Sashe 9
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*"Wallahi Nadiya ba zan bari ki ajiye jaririyar nan a cikin wannan gidan ba, shin kin yi hauka ne da har zaki kawo min wata baren yarinya cikin gidana?, Nadiya ki fita daga idona na rufe, kada ki bari na chanza daga yadda ki ka sanni a da. Idan har kina son zaman lafiya to ki san yadda zaki yi ki fitar da yarinyar nan daga cikin gidan nan".
Hawaye nurse Nadiya taji suna ƙoƙarin sauko mata, saurin share su ta yi sannan ta ce. Shi kenen zan yi kamar yadda ka ce amma ka bari na bata abinci ko cerelak ne saboda na san tana jin yunwa sosai gashi ko shayar da ita ma ba'a yi ba".
"Shi kenen". Mijin ya faɗa tare da shige wa ɗaki. Maida kallonta nurse Nadiya ta yi kan jaririyar ganin yadda take ta faman kuka ya sa ta miƙe tsaye tare da nufar cikin kitchen domin haɗa mata cerelak. Cikin ƙanƙanuwar lokaci ta gama haɗa wa yayin da ta fito da cerelak ɗin cikin ɗan ƙaramin fida da alamu ita ma tana da ƴa ko ɗa. Ajiye fidar ta yi kan table sannan ta ɗauki jaririyar daga kan kujera ita kuma ta zauna, yayin da ta ɗora jaririyar ksn cinyarta sannan ta fara bata cerelak ɗin tana sha.
Saida ta gama tsaff sannan ta kuma yi wa yarinyar wanka a karo na biyu. Yayin da ta shigar da ita É—aki tare da saka mata kayan jariran da mijinta ya siyo domin yaranta.
Sakawa yarinyar su ta yi yayin da kayan suka yi wa yarinyar kyau tare da karɓar jikinta. Nan da nan bacci suka kwashi yarinyar. Ganin hakan ya sa ta ɗaukar towel tare da goya yarinyar a bayanta sannan ta shiga toilet tare da ɗauro alwala. Bayan ta gama ne ta fito daga toilet ɗin yayin da ta ɗauki dadduma tare da hijabi sannan daga bisani ta tada sallah.
Bayan ta idar da sallan ya sa ta fara azkhar tare da lazumi yayin da ta fara kaiwa Allah kukan ta.
Bayan ta gama ta miƙe tsaye tare da nufar hanyar palour. Zuwanta keda wuya ta tarar da mijinta riƙe da akwati yayin da yake s tsugunne yana ƙoƙarin buɗe akwatin.
Da mamaki ta bishi da kallo sannan ta ce. "Mai gida me kuma zaka yi da akwati a wannan tsakar daren?".
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce. "Wannan akwatin ina zuge shi ne domin mu saka yarinyar a ciki sannan mu jefar da ita kan titi kinga duk wanda ya tsince ta ya yi sa'a sai ya riƙe ta".
Saurin ja da baya nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Wannan ai rashin adalci ne, ta ya ya muna ji muna gani zamu saka marainiyar Allah cikin wannan akwatin, zafi ma kaɗai ya ishe ta. Kuma mu rasa inda zamu ajiye ta sai bakin titi. Mundin ina nan to ba zan taɓa barin hakan ta faru ba".
Miƙe wa mijin nata ya yi sannan ya fara tunkaran inda take. Bai yi wata-wata ba, ya zuba mata lafiyayyun maruka har guda biyu. Dafe ƙuncin ta nurse Nadiya ta yi yayin da jaririyar dake kwance s bayanta ta yi matuƙar razana da jin sautin. Nan take ta fara kuka.
Ɗago idanuwanta Nurse Nadiya ta yi wanda suka ciko da hawaye. Nuna ta mijinta ya yi da ɗan yatsarta sannan ta ce. Mundin baki bi umarni na kinyi abin da nace ba, wallahi sai kin gane cewar Allah ɗaya ne. Domin ni ba zan lamunci naje magarƙama saboda wannan yarinyar da dangi uwa ba ba dangin uba ba. Don haka kiyi min shiru ki miƙo min yarinyar naje na jefa ta a chan bakin titi".
Girgiza kai nurse Nadiya ta yi tare da fara ja da baya ta ce. "Ba zan taɓa miƙa maka wannan yarinyar ba sai dai ka kashe ni idan zaka iya amma ba zan bari ka jefar da yarinyar nan ba, domin ba alƙawarin dana ɗaukar wa mahaifiyar ta ba kenen".
A fusa ce ya yi kanta tare da fuzge zanin da ta goya yarinyar dashi. Nan take jaririyar ta faɗi ƙasa yayin da kanta ya bugu da jikin table dake tsakiyar falon. Nan take yarinyar ta fashe da matsanancin kuka mai sauti.
Ture nurse Nadiya mijin ya yi yayin da ta faɗi ƙasa. Maida kallonsa ya yi kan jaririyar tare da miƙa hannu ya ɗauke ta sannan ya nufi inda akwatin yake da jaririyar.
Saurin riƙe ƙafar sa nurse Nadiya ta yi hawaye na zarya kan ƙuncinta ta ce. "Na roƙe da girman fiyayyen halitta, kada ka jefar da yarinyar nan, kayi tunanin idan da ƴar kace a kayi mata haka zaka ji dad'i, dan Allah ba dan ni ba kodan duban halin maraicin da take ciki na rasa kowa nata ka kyale ta. Dan Allah na roƙe ka, idan kace zaka yi haka, zaka shiga hakkin marainiya, ka taimaka ka ƙyale ta". Ta faɗa tare da fashe wa da kuka.
