← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 59

Sashe 31

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take jikin kowanensu ya yi sanyi.
Ajiyan zuciya Grandpa ya sauke!, kana ya ce. "Babu wacce muka kora sai Laila, kuma ita ma ɗin na kore ta saboda zubar min da mutunci da ta yi a idanun duniya kana kuma ta lalata sunan ahalin mu, ita ce dalilin kasance wa ta kan wheel chair yanzu. Ta chanza sunan ahalin mu daga masu mutunci izuwa marasa mutunci. Ita ce kawai nake tunanin na kore ta na damka ta a hannun ƴan sanda. Sannan har yau har gobe ba zan manta irin cin mutunci da jama'a suka yi mana ba duk ta dalilin ta. Kuma bayan nan ma ta dalilin ta ne jikana yanzu haka yake da cutar mantau. Don haka ba zan taɓa yafe mata ba, koda zan yafe wa kowa a duniyar nan to banda Lailah".

Share hawayen da ke shirin zubo mata Grandma ta yi kana ta ce. "Kuma ita É—in a halin yanzu ba ta raye ta riga da ta je gidanta na gaskiya, kuma ina fatan tana cikin rahamar Ubangiji".

Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "Tabbas kun aikata babban kuskure a rayuwar ku, ya zama dole ku nemi gafarar wannan ƴar taku idan kuwa ba haka ba, rayuwar ku za ta taɓe. Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Baku gani ba sannan baku sheda ba ku ka yanke wannan mummunar hukuncin a kanta, idan ma baku samu kun nemi gafarta ba to ku nemi gafarar ƴaƴan ta domin kada fushin Ubangiji ya dauwama a kanku. Ni na gama magana ta za ku iya tafiya".

Ya ƙarashe maganar yana mai kwanciya kan katifar sa.

Kallonsa Mom ta yi ta ce. "Malam batun maganar ƴata fa?". Jin shiru babu amsa ya sa gaba ɗayansu miƙe wa sannan suka fice daga ɗakin Malamin.

Kai tsaye wajan motocin su suka nufa sannan suka shiga ciki yayin da drivers da ke tsaye suka shiga cikin motan tare da tada motocin sannan suka bar harabar wajan. Kai tsaye suka nufo hanyar Dutse. Tun da suka fara tafiya kowanensu ke ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa yayin da gaba ɗayansu suka kasa samun sukuni.

***********************
Zumbur Safeera ta miƙe tsaye tqreda nuna Aliyu da yatsarta sannan ta fara kokarin magana. Nan wata zuciyar ta ce da ita ta rabi da shi kawai. Waje ta samu ta zauna sannan ta kawar da kai gefe ta ce. "Ina neman wata alfarma".

Murmushi Aliyu ya yi kana ya ce. "To fa, alfarma a waje na kuma, me ya sa sai a waje na?".

Amsa Safeera ta bashi da cewa. "Saboda na ga kafi cancanta na nema a wajan ka ne. Ina da buƙatar sabulu da man shafa wa sannan da kayan sawa. Duka kaya na suna chan America. Ina da wasu ƴan kuɗaɗe a acc ɗina, shi ne na ce idan babu damuwa ka taimaka ka kaini in da ake shopping domin na yi siyayya".

Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi kana ya ce. "Wato ma ke É—in nan kin cika Æ´ar rainin hankali, yanzu-yanzun nan ki ka gama yi min rashin kunya, and you are expectimg me to take you to shoppin mall, hope dai kina lafiya ba wai giyan wake ki ka sha ba".

Turnuƙe fuska Safeera ta yi ta ce. "Tun da na zo fa banyi wanka ba, am irritating myself, I feel so disgusted I can't take it anymore shi ya sa na nemi alfarma, amma idan ka ga ba za ka kaini ba it fine, i know what to do".

Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi kana ya ce. "Shi ke nen je ki saka hijabi na kaiki".

Murmushin jin daÉ—i Safeera ta yi kana ta ce. "Amma ba zan iya zuwa haka ba ne, na ga dai akwai sutura a jiki na ga kuma veil na yafa".

Binta Aliyu ya yi da kallo tare da kallon matsatsun kayan da ke jikin ta. Kawar da kai ya yi gefe sannan ya ce. "In dai da wannan kayan za ki bini to babu in da zan je wallahi kinji na faÉ—a miki".

Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen bari na ɗauko hijabi. Ta faɗa tareda shiga cikin ɗakin su Zuwaira ta ɗauko maroon hijab ta sanya. Sosai hijabin ya yi mata kyau.

Fitowa ta yi kana ta ce. "Muje ko".

Kallonta Aliyu ya yi cikin zuciyarsa ya furta kalmar. "Masha Allah Alhamdulillah, tabbas su Mom sun zaɓa min mace kyakyawa, gaskiya nayi dace".

Taɓe baki ya yi a fili ya ce. "Ko kyau, abu kamar a hura ta faɗi".

Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Koma dai mene ne kai ka sani".

Fita suka yi a tare da shiga cikin mota a tare. Tada mota Aliyu ya yi kana suka fice daga cikin gidan yayin da ma'aikatan gidan suka bisu da kallo.

Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin su isa ga shopping mall É—in.

