← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 59

Sashe 22

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ki je ki ce mata ta zo ina da buƙatar ganinta". Cewar Umar.

"Shi ke nen". Nurse É—in ta faÉ—a tare da fice wa daga cikin É—akin.

*******
Ɓangaren su Aliyu kuwa, hawanni ƙalilan ya yi musu suka iso Nigeria. Yayin da suka sauka a airport. Fito wa suka yi tare da neman taxi suka hau kai tsaye suka nufi hanyar asibiti.

******
Mitin ƙalilan nurse Nadiya ta isa ɗakin da su Umar suke. Da sallama ta shiga ɗakin Umar ya amsa. Dubansa ta yi ta ce. "Naji an ce kana kira na lafiya dai ko?".

Amsa Umar ya bata da cewa. "Lafiya ƙalau, ina neman taimakon ki ne, yanzu zanje gida ne na ɗauki abun da zai sa ta sauko ƙasa. Ina so ne ki jire min ita dan Allah kinji?, bana son ta fita ko ina please".

Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Aiki na ne yin hakan, don aka kada ka samu damuwa za ka iya tafiya ni zan zauna na kular maka da ita".

Godiya Umar ya yi mata sannan ya fice daga cikin É—akin.

Zama nurse Nadiya ta yi tana mai maida kallonta sama sannan ta girgiza kai ta ce. "Allah mai iko, ko ta ya ya na aka yi ta ɗane kan fanka oho. Kina jina ƴar lele, maza sauko ƙasa kinji kyakyawa, zan siya miki alewa".

Ganin Amrah ba ta kula ta ba saima ƙara zama da ta yi kan fankan. Furzar da iska nurse Nadiya ta yi sanann ta ce. "Shi ke nen tun da ba za ki sauko ba". Ta faɗa tare da ɗaukar lemon ɓawo da ke cikin plate ta fara ƙoƙarin kai bakin ta.

Hango lemon ɓawo da Amrah ta yi ya sa ta dira ƙasa tare da wafce lemon, sannan ta fara haɗa wa da bawon jikin sa tana sha.

Zaro idanuwa Nurse Nadiya ta yi ganin irin launin idanuwanta. Cikin ranta ta ce. "Wannan green eyes ne da ita, sakk kalar idanun ɗaya daga cikin yaran Mrs Laila. Allah sarki". Ta faɗa yayin da hawaye suka fara bin kan ƙuncin ta.

*************
Bayan isar Yarima Junaid fada ya shiga cikin part ɗin sa ba tare da ya kula kowa ba. Shiga wani ɓangare ya yi a gidan sannan ta duba aljihun shi domin ya ɗauki maƙulli. Zaro idanuwa ya yi waje gani cewar babu muƙullin ɗakin sa a aljihun shi.

"Ta ya ya hakan za ta faru?, ina maƙullin ya shiga kuma?, na shiga uku!, muddin banga maƙullin nan ba sai Yahya ya hukunta ni, yanzu me zan yi kenen?".

Nan take ya tuna da cewar ɗazu ya riƙe Zahra. "Kodai ita ce ta ɗauka?". Ya tambayi kanshi.

Da sauri ya fita daga cikin part É—in sa. Tare da fita hanyar waje. nan take ya ci karo da mai martaba.

Sunkuyar da kansa Junaid ya yi sannan ya ce. "Allah ya ƙara maka nisan kwana ranka shi daɗe".

Dubansa mai martaba sarki ya yi sannan ya ce. "Junaid me ya sa ka fita daga cikin masarautar nan bayan na hana ka fita?".

Nan take cikin Junaid ya É—uri ruwa.

***************
Ɓangaren su Safeera kuwa, shigar da Safeera aka yi cikin room 8, yayin da likitoci suka rufa a kanta. Babu abin da Mom ke yi in banda addu'a yayin da take ta kai kawo a cikin reception ɗin.

Saida suka É—au lokaci sosai a kanta kafin daga bisani suka samu numfashin ta ya dawo. Nan take suka yi mata allurar bacci.

Fito wa likitocin suka yi suna sharfe zufa. Ganin sun fito ya sa su Mom suka nufi in da suke tare da tambayar ya lafiyar Safeera.

ÆŠaya daga cikin doctor's É—in ne ya dube su ya ce. "Alhamdulillah, mun samu numfashin ta ya dawo yanzu kuma ta samu bacci. Zamu saka É—aya daga cikin nurse É—in mu ta je ta duba ta.

"Shi ke nen". Daddy ya furta.

Shiga cikin room É—in da nurse Nadiya take likitan ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Nurse ina son ki je ki dinga kula da wata mara lafiya tana room 8".

Kallonsa Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Am sorry to say sir, but ba zan iya rabu wa da wannan mara lafiyar sannan na koma kan wata ba, wannan an bani amanar ta ne. Kuma nayi alƙawarin zan kula da ita, kuma yana da kyau idan mutum ya ɗau alƙawari ya yi ƙoƙarin cika wa. Ka saka wata nurse ɗin ta je ta kula da ita Please sir ". Ta faɗa cikin ƙasa da murya.

Kallonta doctor É—in ya yi sannan ya ce. "Ina mara lafiyar da ki ke kula da ita take?".

Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "gata chan a sama".

Maida kallonsa Doctor ɗin ya yi sama. Zaro idanuwa waje ya yi domin abin da ya gani ya yi matuƙar bashi mamaki. "I can't believe this, how can this be possible". Ya faɗa. Maida kallonsa ya yi kan nurse Nadiya sannan ya ce. "Ina so yanzu kiyi maza-maza kije ki duba patient ɗin ke cikin room 8 yanzu". Ya faɗa hankalin shi a matuƙar tashe.

