← Book details Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 79

Sashe 44

Kura Da Fatar Akuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da ma na san kashi da tusa duk nice a gidannan, saboda n bi ta bayan gida an shanye ka. Ni dai auren ƙabila babu abin da ya ja mini sai shata layi a tsakanina da ɗana. Ƙiri-Ƙiri ina ji ina gani an yi mini faƙara'u an raba ni da ɗana. Wallahi sai Allah ya saka mini." Ta ce tare da ƙara saka kuka tana share hawaye sai kuma ta kalle su Jannah da idanunta da kamar ba kuka take yi ba dai dai lokacin da Aby fara cewa,

"To yanzu don Allah mene na kawo wannan maganar a gaban yara? Na ɗauka mun riga mun zama ɗaya." Ya ƙarasa cikin jin zafin abin da ta furta yana kallon Amy lokacin da ta miƙe za ta shige ɗakinta hawaye na bin fuskarta.

"Dallah kyale ni! Sai a dake ni a hana ni kuka." Ta ƙarashe maganar tana kallon Ajmal da ya yi dana-sanin maganar.

Zuciya ta ciyo shi kawai ya ɗaga ƙafarsa ya kai musu ita da nufin ya haure su.

"Shikenan, ba ni da damar tsawata musu sai ta shige ta hana hakan? Kalli kansu Aby gabakiɗa atach ne a kansu, saboda iskanci sun tare a hostel babu mai tsawata musu sai sheƙe yarsu suke yi. Malaman islamiya sai magana suke ba sa zuwa islamiya da hadda."

Ya fara ƙoƙarin nemo bulala ya co gaba da faɗin,"Saboda iskanci a maimakon Ummu ta yi ƙoƙarin a ƙwato ta daga halaka, amma sai ta biye mata suna iskancin su babu mai kwaɓa musu."

Ƙara suka saki tare da ɓoyewa a bayanta.

Hajiya Baaba ta juya ta kalle su tare da wafce É—ankwalin Ummu ta girgiza kainta.

"Kuma fa in anbi ta ɓarawo, abi ta maji sawu. Ni kaina wannan uban gammo da suka ɗaura a kansu yana damuna, in dai akan wannan ne ba zan haka ba ka yi mini ƙasa-ƙasa da su."

"Ma za suje da direba ya kwaso kayansu babu wacce za ta ƙara kwana a hostel, in ba za ku yi karatun a gida ba ku bar shi, tun da aure kuke so sai ku kawo miji."

Jin abin da ya ce hankalinsu ya tashi ba kamar jannah da har ta fara kuka.

"Kuma awa É—aya na baku ku kwance wannan gashin in ba haka aski zan yi muku." Ajmal ya ce tare da yarda bulalar ya fice, sai kuma ya dawo lokacin da suke hararar Nahlin da take musu dariya ciki-ciki.

"Ke Nahlin da ga yau ƙarki ƙara aiki komai su za su yi, kafin su tafi makaranta ki tabbatar da sun yi aiki gudan nan, sannan a wata uku nake su iya girki." Ya fice daidai lokacin da ta amsa masa.

"Ai wallahi gara ya yi musu haka dama ni zaman makarantar nan sam bana son shi domin Jannah ƙara lalacewa za ta yi." Ta fice ba tare da ta damu da yadda take kallonta ba, yayin da zuciyarta fari ƙal tamkar farin takadda, don Allah kawai ya san halin da ta shiga da ta koma makarantar.

Suna shiga ɗaki tasa ihu tana didddira har sai da ta faɗi ƙasa.

"Duk ke kika ja mini wannan bala'in da yanzu na bi Sham duk wannan tashin hankalin bai same ni ba." Ta gallah mata harara tana faÉ—in hakan.

"Na tsane shi wallahi. He just like thread in my life, threatening me all the time for what reasons?"

Tsayawa jikin mirrow ta yi tana kallon yadd kitson ya ƙawata fuskarta, ta yi ƙuta tare da faɗawa kan gado tana girgiza gashin dokin.

"Yanzu duk kyan da na yi haka zai sanya na tsefe shi saboda rashin mutunci da shegen sanya ido? Wallahi sai Allah ya saka mini."

Sallama Nahlin ta yi ta shigo cikin fuskar dariya ta zauna gefen gado.

"Please Anty Nahlin, we are not in the mood and you have to respect yourself. You know respect is reciprocal."

"And what?" Ta ce Ummu jin abin da ta fada tare da daure fuska, amma cikin zuciyarta dariya kunshe ganin yadda Jannah ta yi da fuska.

"I came to pass a message. Ya ce na gaya mu haddar shafi goma za ku bayar gobe, don haka sai ku fara karatu, sannan gobe zan fara koya muku girki tun da muna hutu sai kuyi amfani da damar ku."

Wani uban tsuka suka ja."Ya ce mu sauke kur'anin a gobe mana, in yana ƙaryar malinta. Ni wallahi haushi yake bani, in ya ga damar zai zama ustazu dole sai koya ya zama irinsa. Ai tsoron Allah a zuciya yake." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta kunna data ba tare da ta ƙara kallonta ba.

"Na rantse ko shafi biyu ba zan kawo ba don ban iya ba." Cewar Ummu.