Ɓangaren su Amrah kuwa sosai su khairiya ke yi wa Amrah siyayya, kama daga abayoyi atamfa, Arabian gowns, hijabbai da mayafai tare da set na kayan makeup da dai sauransu.

Jan hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara zagaya da ita cikin mall ɗin domin ya zaɓo mata wasu abubuwan.

Bayan shigar su Aliyu ne suka nufi ɓangare da za su samu abin da Safeera ke buƙata.

Sakin hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara dube-duben wasu abubuwan.

Safeera ganin hankalin Aliyu ya tafi wani wajan ya sa ta yi saurin barin wajan tareda nufar wani part na ciki wajan

Amrah kuwa barin in da Umar yake ta yi tare da nufa É—ayan sashin da ba ta san ko ina ba ne.

Juyawar Umar keda wuya kawai ya ga Amrah ba ta nan.

Waige-waige ya fara yi ya ga dai still bai ganta ba. Hankalin sa ba ƙaramin tashi ya yi ba domin kuwa a tunanin sa waɗan da suke bibiyar rayuwarsa sune suka sace Amrah nan take ya kira jami'ansa.

A ɓangaren Aliyu dai shima haka domin ya yi neman duniya bai ga Safeera ba.

Chan Aliyu ya hango Amrah a tsaye. Mamaki ne a ya kama shi domin duk a tunanin shi Safeera ce. "To ikon Allah wato Safeera harta chanza shiga izuwa pink abaya". Ƙarasa wa in da Amrah yake ya yi kana ya ja hannunta ya ce. "Ke safeera ina ki ka je ki ka sa nake ta neman ki?".

Juyo wa Amrah ta yi. Nan take idanuwan kowannensu ya sauka a juna.

Take gaban Aliyu ya yi mummunar faÉ—uwa!, sauri sakin hannunta ya yi tare da ja da baya. Baki na rawa ya ce. "Safeera garin ya ya idanuwanki suka chanxa kala?".

Ɓangaren Umar kuwa ganin Safeera ya yi tana ta tsince abubuwan da take so. Murmushi ya yi ba tare da sanin ba Amrah ba ce ba ya ja hannun ta ya ce. "Ke Amrah kin fiye yqwo maza mu tafi.

Mamaki ne karara ya bayyana kan fuskar Safeera. Saurin wafce hannunta Safeera ta yi ta ce. "Hey wane ne kai kuma?, wace ce kuma Amrah?".

Juyo wa Umar ya yi domin kuwa ya yi matuƙar mamki a karo na farko Amrah ta yi magana. Juyawar sa keda wuya idanuwansa ya sauka a na idanuwan Safeera. Gabansa ne ya bada wani irin ƙara tare da wani irin bugu. Da sauri ya saki hannunta yayin da ya nuna ta cikin zallar mamaki ya ce. "Gari ya ya idanuwan ki suka sauya izuwa blue kuma?, dama kin iya magana ne?".

************************
"Wai Mami su wane ne waÉ—an chan matan ne?, na san a girma za ki girme su amma shi ne suke miki rashin kunya, ni fa idan da abin da nafi tsana bai wuce zagar min uwa da raini ba. Shin ke Æ´ar aiki ce a gidan nan ne suke yi miki irin wannan cin fuskar?".

Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "A'a ni É—in ba Æ´ar aiki bace ba, su É—in kishiyoyi na ne ni kuma ni ce Uwar gidan su".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce.
"Kuttmelesin chan dumadu, chabb ɗi jamm kenen dama wai kishiyoyin ki ne?, kai Mami, gaskiya kinyi sanyi da yawa, chabb na yarda da kaina. Wayyo ni Zahra, dama ni ce nake zaune da waɗan nan kishiyoyin guda biyu da tuni na saita wa kowanensu zama duk gaba ɗaya na ga ɗuwawunsu rawa yake duk da saina saita musu shi. Gaskiya Mami kinyi sanyi da yawa. Ai kuwa dole ne na gyara wa kowa zama a gidan nan kafin na bar wannan masarautar. Domin samm ba zan juri ire-iren waɗan nan abubuwan ba, me yafi wannan raini. Na ga ma kamar sun raina ki, wata a cikin su mai haƙora kamar na akuya mai gatso ɗin nan Talatu na ji kin ce ɗazu ko, ita harda wani dungure miki kai tsabagen ta raina ki".

Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "To ya zanyi Zahra?, ni sam bana san tashin hankali da hayaniya, shi ya sa kawai nake zaune da su a hakan banason rigima. Shiru- ba tsoro ba ne gudun magana ne, a lokacin da ɗana Sooraj yana nan babu wanda ya isa ya yi min abin da suke yanzu. Domin kuwa kowa tsoronsa yake a gidan nan. In dai baya nan ne suke mim waɗan nan abubuwa, idan kuma ya dawo kowa shan jinin jikinsa yake. Ni kuma ban taɓa buɗar baki na faɗa wa mai martaba ko ɗana Sooraj ba. Saboda bana son tashin hankali".

Girgiza kai Zahra ta yi kana ta ce. "Tabbas ni ce zan kawo sauyi cikin wannan masarautar saina tabbatar da na saita musu zama kafin na bar gidan nan, ba zan iya zuba ido na ga ire-iren waÉ—an nan abubuwan na faruwa ba, ya zama dole na koya musu hankali".
Chapter 31 · 0% Book details