← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 59

Sashe 12

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take ta dira a ƙasa tare da baza gashin ta. Masha Allah na iya furta wa lokacin da nayi kicibus da kyakyawar fuskarta wanda ke lulluɓe da farin ciki da annashuwa. Sanye take ciki kaya wanda alamun birrurukan ne suka yi mata, domin gaba ɗaya kayan anyi amfani da ganyayyaki wajan sa ƙashi ne.lumshe green eyes ɗinta ta yi tana mai mai da kallonta kan namun jejin sannan ta musu ciki yaren ko ni kaina ban sani ba".

Nan da nan suka girgiza kai gaba É—aya tare da watse wa . Yayin da birrurukan suka fara aye wa kan bishiyu suna É—iban fruits É—in da ke kai wato kayan marmari.

Ganin gaba É—aya sun watse ya sata sakin murmushi, sannan ta yi wani irin tsalle. Nan take ta dira a kusa da wani jibgegen dutse wanda ke zaman kansa a cikin dajin.

Ajiyan zuciya ta sauke Tare da nufar katoton ruwan dake cikin dajin. Sannan ta shige ciki. Nan take ta fara wanka. Ganin hakan ya sanya birrirukan suka fara saukowa daga kan bishiyu, sannan suka É—auki ganyayyaki suka tunkari inda take.

Nan take suka zagaye ta da ganyayyakin tare da kare ta dasu.

Sai da ta gama wankan sannan ta fito daga cikin ruwan. Fitowa ta yi ta ga sun zagaye ta da ganyayyaki sannan sun shirya mata kaya na ganyayyaki wanda zata saka.

Murmushi ta sakar musu wanda ya sanya dimple ɗin ta ƙara lotsawa.
Cikin yaren su na birirruka ta ce. "Na gode sosai ƴan uwana, ina matuƙar alfahari da ku, ina sonku sosai soyayya mara misaltuwa". Ta faɗa tare da janyi kayan ganyen da suka ajiye sannan ta saka.

Fitowa ta yi daga cikin ruwan. Ganin ta sanya kaya ya saka suka ajiye ganyen da suka zagaye ta da shi.

Tafiya ta fara yi tare da nufar inda dutse dake gabanta yake. Sai da ta ƙarasa wajan sannan ta zauna tare da jingina a jikin dutsen. Shafa jikin dutsen ta fara yi tana mai shafa sunan Amrah dake rubuce a jiki.

Nan take fuskanta ya chanza daga walwalah izuwa damuwa. ganin kamar tana ƙoƙarin shiga cikin damuwa ya sa su birrirukan suka tunkaro inda take yayin da suma sauran namun jejin suka nufo inda take. Nan da nan gwagon biri ya ɗauke ta chakk tare da cilla ta sama. Nan take farin ciki ya lulluɓe fuskar Amrah. Nan da nan suka shiga yin wasa abun gwanin burgewa. Ajiye ta gwagon birin ya yi tare da ajiye Amrah a kan wata ƙaramar giwa, nan take giwar ta fara tafiya da ita tare da yawa ta da ita yayin da sauran namun jejin ke mara musu baya.

*AMERICA*
"What is wrong with you Safeera?, wannan ba tarbiyyar da na baki bane ba, me ya sa za ki dinga zuwa club for God sake?, sunanki Safeera amma kin mai da sunanki Diana saboda bakya jin tsoron duk abin da zai je ya dawo ko?". Matar ta ƙarashe maganar ranta a matuƙar ɓace.

Miƙe wa zaune wacce haka kira Safeera ta yi sannan ta dubi mahaifiyartata cikin shagwaɓa ta ce. "Am sorry Mom, wallahi zan daina zuwa club sannan na daina saka waɗan nan matsatsun kayan kinji. Banason ina gani kina shiga damuwa saboda ni , i promise you that I will change, kuma sunan Diana ƙawaye na ne suka saka min a makaranta, amma zan ce kar su ƙara kira na da sunan kinji". Cewar Safeera.

Murmushi Mom ta sakar mata sannan ta ce. "Don't forget that promise is a debt".

Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda take sannan ta zaunar da Mom ɗin tata ta ce. "Yes Mom, I promise I will never hurt you again because I love you so much Mom".

Rungume ta matar ta yi sannan ta ce. "That's my baby I love you more than you do".

Jin shigowar mutum ya sa su miƙe wa tsaye tare da maida kallonsu inda suke jin takun mutum.

Washe baki Safeera ta yi yayin da ta tafi da gudu tare da rungume shi.

"Welcome back daddy, I really missed you". Ɓanɓare ta daga jikinsa mutumin ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Oh my cute baby, wai yaushe za ki girma ne?, so ki ke ki ɓalla ni, ji fa yadda ki ka tawo ki ka rungume ni".

MurguÉ—a baki Safeera ta yi sannan ta ce. "idan ka karye ai sai na fi kowa shiga damuwa". Ta faÉ—a tana mai kwashe wa da dariya.

"Shi ke nen tom naji, wai ina Mom É—in ki take ne?, ta zo fa na dawo mata da good news". Cewar Daddy.

Daga bayansa yaji ta ce. "Ai gani nan my one, ba saika neme ni ba". Cewar Mom.

Da sauri yaje tare da rungume matar ta shi sanann ya ce. "Na tawo miki da good news, maza ku zauna".

