← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 59

Sashe 19

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zumbur gaba ɗaya suka miƙe tare da nufar kanta da sauri. Nan take suka ga ta dafa kanta yayin da zazzaɓi ya rufe ta shure-shure ta fara yi hannunta dafe da cikin ta. Nan take suka ga ta daina yin shure-shuren.

Zuwa kusa da ita Aliyu ya yi tare da saka hannunsa saitin hancin ta. Ganin bata numfashi ya da shi saurin É—ago da kansa sannan ya ce. "Safeera fa ta suma".

"Suma kuma?". Cewar Mom. Sannan ta ƙara da cewa. "Wai me yake faruwa ne?".

*TOH FAN'S 💃💃NI MA DAI ZANCE ME YAKE FARUWA NE🤔?, DAGA HARBIN AMRAH GABA ƊAYA SAURAN BIYUN SUN FITA A HAYYACIN SU, KODAI AKWAI ABIN DA KE FARUWA NE🤔?, MUJE DAI ZUWA*.

*KUYI MANAGE NA PAGE ÆŠIN NAN BANI DA CHARGE NE SANNAN KUMA BANA JIN DAÆŠI SOSAI. NA SO NAYI MUKU FIYE DA AKA AMMA KUYI MANAGE*

LIKE, SHARE, AND COMMENTS PLEASE 🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)

🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣
*_________________________________________________*
Mom ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta yayin da ta riƙe Safeera ƙamm jikinta.

"Wallahi Allah masani, hanya yarinyar nan ba ta da aljanu kuwa?". Aliyu ya faÉ—a.

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Gaskiya bana tunanin tana da aljanu saboda a wannan ƙasar babu aljanu balle maye, kuma ba ta taɓa zuwa Nigeria ba balle na ce a chan ta ɗebo aljanu".

Kallon baka da hankali Aliyu ya bishi da shi sannan ya ce. "Okay wato a iya Nigeria ne kaÉ—ai ake samun aljanu ko?, gaskiya Daddy ya kamata ka koma islamiyya ko ka dinga shiga YouTube ko chrome kana koyan abubuwan da ya daganci addinin musulunci, don naga kamar har yanzu da sauran ka".

Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Na je islamiyya mana kuma har ma nayi sauka sai dai ba'a ƙasar Nigeria na ta so ba a wannan ƙasar America na ta so".

Kallonsu gaba É—aya Mom ta yi ta ce. "Yanzu ba irin wannan magana ya kamata kuyi ba yanzu, ya kamata a ce ku san abin yi domin ta farfaÉ—o, tun É—azu nake jijjigata har yanzu ba ta numfashi. Dan Allah ku taimaka bana son na rasa Æ´ata É—aya tilo".

Kallonta Aliyu ya yi cikin tausayawa ya ce. "Na fahimci yadda ki ke ji Mom, yanzu mafita ɗaya muke da shi, dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin gargajiya. Idan muka ce zamu yi a nan sanadin hakan ƴan sanda za su iya kama mu, domin za su ɗauka cutar da ita zamu yi hakan na iya sawa su kai mu magarƙama ma. Yanzu mafita ɗaya ce shi ne muje Nigeria domin wannan maganin gargajiya ne kawai zai yi aiki.

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "maganin gargajiya kuma?, gaskiya ba za'a bawa ƴata irin wannan ƙazaman maganin ba, saboda ni duk ban yarda da ire-iren waɗan nan magungunan ba".

Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Ko ka yarda ko karka yarda dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin, in ba aka ba za ku rasa ta".

Jin an ambato batun za'a rasa ta, ya sanya Mom ta miƙe zumbur tare da nufa part ɗin ta. Saida ta ɗau lokaci kafin ta fito daga cikin ɗakin ta. Fitowa ta yi sanye da hijabi yayin da hijabi ɗaya na hannunta. Ƙarasowa wajan ta yi tare da ɗurƙusawa ta sanya wa Safeera hijabin a jikin ta".

Miƙe wa ta yi tsaye sannan ta ce. "Yanzu me ya rage, maza ku shirya mu tafi".

Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Ai kuma bamu haÉ—a kayayyakin da zamu tafi Nigeria da su ba".

Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Kada ka damu da wannan zan saka Æ´an aiki na su aiko mana su".

"Amma ka san da cewa bamu da visa, kuma kuɗaɗe basua aiki a wannan ƙasar domin idan ka ce za ka basu kuɗi za su kama mutum ne, sannan kuma ta ya ya zamu je filin jirgi da ita a haka?, domin fa kwata-kwata ba ta numfashi, ba kayi tunanin cewa ƴan sanda za su yi zargin cewa ko sace ta muka yi. Yanzu dai dole ne muna iya ba da shaida takardun aure, takaddun Haihuwar Ma'aurata da masu dogara, hotunan da ke nuna kyakkyawar alaƙa da dangi da abokai". Cewar Aliyu.

Kallon Daddy Mom ta yi sannan ta ce. "Yanzu mene ne abin yi?". Ta tambayi Daddy.

Amsa Daddy ya ba ta da cewa. "Ina da aboki ɗan sanda a chan airport sannan kuma ina da wani ma wanda na san idan na roƙe shi zai bamu visa tun da gaba ɗaya muna da password. Yanzu kawai abin da zamu yi muje chan ɗin, na san da cewa idan suka ganta za su gane ta domin sun san ta sosai ko a cikin office ɗina suna zuwa su ga photon ta a ajiye kan table, so za su gane
cewar Æ´ata ce".