"Ki gaya masa gobe menstruation É—ina zai fara kuma kin san wahalar da nake sha don haka ba karatu." Jannah ta furta tare da shigewa bayi.

"A lallai wuyanki ya isa yanka ƙaramar mara kunya. Ai sai kije ki gaya masa." Cewar Nahlin.

Dariya Ummu ta yi." Ke da ya aiko ke za ki gaya masa, haka kawai duk kin bi kin takurawa rayuwarmu."

"Kan ku ake ji." Ta bata amsa tare da harararta ta fice.

Taba fita daidai lokacin da ta fito daga bayin."Wai a ƙwato ni daga ɓata, wato na kafurta kenan na shiga ɓata? Gani 'yar jujal jikar sheɗan." Ta ce cikin ɓacin rai.

Sai kuma ta sa kuka tana faÉ—in,"Wallahi Allah ya isa kuÉ—in da na biya, ni ba ma wannan ba yadda zan ita tsefe gashin nan in just one hour? Imagined."

Ummu ba ta ce komai ba ta fara tsifar don ta ga surutun cinye lokacin da ya ba su yake yi.

Ganin haka ta ɗauki masilla ta yi tare da ƙwala wa Talatu da Atine kira da su ta ya.

"Ya rinƙa wani behaving as if he is the most ethical and the most decent person in the world, bayan yaudaren kansa yake ɗan ƙauye kawai. We are in twenty first century he should have known that."

Kan dole babu yadda za su yi suka hau tsifar wanda kamar yadda ya basu awa É—aya ba ta cika ba sai dai suka gama. Tsabar haushi ko lunch ba ta ci ba sai cika take tana batsewa.

Bayan sun gama suka je suka kwaso kayansu duka.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

KURA DA FATAR AKUYA

*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)

Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.

*PAGE 19-20*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

LONDON
Mom zaune akan kujera da wayarta tana waya, oder take bayar wa na kalan furnitures É—in da za a sanya mata a gidanta.

Dad ya fito daga ɗakin cikin shirin fita yayin da jakarsa sagale a kafaɗunsa sai ƙamshi yake yi.

ÆŠagowa ta yi ta kalle shi tare da mai da kanta ta ci gaba da wayarta. Tsayawa ya yi tamkar gunki har sai da ta kammala ta kashe wayar sannan ta juyi ta kalle shi, bayan ta ije wayar akan kujera.

"Ranki ya daɗe na fito zan kai tsaƙon nan airport and daga nan I will heading to office."

"Ok, but amh. Mun yi magana da Governor I think we must go back to Nigeria within two weeks, because of the campaign and I can't go may be you will go on behalf of me an.."

"No way Halima." Ya ce tare da É—aure fuska sannan ya É—ora da cewa,"You know I do not support you in to politics ina ganin it should be better ki bar maganar na..."

"Oh please stop Injiniya, will you represent me or not?" Ta tambaye shi cikin É—aga murya.

"I will not cus am not you errand boy am you husband."

"Ok, fine." Ta kwashi tarkacenta ta shige É—akinta daidai lokacin da ya saki tsaki ya fice daga gidan zuciyarsa a jagule.

NIGERIA
Nahlin ta tashi da asuba bayan ta yi wa su Adal karatu ta zauna tana ɗan gyangyaɗi tana jiran shigowarsu, amma har ta gaji ba ta ga ƙeyar su ba.

"Kai ni kam waɗannan yaran sun ishe ni, Ya Ajmal ya ɗora mini wahala. Miƙewa ta yi ta nufi sashin Hajiya Baaba.

Turus ta yi bayan ta buÉ—e É—akin ganin har yanzu babu wacce ta farka da alama ko sallah ba su yi ba.

"Lailai yaranan ba su da hankali sun raina Yaya wallahi."

Duka ta kai musu tana faÉ—in,"Ku tashi marasa mutunci ayi ta maimata muku magana É—aya, sai ka ce wasu kurame haba."

"Wallahi an takurawa rayuwarmu wai baccin safen mutum ba shi da ikon yi. Da hostel ne in bamu da lecture sai mu kai ƙarfe sha biyu muna bacci." Cewar Jannah.

"Aiko an yi asara." Ta ba su amsa sannan ta É—ora da cewa,

"Ba wannan ya kawo ni ba don ina da abin yi. Za ku yi karatun ko na kira shi."

"Taɓ! Allah na tuba, ai da wuya na haddace ko aya biyu gara Ummu na ga ta yi karatu kafin ta kwanta, kuma ta tashi da daddare."

"Ni ma bai zauna ba Allah." Cewar Ummu tana turo baki.

"Allah ya shirye ku wallahi. Yara sai kace kafuran farko, ko kafuran aljanu sun shiga jikinku. Ni kama bari na kira shi kun fi ƙarfina."

Riƙe hannunta suka Ummu ta ƙwace wayar tana faɗin,"Haba our unique Anty, it hasn't gotten to that. Yanzu zamu fito. A dai yi ma uren nan na ki mu huta."

"Allah ya sa ita ma ba kusa da gida za ta sanya a gina mata gida ba don ta takura mana."

Ta furta tana ƙoƙarin tuɓe rigar baccinta.

Dariya ta yi ta sa kai za ta wuce tana mamakin halin ƙanninnata da take matuƙar so sosai.
Chapter 44 · 0% Book details