← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KaÉ—a kai Zahra ta yi ta ce. "Aba dai me ya sa za ki je ki É—auko bayan ina zaune a nan wajan?, kada ki damu kiyi zaman ki kawai a nan zan je na É—auko".

"Shi ke nen". Jakadiya ta furta.

Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da nufae hanyar waje. Saida ta je daff da za ta fita ta ji muryar Mami na faɗin. "Zahra dakata".

Tsayawa chakk Zahra ta yi tare da maida kallonta kan Mami ta ce. "Mene ne Mami?".

Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Babu komai, ina so in faÉ—a miki cewa idan ki ka je chan duk abin da za su yi miki kada ki tanka su dan Allah, bana son a kuma samun wani matsalar please and please".

Girgiza kai zahra ta yi kana ta ce. "In sha Allahu ba zan kula su ba".

Ta faÉ—a tana mai fice wa daga É—akin. Kai tsaye in da ta ga su Samira sun nufa É—azu ta nufa domin É—auko nail cutter É—in Mami.

Saida ta zo dai-dai ƙofar part ɗin su kana ta buɗe handle ɗin ƙofan ba ta yi wata-wata ba ta ƙusa kai ciki.

Take ta shaƙi hayakin da ya gauraye ilharin parlourn part ɗin su Samira. Tari Zahra ta fara yi tare da toshe hancin ta. Domin kuwa warin shisha ne kawai ke tashi a ɗakin.

Waige-waige Zahra ta fara yi. Nan take idanuwanta suka sauka a kansu Samira wanda ke faman zuƙan shisha. Dubanta suka yi tare da cewa. "Ya haka yi ne?, me kuma ya kawo ki ɗakin mu?".

Ƙasa da kai Zahra ta yi cikin jin takaicin abin da suke aikata wa.

Ɗaga kanta Zahra ta yi ta dube su ta ce. "Tirr da wannan rayuwa irin taku. Gaba ki ɗaya kun taso babu tsoron Allah a zuƙatan ku, wannan wace iriyar rayuwa ce?, kuna mata kuna shan hayaƙi wanda babu abin da take haifar wa sai cutarwa, Allah ya shirye ku. Ni duk ba wannan ba na zo ne duba nail cutter ɗin Mami yana ina?".

Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi. Yayin da Yusrah ta miƙe tare da zuwa daff da in da Zahra take sannan ta busa mata hayaƙin bakin ta.

Kawar da kanta Zahra ta yi gefe tare da É—aga hannun da zimmar dirza bakin Yusrah a bango. Nan kawai furucin Mami suka faÉ—o mata da cewa duk abin da za su mata kada ta kuskure ta tanka musu.

Furzar da iska Zahra ta yi waje sannan ta ce. "Ni banzo wajan nan domin na takale ku ba, na zo ne saboda na nail cutter É—in Mami".

ÆŠaukar nail cutter É—in da ke kan table Samira ta yi kana ta ce. "Gashi nan ba za'a bayar ba me za ki yi?".

Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Ni babu abi da zan yi kawai ki bani nayi tafiya ta salin alin".

Miƙe wa tsaye Samira ta yi ta ce. "Na ce ba za'a bayar ba, kina ƴar aiki kina yi mana magana yadda ki ke so, to ki sani cewa ko uwark..........

Maganar Samira ce ta dakata sakamakon tsawar da Zahra ta daƙa mata wanda saida ya ratsa ilahirin ɗakin baki ɗaya.

Take tsoro ya cikashe zuciyoyin su baki É—aya.

Cikin huci Zahra ta nuna Samira da ɗan yatsarta kana ta ce. "Duk abin da za ki yi to ya tsaya a kaina banda mahaifiyata. Idan kuwa ki ka kuskure ki ka yi sakin baki wajan furta magana mara daɗi kan uwata a ranar za ki san bambancin ƴar sarauta da kuma ƴar magarƙama. Maza miƙo min nail cutter ɗin kafin na ɓa ta muku rai".

Jiki na rawa Samira ta cilla wa Zahra nail cutter ɗin. Chafke wa Zahra ta yi sannan ta bi gaba dayansu da kallo tare da girgiza kai ta ce. "Na fuskanci cewa ba za ku iya zama da mutum cikin lafiya ba tare da wani hayaniya ba. Amma tun da haka ku ke so faɗuwa ta zo dai-dai da zama. Domin ni gyatumar ku ce a fannin rashin son zaman lafiya. Mu zuba mu gani, sai kun ɗanɗana wa aya zaƙin ta".

Tana kaiwa nan ta fice ta bar musu É—akin.

Suna ganin ta fita suka sauke ajiyan zuciya.
Kallon Samira Fasma da Yusrah suka yi sannan suka ce. "Me ya sa za ki ba ta nail cutter É—in?".

Amsa Samira ta basu da cewa. "Ta ya ya ba zan ba ta ba, kuna gani lokaci É—aya yadda fuskarta ya canza kuma ku ce kada na ba ta nail cutter, wannan idan haka bar mu da ita tsaff za ta zane mu, don wallahi yadda nake ganin yanayin ta kamar Æ´ar daba ko in ce Æ´ar jagaliya".

Tsaki Fasma ta buga kana ta ce. "An dai ji kunya wallahi, wai a ce wannan ƴar talakawan ta zo har masarautar mu tana razana mu, gaba ɗaya ta ana mutane saƙat dole muyi wani abu domin yin maganin ta. Idan ba haka ba to ba za ta daina ba, dole mu koya mata hankali".

