'yan ajin suka dare a tunanin su aljanunta ne suka tashi. Kimanin minti ɗaya ba ta motsa ba, wanda ganin hakan hankalinsa ya tashi. Ruwa aka samo tare da watsa mata. Firgigif ta yi ta miƙe sai ta zura da gudu waje tana zunduma ihu.
Tun kafin ta shigo ciki Hajiya Baaba ta jiyo ihunta. Barin tuƙa tuwon shinkafar da take yi ta fito har zaninta na faɗi, amma ba ta kula ba.
"Uban wa ya taɓa mini jikalle? Waye shi ya san waye mahaifiyarki?" Ta jera mata tambayoyin tare da kamata tana rarrashin.
"Wayyo na shiga uku! Inna ƙara zuwa makarantar nan ba dad ya haife ni ba. Dukana ya rinƙa yi, sai da ya yi mini bulala ɗari."
Chapter 23 · 0% Book details