S hassale ya wafce ƙafarshi daga hannunta ya yi ya sa ƙafarsa ta dama tare da naushin cikin ta. Take nurse Nadiya ta saki wata iriyar razananniyar ƙara, nan take idanuwanta suka fara lumshe wa. Kallon jaririyar dake hannunsa ta yi sannan ta ce. "Allah ga baiwar ka nan, ka kare ta a duk inda take sannan ka shiga cikin alamuranta, ka sanya maƙiyanta suyi danasanin abubuwan da suka aikata mata tare da sauran ƴan uwan ta mata. Ya Allah ka saka yarinyar nan tare da sauran ƴan uwanta sune za su zamo jagororin wannan garin, yayin da maƙiyansu waɗan da suka yi sanadiyar faɗawarsu cikin wannan mummunan yanayin su zo suna duƙa musu". Tana kaiwa nan ta yi shiru alamun ta suma.
Saka yarinyar mijin nurse Nadiya ya yi cikin akwatin yayin da ya nufi hanyar waje da ita. Saka akwatin ya yi a bayan mota yayin da kukan jaririyar kawai ka ke ji domin ta kasa shaƙar iska daga cikin akwatin yayin da idanuwanta waɗan da suke blue suka ƙara rinewa sosai saboda kuka. Buɗe gate ya yi yayin da ya koma jiki motan tare da shiga ciki.
Tada motar ya yi daga bisani ya fita daga cikin gidan.
Saida ya yi tafiya mai nisan gaske yayin da gaba É—aya mutane sun rurrufe shagunan su saboda dare ya ratsa sosai. Chan ya samu guri a tsakiyar titin da ba bu kowa ko mai wuce wa balle a samu mai ganinsa ya yi parking É—in motar. Sannan ya fito daga cikin motan tare da buÉ—e bayan boot. Fito da akwatin ya yi daga cikin motan. Saida ya tabbatar da ba bu mai ganinsa sannan ya ajiye akwatin a tsakiyar hanya inda mutane ke wucewa sannan daga bisani ya bar wajan da sauri tare da shige wa cikin mota ya bar harabar wajan baki daya.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Ohh waɗan nan ƴan ukun suna ganin rayuwa tun kafin sun san mene ne ciwon kansu, ko yaya zata kasance da jaririya mai blue eyes?, yanzu ɗaya na daji tare da namun jeji, ga kuma ɗaya a magarƙama, yanzu kuma ɗaya na bakin hanya sannan yaya girman su ukun zai kasance?, ko ta ya ya za su hadu da juna nan gaba sannan su san su ɗin su uku ne. Muje dai zuwa domin jin yadda zata kasance*.
COMMENTS & SHARE FISABILULLAHI ðŸ™ðŸ™ðŸ™
ALKALAMIN âœï¸
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZinariyarðŸ§â€â™€ï¸Jajirtattu)
https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G

Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*ðŸªðŸŒŽðŸª.
Daji 🌲
Magarƙama🢠da kuma
BirniðŸ™ï¸
WRITTEN & DIRECTED BY âœï¸ A'ISHA M.B 💞💞💞
(ZinariyarðŸ§â€â™€ï¸Jajirtattu)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 âœï¸
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Æ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauÆ™i_.âœï¸
*DIAMOND 💎 STARâ*
*LADIES ðŸ§â€â™€ï¸ðŸ§ðŸ¼â€â™€ï¸ðŸ§â€â™€ï¸*
*(We stand together)*
ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤
بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 9ï¸âƒ£â–¶ï¸ðŸ”Ÿ
*_________________________________________________*
Ba bu abin da jaririyar ke ta faman yi sai kuka, yayin da namun jejin suka bita da kallo. Nan take wasu daga birrirukan suka fara arewa kan bishiya yayin da suka nufi gidan zuma tare da É—aukar kashin zuma suka nufi inda jaririyar take.
Suna isa suka saka mata a baki, nan take ta fara tsotsan zuman tana yi tana kuka. Ɗaukar ta gwagon biri ya yi tare da ɗora ta kan cinyarsa, a yayin da ya yi mata lulluɓi da ganye sannan ya fara bata zuman da kansa.
Nan da nan gaba É—aya namun daji suka tsaya tare da zagaye su. Nan take jaririyar ta kalle su tare da sakin murmushi.
**Saka shi suka yi a cikin cell yayin da suka fara jibgarsa ta ko ina, saida suka tabbatar ya jigata sannan suka ƙyalesa. Zama DPO ya yi yana kallonsa ya ce.
"Shin wane ne ya tura ka don ka taimaki Mrs Laila?, ba za ka faɗa ba ko sai an ƙara maka duka?".
Ɗago da rinannu isanuwansa ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ni ɗin jami'i ne, kuma doka bata yarda jami'i ya daki jami'i ba tare da wani ƙwaƙwaran hujja hakan abin da ya aikata ba, sannan kotu bata baka damar yin hakan ba, mundin kotu ta gano to tabbas sai an cika tarar maƙudan kuɗaɗe sannan kuma a dakatar da kai daga aiki".
Baki sake DPO ke kallon ɗan sandan sannan ya ce. "Ni tun da nake ban taɓa ganinka a cikin rukunin ƴan sanda ba, ƙarya ka ke kai ɗin ba ɗan sanda bane, so dai ka ke ka faɗi abin da za ka kare kanka da shi, to ni kuma ba zan bar hakan ta faru ba, mundin ina nan saina tabbatar da cewa kotu ta hukunta ka bisa ƙwaƙwaran hujjoji da nake dasu a kanka. Don haka ka faɗa min gaskiya domin a sassauta maka hukunci da za'a yanke maka".
Murmushi ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ko za ka kai gobe kana duka na tare da tambaya na ba zan taɓa faɗa maka ba, sai dai kayi duk abin da ka e ganin za ka yi".