Zama suka yi suna mai fuskantarsa. Kallon su ya yi sannan ya ce. "Akwai É—an yahya na yau ko gobe zai zo neman auren Safeera, kunga idan haka yi engagement a nan sai mu koma Nigeria da zama tun da anyi min transfer É—in wajan aiki na koma Nigeria, kuma wanda zai zo neman auren ki shi É—in police officer ne, kinga zaki kasance koda yaushe kina da tsaro".

Miƙe wa tsaye Safeera ta yi sannan ta ce. "NI banason nayi aure yanzu, kuma ba zan je Nigeria ba. Ni a nan zan ci gaba da zama. Ko da karatu ban gama ba, amma shi ne za'a kawo min maganar aure. Ni dai gaskiya ba zan taɓa auran wanda zaku kawo min ba domin ni banason aure yanzu karatu nake so na ci gaba".

Miƙe wa Daddy ya yi ranshi a matuƙar ɓace ya ce. "Kina nufin ba za ki bi umarni na ba kenan?, ɗan yahya na ne fa zai zo neman auren ki, shi ne za ki ce bakya so, to ki kina so ko bakya so sai anyi engagement ɗin nan, kuma karatu daga yau na dakatar da shi,bake ba ba karatu".

Fashe wa da kuka Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi ba za'a min aure a wannan shekarun nawa ba". Tana kaiwa nan ta shige ɗakin ta tare da rufe ƙofar ɗakin.

Maida kallonta Mom ta yi kan Daddy sannan ta ce. "Daddyn Safeera ina ganin kamar kada mu tilasta mata, tun da bata so kawai mu rabu da ita ta yi karatun tun da shi take so".

Kallon Mom Daddy ya yi sanann ya ce. "Kiyi min shiru Zainab, dama kece ki ka sangalta yarinyar nan ta zama haka. To ki jini da kyau ko tana so ko bata so wannan engagement É—in kamar anyi an gama ne, sai dai ba bu numfashi a tattare da ni".

*LONDON*.
Kwance yake a kan faɗeɗen gadonsa mai matuƙar girma, yayin da ya rufu da bargo mai matukar laushin gaske.
Ba bu abin da ke tashi a ɗakin sai ƙamshi da ƙaran Ac. a hankali ya ta shi zaune. Tabbas dukkan yabo da jinjina za su ci gaba da tabbata ga Allah SWA wanda ya yi wannan kyakyawan halittar. Lumshe fararen idanuwansa ya yi masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.

Wayarshi yaji tana ruri. A hankali ya duba kan table É—in da ke kusa da shi yayin da ya ga sunan Abba bayyane kan screen É—in shi.

Ɗaukar wayar ya yi yayin da ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnensa sallama riƙe a bakin sa. Daga ɗayan ɓangaren haka amsa sallamar. Sannan naji an ce. "Umar yaushe za ka dawo Nigeria?, na faɗa maka cewar ina so a fara aiki a wannan dajin domin a fara gina wannan company, nayi magana da engineers ɗin da za su je suga yadda girman dajin yake, amma an ce akwai namun jeji a wajan dole sai an kore su. Ya kamata ka dawo Nigeria domin a san abun yi".

Ajiyan zuciya Umar ya sauke, sannan ya ce. "Shi ke ne Abba, in sha Allahu zan dawo nan da next week. Ya maganar zaɓe ko har yanzu ba'a fara ba. Ni a tawa shawarar Abba ya kamata ka ajiye govnor wallahi, kamata ai a ce kana hutawa a gida, ka bari wani ya hau kawai".

Murmushi Abbban na shi ya yi sannan ya ce. "Ai kuma kaga ba zai yiwu ba domin ni buri na shi ne na idimtawa al'umma da ƙasar baki ɗaya. So kaga aikin lada kawai nake bawai saboda kuɗi ba ko mulki".

"Shi ke nen Abba ba bu damuwa, zan dawo ko cikin week É—in nan ne".

"Okay son Allah ya dawo mana da kai lafiya". Amsa wa Umar ya yi da Amin daga bisani ya kashe wayar.

Miƙe wa tsaye ya yi tare da ɗaukar towel ya shiga toilet. Sai da ya ɗau lokaci sosai kafin ya fito daga cikin toilet ɗin ƙugunsa sanye da towel, sannan ya nufi wajan dressing mirror. Ɗaukar mai ya yi ya fara shafa wa. Sannan ya ɗauki wani oil tare da shafa wa a sumar ƙanshi wanda suka kwanta suka yi luff.
Ɗaukar turarruruka ya yi tare da feffeshe jikinsa da su. Nufar wardrobe ɗin shi ya yi tare da zaƙulo ƙananun kaya brown colour sannan ya sanya su. Nufar inda takalman sa suke ya yi, tare da ɗaukar canvas brown sannan ya sanya su. Bayan ya gama ya nufi inda yake ajiyan hulinanshi sannan ya ɗauki Pcap brown ya sanya. Sannan ya nufi inda yake ajiyan eye glasses ɗin shi sannan ya ɗauki daya daga cikin glasses ɗin shi wanda ke photochronic ya manna a fuskarsa. Nufar inda wrist watch ɗin sa suke ya yi tare da ɗaukar wrist watch rolex ya sanya a hannunshi. Gaba ɗaya abubuwan da sanya diamond 💎 ne.

Masha Allah kawai baki na ya furta lokacin da naga irin haÉ—aÉ—É—iyar shigar da ya yi wanda suka yi masa mugun kyau.

ÆŠaukar wayarsa ya yi yayin da kai tsaye ya shiga contact list. Nan take naga ya danna kiran sunan officer. Ringing biyu haka É—auka.

Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Peace be unto you Sir, hope everything is going we'll?".
Chapter 12 · 0% Book details