Sashe 43
Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da murmushi mai tsada ta ƙarasa gurinsu wanda ya kashe mata ido tun da ta taho. Hure masa idon ta yi da ta isa gare shi. A jiyar zuciya ya saki mai ƙarfi.
"A koda yaushe muka haɗu gani nake kina ƙara kyau bab, kin kuwa ganki tamkar wata a cikin taurari.
Murmushi ta yi jin abin da ya faÉ—i."Ku shigo ciki Mufid ka ga abokinka sai zuba yake."
Dariya ya yi."Ai dole ya yi zuba kamar fanfo samun mace irin ki ai baiwa ne. Tabbas abokina É—an baiwa ne."
Ƙara murmushi ta yi tare da nufar hanyar shiga cikin gidan wanda ganin haka suka bita.
"Ƙawarmu, aminiya, kuma 'yar uwarmu."Ya faɗa daidai lokacin da ya buɗe labulen falon bayan ya yi sallama.
"Barka da zuwa ku shigo. Huzaifah duk wannan matsayin ni kaÉ—ai?"
"Ai kin wuce haka ko bab?" Ya yi maganar yana tambayar Jannah dake gefensa.
ÆŠaga masa kai ta yi tana murmushi.
Bayan sun gaisa da tsokanar juna sai Ummu ta miƙe tana murmushin ta ce,
"Bari mu shiga ciki mu barku ku ci abinci."
"A don Allah ku tsaya na fi son ina kai loma ina cin abinci mai daÉ—i da my future wife ta girka. I know it will be very testing"
Hajiya Baaba da ta fito da hura da nono a hannunta tana faɗin,"Ina kuke 'yan son jiki? Sai ku karɓi wannan hurar ku dama masa, ko banza ya samu yaci abincin da ya fito daga gidanku tun da ƙila kafin in gama abincin sun tafi."
Turus ta yi tana kallonsu don ba ta ji shigowarsu ba saboda bayan fitar Ummu rediyo ta kunna.
"A lale marhabin da zaratan maza." Ta ce tana washe baki ta ƙarasa gurinsa.
Sai suka yi tsuru-tsuru don a tunainsu sun ji abin da ta faÉ—a.
Duƙawa suka yi suna gaishe ta. Guri ta samu ta zauna taci gaba da cewa,"Haba ku tashi ai kamar Adamuu na ɗauke ku. Ma za ku tashi 'ya'yan albarka."
Miƙewa suka yi suka koma mazauninsu suna shafa ƙeya.
"Sai na ji kamar ka ce za ka ci girkin Jannah ko?"
ÆŠaga mata kai ya yi cikin kunya yana sosa kai tare da mamakin tambayar.
"Taɓ! Aiko ka bugo don wallahi ko ru.."
"Hajiya Baaba kamar kin ɗora abu a wuta kamar yana ƙonewa." Cewar Ummu tama kama hannunta ta miƙe.
"Ke dallah kyale ni na faɗi gaskiya ai ita ɗaci ne da ita." Ta ƙarashe maganar tana wafce hannunta da ta tsaya kamar mutum mutumi.
"In kana jin sangartacciya na bugawa a jaridan ita ce, ka ga duk wannnan abincin da suka shirya maka, wallahi duk siyo shi suka yi. Ni saboda takaici kasa magana na yi, amma na ce sai na gaya maka kar na cuce ka saboda alkhairin da ka yi mini."
"Haba Hajiya Baaba, gaskiya abin da kike yi bai dace ba, kum.."
"Kin san Allah in kika ƙara magana sai na kwaɗe ki da maficin nan. So kike na cuce shi? Ai gara na gaya masa idan aka yi auren da ni za a taho don ni zan rinƙa masa girkina mai daɗi da rainon yara. Maganar aure fa ake yi, kuma ai dole sai an faɗi naƙasun kowa."
Sai ta gyara zama tana kallon Jannah da takaici ya hana ta cewa komai sai hawaye da kin bin ƙuncinta domin ta ji a jikinta dole sai ta kunyata ta.
Harara ta banka mata tare da kallonsa ta saki dariya."Ka na jina ko yaron kirki? Da Ummu takan yi abin kirki amma zuwanta gidan komai ta daina, ba su da aiki sai kallo da hira a waya. Shi ya sa na ce ba zan ɓoye maka komai ba gara na sanar dakai fare zamu taho in an yi bikin."
Saboda dariya Mufid har tuntsira ya yi. Shi kuwa Huzaifah dariyar yake ƙoƙarin ɓoyewa, amma har sai da ta ci ƙarfinsa ya dara.
"Oh my God! Gaskiya you Grandma is so dramatic, I love her." Ya ƙarashe maganar yana kallon Jannah ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye sai kuma ta share tana faɗin,
"Ai dama shi kansa ya san bai nemi aure inda matarsa za ta rinƙa masa kirki ba, in kin yi hakanne ki kunyata ni." Ta faɗa a tsiwace tana harararta.
"Au iyye a gabansa sai kin nuna halinki?" Ta ce tare da kama bakinta tana kallon ta. Sai ta juya kallonta garesa ta ci gaba da cewa,
"Ka gani ko? Allah na gode maka da ta nuna maka halinta. Yanzu da na ce maka fitsararriyace ba ta ganin kowa da gashi sai ka ji haushina, amma gara da ta nuna maka halinta ƙiri-ƙiri ka gani.Ita ɗin kura ce da fatar akuya. A waje kamar mutuniyar kirki."
