← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 59

Sashe 4

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin share ƙwallan dake shirin zubo mata Mrs Laila ta yi tare da miƙe wa tsaye daka kan gadon sannan ta durƙusa kan gwiwowinta tare da haɗe hannayenta guri ɗaya tana mai fuskantar nurse ɗin ta ce.

"Na roƙe ki da girman fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) ki taimake na fita daga wajan nan na samu na tseratar da rayukan yarana sannan na ceci tawa rayuwar. Bana son na mutu ba tare da gaskiya ta yi halinta bah, ina so koda nan gaba yarana na su kasance sune waɗan da za su bayyana gaskiya sannan jama'a suyi alfahari da su, su kasance ababen faɗa na alkhairy a wajan jama'a. Ki tamaika min dan Allah". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka.

Tausayin ta ne ya kama nurse Nadiya. Saurin ɗaga Mrs Laila ta yi tsaye sannan ta ce, "Na dahimce ki kuma na tausaya miki matuƙa amma matsalar ba daga nan take bah, matsalar ita ce yanzu koda na barki ta ina za ki fita bayan ko ina a asibitin nan karaɗe yake da jami'ai tare da CCTV camera. Ya kamata kiyi ƙara nazari a kai saboda kin san yin hakan babban hatsari ne dole sai mutum ya shirya don koh a ƙofar gate ma akwai jami'ai Da ƴan jarida jira kawai suke ki fito su fara karɓar bayanai. Kuma sannan jariran ta ya ya za ki fita da su?".

Kallon nurse Nadiya Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Guda ɗaya zan ɗauka na bar ɗaya". What!" Nurse Nadiya ta furta. Cike da da mamaki ta ce, "saboda me za ki ɗauki ɗaya ki bar ɗaya bayan kuma duka yaran ki ne? baya sannan ma naji an ce kin haifi guda ɗaya a cikin magarƙama ga kuma biyu a nan. Idan ki ka tafi da guda ɗaya sauran biyun ya zaki yi da su? saboda me za ki aikata hakan?".

Haka nurse Nadiya ta shiga jera mata tambayoyi. Murmushi Mrs Laila ta yi tare da nufar inda jariran suke tana mai shafa fuskarsu ta ce.

"Ina so ne gaba ki É—ayansu su taso a gurare daban-daban a cikin wannan duniyar. Bawai zan raba su bane saboda wani kuduri nawa. Zan yi hakan ne kawai saboda tseratar da rayukan su sannan kuma su san mahimmanci da rayuwa take dashi. Ina da dukiya wanda yawanta ba zai misaltu bah kuma wannan dukiyan tun kafin na haife su na mallaka musu. Kuma hakan wannan property É—in makiya na za su iya kashe koh nawa ne domin yarana su saka hannu hakan wannan property É—in daga baya kuma su kashe su domin shi ne burinsu. Ni kuma ba zan bar hakan ta faru bah. Shi ya sa zan raba su, su rayu a gurare daban-daban yayin da kowaccen su za su kasance da uwa daban-daban. Daga baya idan sun girma su binciki tarihin su, tohh dole ne a dawo da shari'a sannan a bayyana gaskiya ta hanyar bayar da gamsassun bayanai".

Nannauyan ajiyan zuciya nurse Nadiya ta sauke sa'anan ta ce. "Shi kenen baki da wata matsala. Na miki alƙawari idan ki ka ɗauki ɗaya zan riƙe ɗaya koh kuma ba bawa duk wanda ya zo yana neman haihuwa zan bashi, idan kuma bansamu bah zan damƙa ta gidan marayu. Kuma sannan na miki alƙawarin ba zan taɓa cin amanar ki koh na yaudare ki bah. Amma kuma ina da wata tambaya, shin ta ya ya yaran gaba ki ɗaya za su haɗu bayan kuma duk a gurare daban-daban suke? kuma sannan ta ya ya za su san koh su ɗin su wane ne bayan kuma ba bu wani hujja da za'a fahimtar da su cewar iyayen da suke tare da su ba iyayensu ba asalin iyayensu ba ne? kuma wane ne zai basu property ɗin su?".

Murmushi Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Wannan ba abun damuwa bane gaba ɗaya bayanai da hujjoji suna tare da hajiya Binta a magarƙama. Ban faɗa mata komai ba saboda gudun cin amana, amma na san ba zata ci amana ta ba kamar yadda na saka ran cewa kema ba za ki ci amana ta bah. Kuma sannan haɗuwa da sanin asalin su za su fahimta domin Hajiya Binta zata sanar dasu ko mai".

Kallon ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Wace ce kuma hajiya Binta?". Amsa Mrs Laila ta bata da cewa, "hajiya Binta ita ce na zauna da ita a magarƙama kuma komai yana wajan ta hatta ta ukun su tana wajan ta".

"Shi kenen toh na fahimta yanzu dai abin da zamu yi domin fita daga cikin wajan nan shi ne dole na baki kayan nursing scrubs wato kayan mu na Nurse's ƙi saka saboda kada a gane ki sannan na baki face mark. Ita kuma jaririyar da za ki ɗauka ki saka ta a cikin troley na ƙasa amma dole sai na bata maganin bacci gudun kada ta yi kuka a gane. Bauan kin fita ni sai nayi ihuu na ce kin fasa min habu sannan kin gudu".

"Eh hakan ya yi shi kenen sai mu fara koh". Cewar mrs Laila. Nan da nan suka shirya kamar yadda suka tsara yayin da Mrs Laila ta saka kayan Nurse's ɗin wanda suka kwanta suka ƙarɓi jikinta sannan kuma ta bawa nurse ɗin kayan patient ta saka a toilet. Sai da suka gama shiryawa tsaff.