"Tom shi ke nen, yanzu waye zai É—auke ta?". Mom ta tambaya.

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Kada ki damu, ni zan ɗauke ta". Yana kaiwa nan ya shiga cikin room ɗin sa. Saida ya ɗau kusan rabin hour bai fito ba, sannan daga bisani ya fito cikin ƙananun kaya wanda suka yi matuƙar karɓar jikin sa. Nufar in da suke ya yi sannan ya sa hannu tare da ɗaukar Safeera sannan ya yi hanyar waje da ita.

Ganin hakan ya sa su Daddy suka mara masa baya bayan sun ɗauki muƙulli.

Kai tsaye in da motocin gidan suke Aliyu ya nufa. Danna muƙullin motan Daddy ya yi. Nan take motar ta buɗe da kanta.

Ganin hakan ya sa Aliyu saka Safeera cikin motan yayin da gaba ɗaya su Daddy suma suka shiga cikin motar. Tada motar Aliyu ya yi. Yayin da gate man ya buɗe musi ƙofa daga bisani suka fice daga cikin gidan baki ɗaya.

Basu nufi ko ina ba sai hanyar airport.

************************
*Nigeria*

"Mene ne ka aikata haka officer?, me ya sa za ka harbi yarinyar nan bayan da cewa Gov. Musa Muhammad ya ce baya son É—ansa ya san da cewa munzo mun kori dabbobin da ke cikin daji nan".

Officer da haka faɗa wa hakan ya ce. "To baka ga yadda take tsalle kan bishiyoyi ba kamar biri, na san ba zamu iya kamata ba idan muka ce zamu kamata za ta illatar da mu ne. Bani da wani zaɓin ne shi ya sa na harbe ta a ƙafa".

"Wannan laifin ka ne, yanzu idan Sir Umar ya sani na san tamu ta ƙare".

Wayarsa ya ji tana ringing. ÆŠauko wayar ya yi daga cikin aljihun sa sannan ya É—aga kiran tare da karawa a kunnen sa ya ce. "Hello".

Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Maza-maza ka ce da sauran jami'an wajan nan su bar wajan, domin kuwa Sir Umar ya nufo hanyar wajan yanzu".

Zari ido jami'in ya yi tare da katse wayar sannan ya kalli sauran jami'an ya ce. "An kira yanzu an ce mu bar nan domin sir Umar yana tawo wa nan".

Da sauri suka matsar da Amrah wanda ke yashe kafarta sai fidda jini yake gefe. Sannan cikin ƙware wa suka fara shiga cikin motocin. Tare da tada mota suka bar harabar wajan.

Bai ɗauki Umar lokaci ba ya ƙaraso wajan. Guri ya samu a cikin dajin sannan ya yi parking.

Fitowa ya yi ciki cikin izza. Sannan ya rufe ƙofar motan. Dafe zuciyarsa ya yi ciki ranshi ya ce. "ban san dalilin da ya sa zuciyata take ta buga wa da ƙarfi-ƙarfi ba, amma yanzu tun da na zo , na san hankali na zai kwanta". Ya faɗa tare da fara tafiya.

Sai da ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya isa wajan kogin dake cikin dajin. Tsayawa ya yi jin yadda dajin ya É—auki shiru. Mamaki ne ya kama shi jin babu ko da kururwan wani dabba a cikin dajin sai dai tsuntsaye wanda suke ta kai kawo a sama.

Ƙatasawa in da kogin yake ya yi. Take idanuwansa ya sauka a kan dutsen da ke kusa da kogin. Daff da dutsen ya je ganin kamar abi rubuce a jiki.

Durƙusawa ya yi tare da shafa sunan dake jikin dutsen ya yi. Murmushi ya yi sannan ya ce. "Kenen sunanta Amrah, nice name".

Miƙe wa ya yi tsaye sannan ya bar wajan.

Tafiya ya soma yi yayin da ya fara arangama da dabbobin da ke yashe a ƙasa.

Mamaki ne ya kama shi ganin dabbobin da ke daji yashe a ƙasa cikin jini.

Daga nesa ya hangi Amrah dake kwance kusa da jikin bishiya. Zaro idanuwa ya yi waje yayin da ya tafi da gudu tare isa in da take.

Yana zuwa ya durƙusawa tare da aza kanta a kan cinyarsa. Tattaɓa fuskar ta ya soma yi. "Amrah me ya sa me ki?, wane ne ya yi miki haka?". Ɗaukar ta ya yi chakk tare da nufar in da motar shi yake da ita.

Saka ta ya yi cikin mota sannan shima ya shiga tare da tuƙa motan sannan ya bar harabar wajan.
Kai tsaye asibiti ya nufa da Amrah.

****************
Ɓangaren su Zahra kuwa suna isa Kano basu nufi ko ina ba sai asibiti suka nufa. Nan take nurse's suka saka ta a gadon marasa lafiya tare da shigar da ita cikin ɗaki. Nan take suka fara mata aiki ta yadda numfashinta zai dawo. Saka mata oxygen suka yi tare da bata allura.

Cikin ƙanƙanin lokaci numfashinta ya dawo.
Allurar bacci suka bata tasha ta yi bacci.

Fita likitocin suka yi suka bar Zahra kaÉ—ai a É—akin.
Miƙe wa DPO ya yi sannan ya dubi ɗaya daga cikin likitocin ya ce. "Me yake faruwa ne?, ya jikin nata?".
Chapter 19 · 0% Book details