"Oh common bab. Kin san ko wace irin mace kike ina sonki, saboda tsarinki da zubin ki duk sun yi mini." Ya ce mata bayan ya miƙa mata handkerchief ɗinsa, sannan ya juya yana kallon Hajiya Baaba da ta ɗaure fuska jin abin da ya ce don ita ba haka ta so ba, ta so ace ya nuna ba zai iya ba ko ta yi zuciya ta koyi aiki.
"Ba ki da matsala Hajiya Baaba, mu house is welcome to you at anytime you wish. Sosai kika burge ne Ina matuƙar son ki dawo gidana gabaki ɗaya da zama."
"Humh! Ka ji da gulman turancinka na bogi, ai ni ba na faɗa maka bane don na burge ka, na faɗa maka ne don na gaya maka gaskiya." Ta ce tare da juyawa za ta shiga kicin ganin haƙarta ba ta cimma ruwa ba.
Ajmal da ya yi sallama ya shigo don kawo mata maganin da tun safe ta addabe shi da kira ba ta da lafiya, amma ga mamakinsa tun daga ƙofar ɗakin ya fara jiyo muryarta tana zuba.
Idanu ya zuba musu bayan ya yi sallama ya shigo. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita musu magana ba duk da ganin yadda suka yi razana don sun É—auka har su tafi ba zai shigo ba.
Da sauri Huzaifah miƙe zai bi bayansa amma sai Jannah ta hana shi,
"Lemme go and great Babban Yaya."
"No you don't have to do that."Ta ce tare da riƙe gefen rigarsa tana girgiza masa kai cikin rashin karsashi domin gabakiɗaya Hajiya Baaba ta ɓata mood ɗinta.
Sun daɗe suna hira har sai da suka gaji don kansu suka yi wa Hajiya Baaba sallama suk tafi bayan sun cika lalitarta da bugun Abuja wanda ta rinƙa shi masa albarka kamar a ta goya su.
"Wayyo Allah! Tun shigowa Ya Ajmal na rasa sukuni. Ni kam mun bani Allah ya sa karya gayawa Aby." Cewar Jannah tana dafe ƙirjinta ganin motar su ta ɓace daga gurin.
"Amin, ni wallahi har sai da cikina ya murÉ—a. I was thinking that he would embarrassing us in front of him, but thankfully he didn't."
"He never try that, cus i won't stay an watch it." Cewar Jannah cikin É—aure fuska, sai kuma ta juya tana kallon hanyar da suka bi.
"Kin san Allah yau ni da Hajiya Baaba a gidan nan about what she did to me I was very devastated."
Dariya ta yi ta ce," To me za ki yi mata kamar ba ki santa ba, ki ƙyaleta kawai kar ki ja ma kanki. Allah I was expecting that, infact more than that from her. Kawai dai we don't have any options ne shi ya sa."
Ƙuta ta yi ba ta ce komai ba ta buɗe get ɗin suka shiga.
Washegari da safe ko breakfast ba su yi ba kiran dad ya riske su. Gwalalo idanu suka a tare.
"Kai anya kiran nan ba lafiya ba fa. Ni fa kallon da Ya Ajmal ya yi mana na san dole sai ya kai ƙararmu gurin Aby, don ya cika gulma kamar ba malami ba." Cewar Jannh da ta miƙe cikin tsoro.
Ita dai Ummu ba ta ce komai ba ta miƙe har ta murɗa ƙofa sai ta dawo ta kalleta,"Don Allah ki yi sauri kin tsaya sai kuma mun ƙara wani laifin."
Ta faɗa ranta a ɓace ganin ƙoƙarin zama take wanda ya sa ta miƙe suka fice da sauri.
Ganin Hajiya Baaba zaune a kan kujera tana ta girgiza da kaɗa ƙafa jikinsu ya ba su ba lafiya ba.
Da sauri suka durƙusa a tare."Ina kwana Aby."
"Rufe mini baki shashashun banza! Ina kallon ku masu hankali har na barku kuke zaman hostel ashe wawaye ne ku ban sani ba?"
Aby ya furta murya a zafafe," A'a Muhammadu ka san ba zan ɗauki hakan, wanda na san duk zugin wannan munafukin ne. Ai tun da na ga ya shigo ya ije maganin ba tare da ya ce komai ba na san sai ya haɗa munafunci. In ban da gulma tun yaushe na rinƙa kiransa ya siyo mini, amma da yake isashshe ne bai zo ba sai da gulmarsa ta kawo shi."
"Haba Hajiya Baaba, ya muna ƙoƙarin gyara za ki ɓata kuma." Sai ya juya gun su.
"Ke Jannah da gaske kun kawo saurayi gidanan?"Ya ƙarsa maganar cikin tsawa.
"To laifi ne hakan Muhammadu? Na ga shi mace ya aje a gidansa yana hutawarsa. Ko so yake mu rinƙa ado da su a ƙofar gida? In ban da gulma da sa ido waɗannan tiƙa-tiƙan da 'yan matan da ba bu abin da suke yi, sai warin balaga za a tsaya ana tambyarsu don sun kawo maza gida zance."
Zare ido suka yi suna kallonta,"Warin balaga?Kai amma Hajiya ta cuce mu duk irin ƙanshin da muke yi." Jannah ta ce tana hararar ta tare da shinshina jikinta.
"Ni fa ba aure zan yi ba kuma abokina ne. Bayan wannan babu abin da ke tsakaninmu." Ta furta cikin rashin shakku da tsoro.
"Gabakiɗaya ke kike ɓata yarannan Hajiya. Idan aure za su yi ai babu wanda zai hana su, amma sa bari su yi zurfi a karatunsu. Duka fa yanzu suka zana jarraba na first semester, ko Nahlin sai da ta kai 3 hundrent level za ta yi aure."