← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 59

Sashe 5

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rass! Gaban Mrs Laila ya faÉ—i. Cike da tsoro ta kalle shi ta ce, "ni nurse ce kuma Doctor ne ya umarce ni dana zubar da waÉ—an nan dattin a waje. Saboda wari yana affecting É—in patient É—in mu na asibiti kuma yana iya tada musu da rashin lafiyar su".

Jinjina kai police É—in ya yi sannan ya saka a É—auko masa portable scanner domin ayi scanning É—in troley dake hannunta.

Ganin hakan ya sa gaban Mrs Laila ya tsananta faɗuwa. Karɓar scanner police ɗin ya yi wajan ɗaya daga cikin jami'an sannan ya fara scanning troley ɗin. Rintse idanuwanta Mrs Laila ta yi yayin da take karanto duk wani addu'oin da ya zo cikin zuciyarta.

Saida ya zo daff da inda jaririyar take sannan ya ɗauke scanner ɗin tare da bata damar fita. Hamdala Mrs Laila ta yi sannan ta fara jan troley ɗin harta je daff da bakin ƙofa.

Daga sama ta ji muryar police ɗin ya ce. "Dakata". Chak Mrs Laila ta tsaya Tare Dmda jiran furucin da zai ƙara fitowa daga bakinsa.

Zuwa police ɗin ya yi daff da ita sannan ya ce. "Ina son kafin ki fita ki cire facemark ɗin fuskarki na ganki". Ta ke zuciyar Mrs Laila ya buga da mugun ƙarfi. Cikin zuciyarta kuwa ta ce. "Na shiga uku yanzu na san shi kenan asirina zai tonu. Ya zama dole na ƙara yi masa wata ƙaryar domin fita daga wajan nan".

Juyawa ta yi tana mai fuskantar sa sannan ta ce. "Kayi haƙuri ni ɗin matar aure ce miji na ne ya bani umarnin yin hakan, kuma ya ce kada na kuskure na buɗe fuskana saboda baya son haga matarsa. Kuma kaga dole na bi umarnin sa saboda igiya uku ce a kaina ba zan so na rasa su ba kuma aljannata tana ƙarƙashin kafar mijina dole nayi masa biyayya. Ko kaima ba zaka so matar ka ta bijire maka bah". Ta faɗa tana mai kauda kai gefe.

"Shi kenen na fahimce ki. Tabbas ke É—in mata ce ta gari har ki iya jure zafin rufe fuskarki saboda kiyi wa mijinki biyayya toh tabbas ba bu makawa ke É—in ta gari ce, ba bu komai za ki iya tafiya".

Godiya Mrs Laila ta yi masa daga bisani ta fice daga cikin asibitin.

Bayan ficewar Mrs Laila daga cikin room 8 nurse Nadiya ta ɗauki ɗayar jaririyar sannan ta ɓoye ta a ƙarƙashin gado. Maida kallonta kan CCTV camera dake cikin ɗakin ta yi sannan ta ɗauki ƙarfe tare da fasa cameran. Yayin da ta samu kanta ta dinga bugawa a jikin gini har saida taga yafara jini.

Nan ta ke ta faɗi ƙasa sannan ta ƙwalla wani irin razananniyar ƙara!. Nan ta ke ƴan sanda da warders suka fara nufo hanyar ɗakin yayin da likitoci suka nufo wajan. Buɗe ƙofar suka yi yayin da suka tarar da nurse Nadiya a kwance rai a hannun Allah.

ÆŠaya daga cikin jami'an ne ya isa gare ta tare da tambayar ta me ya faru?. Cikin ciwo ta ce.
"Ta gudu mai laifin ta gudu ita ce ta ji min rauni saboda kada na tona mata asiri".

Shitttttt! ÆŠaya daga cikin jami'an ya faÉ—a yayin da ya É—auki field telephone na Æ´an sanda tare da sanar da sauran jami'ai. Nan ta ke labari ya karaÉ—e cikin asibitin cewar Mrs Laila ta gudu.

Ta ke Æ´an sanda da warders suka shiga zagaye cikin asibitin suna neman Mrs Laila.
Police É—in da ya bar Mrs Laila ta fita ne ya yi nazari yayin da yaga cewar tabbas shi É—in babban maloho ne har bai iya gane cewar ita ta fita bah. Nan ta ke suka fita tare da fito da police dog's da makamai na tsaro.

Nan ta ke Æ´an jarida suka fara É—aukar rahoto na labarai cewar Mrs Laila ta gudu daga asibiti.

Fita jami'an suka yi daga cikin asibiti sannan suka saki karnuƙa suka fara bin ƙarnin jinin dake jikin Mrs Laila.

TOH FANS KOYA ZATA KASANCE DA MRS LAILA DA KUMA JAMI'AI? SHIN ZA SUYI NASARAN KAMA TA KO KUWA TA TAFI KENEN? SHIN NURSE NADIYA MAI AMANA CE KOH KUWA MAI BUTULCI CE? SHIN YARANTA ZA SU TASO SU GURARE DABAN DABAN SU SAN JUNA DAGA BAYA? WAI WACE CE MA MRS LAILA? DOMIN JIN AMSOSHIN TAMBAYOYINKU KU CI-GABA DA BIBIYA DON JIN YACCE ZATA KAYA.

*KADA KU MANTA INA SON NAGA RUWAN COMMENTS. YAWAN COMMENTS YAWAN POST😍😘💕💕😍. COMMENTS ƊIN KU SHI NE ZAI NUNA KUNA MARABA DA WANNAN LITTAFIN SANNAN KUNA JIN DAƊIN SA*.

COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏 🙏
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)

[7/24, 11:15] Ayeesher M.B🥰🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣▶️6️⃣
*__________________________________________*
"Sir Mrs Lailah Abdullahi fah ta gudu daga asibiti amma yanzu mun bazama nemanta".

"What! Kamar ya ta gudu? ina ku ke da harta samu damar fita daga cikin wannan asibitin? wannan wane irin shashanci ne?". Cewar DPO

"Kayi haƙuri sir ɓadda kama ta yi hakan ya sa bamu gane ta ba. Amma yanzu zamu je mu binciki ccctv camera domin ganin komai". Cewar police officer ɗin

"Shi kenen ba bu damuwa. Amma yanzu me zamu ce wa mutanen gari da kotu kenen? wai waya ce muku ma ku fito da ita daga magarƙama?. Yanzu dai shi kenen best solution shi ne kuje gidan radio da gidajen jarida ku buga news paper da photon ta ku saka wanted duk wanda ya ganta yana da kyauta mai tsoka. Kuma baya sannan ku sanar da masu motoci da adaidaita cewar yau ba bu aiki kada wanda ya fito hatta masu motar tasha karsu fito domin banason ta fita daga cikin garin nan kajini Koh?".

"Shi kenen sir yadda kace haka za'a yi". Yana kaiwa nan ya kashe wayar yayin da suka nufi cikin inda ccctv cameran yake.

Miƙarda Nurse Nadiya ɗaya daga cikin police ɗin ta yi. Yayin da Doctor ya saka mata bandage tare da bata magani rage zafi tasha.

"Wai mene ne ya faru?". ÆŠaya daga cikin warders É—in ta tambayi Nurse Nadiya.

Share hawayen ta Nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na shigo zan bata magani sai ta ce min na taimaka mata na fitar da ita ni kuma naƙi amince mata harna yi iƙirarin cewar zan tona mata asiri, kawai sai ji nayi ta buga min ƙarfe a kaina sannan ta cire min kayan Nurse's ta saka. Bayan ta buga min ban sake sanin inda kaina yake bah sai yanzu".

Ajiyan zuciya police É—in suka sauke sannan suka ce. "Amma shin ina yaran da ta haifa suke?".

Nan ta ke zufa ya fara ƙeto ma nurse Nadiya ta kowane sashi na jikinta.

Cikin daƙewa ta ce. "Iya jaririya ɗaya na gani a wajan ta kuma ta fita da ita".

"Shi kenen Kada ki damu zaki bamu number ki da address É—in ki domin mu ci-gaba da investigation hakan wannan lamarin because this is an criminal offense ba zai yu a rufe bah. Kuma sannan zamu bincika gaba ki É—aya ccctv camera dake cikin asibitin nan".

Yana kaiwa nan ya yi musu alamun da su fita. Fice wa suka yi gaba ki É—aya yayin da suka bar iya nurse Nadiya da doctor a ciki.

Gaban nurse Nadiya ne ya tsananta faÉ—uwa jin cewar za'a je a duba ccctv camera.

Ta ke kukan jaririyar dake ƙasan gado ya karade ɗakin. Rass! gabanta ya faɗi.

____ Yauwa Doctor ina ccctv csmersn cikin room 8 naga kowane É—aki ccctv camera yana yi amma banda na room 8. Muna so ne mu É—au recording duk abin da ya faru a É—akin". Cewar É—aya daga cikin Æ´an sandan.

"Kuyi haƙuri na manta ban faɗa muku bah ccctv cameran ɗakin nan ya daɗe da de nayi kuma mun kira mai fixing ɗinshi ya ce zai zo ya gyara".
Cewar likitan.

Miƙe wa ɗan sandan ya yi a fusa ce sannan ya ce. "Wannan wane irin shashanci ne? ya za'a ce ccctv camera na room 8 bayayi bayan kuma duk sauran suna yi? kin san mahimmanci cctv camera kuwa?".

Cctv hana sanyawa a cikin ɗakunan majiyyata, da sassan kulawa masu mahimmanci. Wannan na iya taimakawa wajen lura da yanayin marasa lafiya da faɗakar da ma'aikatan kiwon lafiya idan akwai gaggawa. Cctv kuma na iya taimakawa wajen lura da hulɗar marasa lafiya tare da masu ba da lafiya don saka idanu hakan ingancin kulawa da bin ka'idoji. Amma shi ne zaku je wannan room 8 ɗin ba bu, a shi ma ya kamata a bar cctv domin babban makashiya ce a ciki dole a dinga ganin take-taken ta. Yanzu da a ce cctv na ɗakin nan nayi da binciken sai ya fi mana sauƙi. Rubbish kawai". Police ɗin ya faɗa tare da ficewa daga wajan. Ganin hakan ya sa sauran jami'an suka mara masa baya.

Haka jami'an suka bazu cokin gari wajan neman mrs Laila Abdullahi. Yayin da bangare guda kuma Jami'ai waɗan da ke tare da police dog's wajan bin ƙarnin jinin Mrs Laila sun gaza samo ta. Ba yacce suka iya haka suka koma police station.

Ɓangare guda kuma ƴan sandan sun buga photon Mrs Laila a jarida wanda haka saka wanted a jiki. Sannan suka fara kafawa a titinuwa. Yayin da gefe guda kuma suka je gidan radio tare da sanar da jama'ar garin. Nan da nan garin ya karaɗe da maganar Mrs Laila Abdullahi babbar yar ta adda mai safaran miyagun ƙwayoyi wanda gaba ki ɗaya garin ya amsa da hakan.
Chapter 5 · 0% Book details