Sannan mrs Laila ta saka facemark tare da nufar inda jariran suke wanda gaba ɗaya sun lulaya duniyar bacci saboda wanka da gasa musu cibi da nurse ta yi tare da maganin bacci. Kallon su ta yi hawaye na bi bisa ƙuncinta ta ce. "Kuyi haƙuri ku yafe min, banso haka ta kasance ba, banida niyar raba ku amma dole ce ta sani zan raba ku. Kaddarar mu ce a haka kuma wannan jarabawar da zaku shiga, in sha Allahu sai kun tsallake ta". Ta faɗa tare da ɗaukar ɗaya daga cikin jariran mai green eyes sannan ta yi rolling ɗinta a cikin towel daga bisani ta saka ta a ƙasan troley ɗin wanda samansa ke rufe da kaya magunguna a kai. Maida kallonta ta yi kan nurse Nadiya sannan ta nufe ta tare da rungume ta ta ce.

"Insha Allahu ba zan taɓa manta irin wannan habun alkhairin da ki ka aikata a gare ni bah na gode sosai Nurse". Tausayinta da kuma yaran ne ya ƙara shiga zuciyar Nurse Nadiya ta ce. "Kada ki damu da wannan ɗan ƙaramin taimakon, idan da ina da halin yin fiye da haka ma zan yi. Kuma karki ƙara ce min Nurse suna na Nadiya ki ɗauke ni tamkar ƴar uwa kamar yadda ki ka ɗauki Hajiya Binta. Dan haka yanzu ki hanzarta ki fita kafin wani yazo ya ganki". Ta faɗa tare da cire ID card ɗin ta sannan ta sawa Mrs Laila a wuya.

"Kinga yadda ki ka yi kyau kuwa a cikin uniform ɗin nan, yacce ki ka san real Nurse, ba but wanda zai gane ki kinyi ɓadda kama sosai. Murmushi wanda bata yi tsamani shi ba ne ya suɓuce wa Mrs Laila sannan ta ce. "Na gode sosai Nadiya, Allah ubangiji ya baki damar sauke nauyin da ki ka ɗauka".

"Ameen". Nurse Nadiya ta furta. Mrs Laila na kaiwa nan ta riƙe troley ɗin sannan ta fara ja harta isa bakin ƙofa. Tsayawa ta yi tare da maida kallonta kan jaririyar dake kan gado sannan ta ce. "Nadiya duk wanda ya yi adopting ɗin ƴata kice mai ya kula min da ita sosai saboda ba dan banason ta na ajiye ta bah". Tana kaiwa nan ta murɗa hannun handle ɗin ƙofar tare da ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin.

"Dakata!". Ta ji nurse Nadiya ta furta. Tsaya wa ta yi chakk ba tare da ta motsa koda ɗan ƴatsarta ba. Ta kowa nurse Nadiya ta fara yi tana nufo inda Mrs Laila take. Nan ta ke gaban Mrs Laila ya shiga faɗuwa! Saida tazo kusada ita sannan ta miƙa hannunta tare da riƙe na Mrs Laila sannan ta saka mata kuɗaɗe. Nan ta ke Mrs Laila ta sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Na baki tsoro ne? ga kuɗi nan ba bu yawa na san zaki buƙaci kuɗin hawan mota da kuma kuɗin da za ki ɗan ci wani habu idan kina jin yunwa kuma sannan number na yana jikin Id card ɗina idan kina da buƙatar wani taimako ki kirani kinji".

Nan ta ke Mrs Laila ta ji ina ma a ce dukiyoyin ta na kusa da ta mallaka wa nurse Nadiya ɗaya daga ciki. Share hawayen da ke zarya kan ƙuncinta ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai Nadiya haƙiƙa ke ɗin mace ce ta ƙwarai kuma in sha Allahu saina saka miki da alkhairy".

Girgiza kai nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Ni banyi miki hakan ba domin ki saka min nayi ne domin Allah dan haka ki hanzarta ki tafi kada su shigo su tarar damu".

"Shi kenen". Mrs Laila ta furta Daga bisani ta fice daga cikin É—akin. Kallon ta jami'an suka yi yayin da suka ga kamar yanayin nurse da ta shiga da kuma wacce ta fito ya bambanta domin tafiyar da take yi tamkar mara lafiya.

Fargaba da tsoro ne ya cunkushe guri ɗaya a zuciyar Mrs Laila. Tafiya ta ci-gaba da yi a karkace da troley yayin da hannayenta da ƙafafuwanta ke kakkarwa saboda tsoro, gashi maranta bai daina yi mata ciwo bah duda cewar ta sha maganin relief. Saida taje har gaban gate zata fita taga an dakatar da ita.

Tsayawa ta yi tana mai kallon masu gadi. Daga gefe kuma police ne da sojoji sai Æ´an jarida zagaye a wajan. ÆŠaya daga cikin police É—in ne ya kalle ta ya ce. "Nurse ina kuma za ki je da troley bayan kuma ba'a fita da shi?".

Wani irin zufa ne ya fara ƙeto daga kowane sashe na jikin ta. Cikin ƙasa da murya ta ce, "Eh dama zan zubar da magunguna ne a shara zan dawo da troley ɗin".

Kare mata kallo police É—in ya yi sannan ya ce. "Shara kuma? bayan dustbin É—in asibiti ina kuma za ki je da wannan. Kuma yana ga kina magana kamar wata mara gaskiya, hanya ke nurse ce kuwa?".
Chapter 4 · 0% Book details