Kallonsa nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lafiya dai Doctor, naga kamar hankalin ka a tashe".

Doctor É—in ya dube ta ya ce. "Dole hankali na ya kasance a tashe domin naga abin da ya firgita ni, kije ki duba É—akin ko mara lafiyar mu tana wajan, ni zan wuce office".

"As you wish sir". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye tsreda fice wa daga ɗakin.

Zama Doctor ɗin ya yi yana mai kallon Du'a wanda ke a kan fanka. "Abin mamaki baya ƙare wa, yanzun nan da na fito daga ɗakin ɗayar yarinyar amma kuma yanzu na zo nan, na tarar da mai kama da ita sakk. Wai ko dai na sha maye ne yau?". Ya tambayi kansa.

******
"Shi ya san abin da ya gani hankalin sa ya tashi, koma dai mene ne zan je ɗakin na gani". Cewar nurse Nadiya. Tana isa ƙofar ɗakin ta murɗa handle ɗin ƙofan.

Chan ta hango Safeera a kwance. Riƙe haɓar ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lahaula, Amrah wato har kin riga ni zuwa nan ɗin ma. Ta ina ki ka bi har ki ka riga ni zuwa?". Dube-dube ta fara yi.

"To wai ina mara lafiyar take ne?, wato dai wannan likitan so yake kawai ya bani wahala shi ya sa ya ce min wai akwai mara lafiya a nan". Ta faÉ—a tana mai maida kallonta kan safeera wacce ke kwance kan gado idanuwanta a lumshe.

Mamaki ne ya kama nurse Nadiya ganin cewar tufafin da ke jikin Safeera ba irin shi ne a jikin Amrah ba. "Ta ya ya Amrah ta iya sauya kaya cikin ƙanƙanin lokaci aka?". Nurse Nadiya ta tambayi kanta.

Furzar da iska ta yi sannan ta ce. "Mybe ni ce
ban duba ba sosai . Amrah ina zuwa bara naje na faÉ—a wa Doctor É—in cewa banga mara lafiyar da ya faÉ—a ba". Ta faÉ—a tare da fice wa daga cikin É—akin.

Nufar ɗakin da Amrah take ta yi. Tana isa ƙofar ɗakin ta buɗe tare da shiga cik. Yayin da idanuwanta suka sauka a kan Amrah. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa!, yayin da gabanta ya shiga dukan uku-uku. Babu zato ta ji kanta ya yi mugun sara mata. baki na rawa ta ce.

" Amrah!, kenen ba Amrah na gani a wan can É—akin ba?, to in dai da gaske ba Amrah bace a wannan É—akin ita kuma ta cikin É—akin wace ce?".

💃💃💃🌹🌹💃💃💃

*TASHIN KAI, NURSE NADIYA FA TA SHIGA RUÆŠANI KOMAI ZAI FARU IDAN TA GANO CEWAR SU BIYU NE A ASIBITIN, SANNAN KUMA YARAN LAILAH ABDULLAHI NE?. MUJE DAI ZUWA*

*WAYYO LOW BATTERY 🔅 🔋, MUNA FAMA DA RASHIN WUTA BANI DA CHARJI🥺, JIYA MA NASO NAYI MUKU AMMA RASHIN WUTA YA HANA. KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE PLEASE 🙏*.

KARKU MANTA DA SHARING, COMMENTS, AND LIKES FISABILULLAH 🙏🙏🙏🙏.

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣
*_________________________________________________*
Nurse Nadiya ta faÉ—a cikin ruÉ—u da gigicewa. Kuma maida kallonta ta yi kan Amra sannan ta ce. "Amrah green eyes ne da ita, ita kuma wan can fa?, to in har wan can ta É—akin blue eyes ce da ita hakan yana nufin Æ´aÆ´an Mrs Laila ne".

Ta faɗa tana kuma koma wa ɗakin da ta ga Safeera. Tana ƙarasawa ƙofar ɗakin ta shiga ciki. Da mamakin ta kuwa sai ta ga babu kowa a ɗakin.

Hakan ba ƙaramin mamaki da tsoro ya sanya ta ba. "Kodai na fara gane-gane ne?, ba'a nan ɗakin ba ɗa zu naga wata mai kama da Amrah?, where is she?". Ta tambayi kanta.

Tuna wa da cewar Umar ya ce kada ta bar Amrah ita kaÉ—ai ya sanya ta saurin barin wajan tare da nufar in da É—akin da Amrah take.

Safeera kuwa bata je ko ina ba sai bandaƙi domin ɗaura alwala. Bayan ta gama ta fito daga cikin toilet ɗin yayin da ta duba ko ina amma babu hijab sai iya ɗingilallen mayafin ta.

Zama ta yi a bakin gado sannan ta duba arabar wajan. Sai a lokacin ta lura cewar ba'a gida take ba.

Zumbur ta miƙe tsaye tana mai waige-waige. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin cewa tabbas nan ba ɗakin ta ba ne. Kwalla kiran sunan Mom ta fara yi cikin tsoro da fargaba. Su Mom da ke reception jin muryar Safeera hakan ya sa su yin saurin nufar ɗakin da take.

Da sauri suka shiga É—akin suka tadda ta tsaye gaba É—aya duk ta bi ta rikice.

Kallonta Mom ta yi ta ce. "Ƴata Safeera kin farka?, Alhamdulillah Allah na gode maka".
Chapter 22 · 0% Book details