Sashe 58
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faÉ—a amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika É—auki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba".
Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali".
BuÉ—e idon ta guda É—aya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buÉ—e idonta gaba É—aya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?".
Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass É—in motan tare da tofar da poison din bakinta.
Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haÉ—iye poison din ba. "Wai dama ashe ba haÉ—iye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haÉ—iye?".
Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haÉ—iye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faÉ—a maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba".
girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haÉ—iye guban?".
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, É—azun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki".
"Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving.
Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min".
Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba É—aya zan haÉ—a na kawo miki".
******************
Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah ka kaini gida Please".
Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu".
Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?".
Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na Æ´an uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da Æ´an uwanki, za su samu dubbannin kuÉ—aÉ—en da ba za su misaltu ba".
"What!". Safira ta faÉ—a cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane Æ´an uwa ka ke magana a kai?".
Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba".
Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?".
Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana É—aya daga cikin richest women in the world, ita É—in Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na".
"Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faÉ—a min waÉ—an nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba".
*************
"Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta".
Cewar warder.
Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe.
*******
Sooraj kuwa chan ya hango mai saida ruwa. Parking ya yi tare da sauka sannan ya je ya siyo ruwa guda É—aya. Saida ya É—au lokaci Sosai Kana ya dawo cikin motan. Zuwan shi keda wuya ya ga bata cikin motan.
Mamaki ne ya kama Sooraj . "Lallai ma yarinyar nan, yanzu kuma ina ta shiga". Waige-waige ya soma yi, chan idanuwansa ya sauka a kanta. Tsaye take da wasu samari guda uku suna sanye da baƙaken suit. Yayin da Zahra ke surfa musu bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Dafa kansa Sooraj ya yi. "Wayyo Allah, wannan wace iriyar masifa ce, wai ko ina taje saita nuna halin ta".
Ya faɗa yana mai ƙarasa wa inda take. Zuwa wajan keda wuya Zahra ta ganshi. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce . "Yauwa masha Allah kazo a dai-dai, zo ka jini da wata masifa, ina zaman-zama na waɗan nan kajin dake sanye cikin wannan abun da suka kira suit suka zo inda nake, na tambaye su me suke so suka ce wai ai zuwa suka yi su sace ni, shi ne na ce idan za su iya su sace ni".
Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kema in banda abunki ai wasa suke miki".
"A'a wallahi waɗan nan ba wasa suke ba, kana ganinsu yadda ka san wasu ƙasurguman masheƙa, ni kuma dai-dai nake da su". Cewar Zahra wacce ta faɗa hannunta riƙe a ƙugu tana karkaɗa su tare da karka ƙafarta yadda kasan wacce zata yi dambe.
"Shi ke nen to mu tafi ko". Sooraj ya faÉ—a yana mai kama hannun Zahra.
Nan take maza ukun da ke sanye cikin suit suka kalli juna, nan suka fito da wani abu kamar perfume tare da fesa musu.
Duk abinda ke faruwa a gaban idanuwan Mk.
Nan take jiri ya ɗebe su suka faɗi a ƙasa.
Kwashe su mutanen suka yi tare da saka su a mota.
Ganin hakan ya sa jama'a suka saki ihuu yayin da suka jifar motan kidnappers ɗin da dutsina. Da sauri kidnappers ɗin suka tada mota tare da fara ƙoƙarin barin wajan. Nan jama'a suka dinga binsu a baya har suka ɓace wa ganinsu.
Da sauri Mk ya nufi inda motar Sooraj yake domin ganin idan akwai inhaler a motar domin ya san perfume da aka fesa musu zai iya affecting É—in shi, domin kuwa ya san Sooraj yana da asma. Nan ya fara dube-dube a motar. Cikin sa'a kuwa ya ga inhaler É—in saman kujera. Da sauri ya É—auka sannan ya nufi motarsa da sauri tare da tada wa ya bi bayansu Zahra.
Gudu suke falfalawa kamar za su tashi sama.
BuÉ—e idanuwanta Zahra ta yi ta gansu cikin mota. Ihuuu ta buga yayin da ta fara dukan wanda ke bayan seat É—in kusa da Sooraj.
Nan take ɗaya a cikin su ya kwaɗe ta da mari. Jin marin Zahra ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta. Nan take ta fusa ta yayin da ta kama kunnen wanda ke kusa da ita tare da fara gantsara masa cizo.
Ihuuu saurayin ya buga yayin da ya fara ƙoƙarin ƙwace kanshi amma hakan ya cutura. Kuma hakan bai sa sun dakatar da tuƙin ba.
Nan saurayin ya taki sa'a ta sake shi. Ganin ta saki kunnensa ya sa shi dafa kunnensa wanda ya yi jajir. Gurnani ya fara yi. Nan ya shaƙe mata wuya tare da ƙoƙarin yi mata allura kan jijiyar wuyanta.
Duk abinda ke faruwa Sooraj bai sani ba, domin har izuwa wannan lokaci bai farfaÉ—o ba.
Babu zato suka fara jiyo Sooraj yana nishi sama-sama alamun asma É—insa ya tashi.
Ganin hakan ya sa Zahra ta sa dukannin ƙarfinta ta ture wannan saurayin.
Hankali tashe ta É—aga Sooraj tare da girgiza shi. "Yahya Sooraj me ya sa me ka?, dan Allah kada ka mutu ka barni".
Cikin fitar hayyaci Sooraj ya dube ta ya ce. "Asma É—ina ya tashi kuma inhaler É—ina yana cikin motata".
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi nan take tausayin Sooraj ya kama ta. Kallon kidnappers É—in ta yi ta ce . "Dan Allah ku mayar da mu, idan ba haka ba zai mutu, ko baku ga yana cikin mawuyacin hali ba ne".
Ko kallon Zahra basu yi ba saima ƙara wa motar gudu da suka yi.
Rungume Sooraj Zahra ta yi tare da É—aukar ruwan da ya siyo ta bashi yasha.