"Ƙwarai kuwa Fasma, maganar ki gaskiya ce dole mu koya mata hankali".

*************************
"Amrah maza ki sauko mu shiga ciki kinji". Cewar Ramlat. Girgiza kai Amrah ta yi kana ta ce. "Babu in da zani, ni kawai ku maida ni wajan Æ´an uwa na, su nake son gani".

Dafe kanta Khairiya ta yi ta ce. "Shi ke nen zamu kaiki kinji. To sauko".

Girgiza kai Amrah ta yi alamun A'a.

Babu yadda suka iya haka suka koma ciki suka bar Amrah a kan bishiya.

**********
"Hello yallaɓai, mun samo matar da ka ce mu samu wannan malamar asibitin yanzu haka tana wajan mu a dajin da muka saba haɗuwa wajan yin harƙalla".

Murmushi Gov. Musa ya saki sannan ya ce. "That's great wannan good news ne ku bani nan da mintuna ashirin zan zo".

Yana kaiwa nan ya katse wayar. Yana sauke wayar ya ga kira ta kuma shigowa sai dai na wannan karan da private number haka kira.

Kallon screen É—in wayar Gov. Musa ya yi cike da mamani yake bin wayar da kallo. ÆŠaga wayar ya yi tareda saka wa a handsfree sannan ya ce. "Who's on the line?".

Ji ya yi an saki murmushi sannan ya ce. "Wato baka gane ni ba kenen, to MK ne, naji labarin cewa ka sa an sace nurse Nadiya saboda ta faÉ—a maka in da Mrs Laila take, sai dai kuma hakan ba zai yi aiki ba domin ita kanta ba ta san Laila na raye ba. Maza ka sa yaranka su sake ta idan kuma ba haka ba zan tona asirinka a wajan É—anka, na san da cewa babu abin da kafi so a duniyar nan sama da É—anka bayan É—anka sai kuÉ—i ko, to ka sani cewa ni É—in zan je na tona maka asiri na faÉ—a masa irin mahaifin da yake da shi".

ÆŠan jimm gov. Musa ya yi daga bisani kuma ya babbake da wata mahaukaciyar dariya.

Nan take ya haɗe ransa tamkar bai taɓa dariya ba ya ce. "Ta ina za ka faɗa masa ko ni ɗin wane ne?, wane hujja ka ke da shi a kan hakan?, ka sani cewa ɗana ba zai taɓa yarda da kai ba muddin ba hujja ka nuna masa ba".

Daga ɗayan ɓangaren Mk ya saki murmushi sannan ya ce. "Tabbas kayi gaskiya bani da hujja amma ka sani cewa ina da hujja ta yadda kayi amfani da makircin ka wajan kashe mahaifiyarsa. Ka san dai babu wanda ya fi ƙauna a duniyar nan sama da mahaifiyar sa kuma kai ɗin nan ka kashe ta saboda abun duniya".

Take gaban Gov. Musa ya faɗi!, yayin da zufa ya fara ƙeto wa ta kowane sashe na jikin sa. Duk iskan AC da ke kaɗa wa a ɗakin sa bai ana shi yin gumi da tamkar wanda haka watsa wa ruwan zafi haka gov. Musa ya rikice.

Tattaro nutsuwar sa ya yi kana ya ce. "Ta ya ya ka sani?, wane ne ya faÉ—a maka?".

Dariya Mk ya kwashe da shi ya ce. "Wato har ka manta da tsohon abokin ka kenen wato Abdullahi mijin Mrs Laila?, Kai da kanka ka sa his Excellency Abdullahi ya gudu daga Nigeria izuwa ƙasar China saboda sharrin da ka maƙala wa matar sa da kuma shi. Kada ka damu gaskiya ta kusan bayyana domin kuwa kundin littafin da ka ke nema na duk asalin abubuwan da ya faru yana nan cikin tsararren guri. Zan ƙara tunatar da kai idan ba ka sa yaranka sun saki Nurse Nadiya ba zan tona maka asiri. Sannan bara na faɗa maka wani abu, ƴar mrs Laila guda ɗaya tana Kano idan ka isa ka gano in da take kuma ka sace ta".

Yana kaiwa nan ya katse wayar. Gaba É—aya gov. Musa ya rikice da jin furucin Mk hakan ya sa ya yi gaggawan kiran yaran sa masu taya shi aikata miyagun laifuka sannan ya ce dasu su saki nurse Nadiya.

Kamar yadda ya buƙata haka suka saki nurse Nadiya yayin da suka maida ta gidan ta.

*AFTER ONE WEEK*
Ko ina a cikin masarauta ya cika yayin da haka ƙawata ko ina da kayan al'atu tare da na al'adu. Yayin da dakarai suka jeru sai kai kawo suke a masarautar.

Babu abin da ke tashi sai ƙamshi abinci da ƙamshi abubuwan laƙumashe. Yayin da ƴan aiki suka bazama sai girke-girke da share-share suke.

Jin hayaniya ya sa Zahra miƙe wa daga kan gadon ta tare da yin miƙa sannan ta ce. "Wai yau me ke faruwa a masarautar nan ne?, kodai baƙo za su yi ne?".
Ta tambayi kanta.

Takawa ta fara yi tare da nufar hanyar waje sannan ta fice daga É—akin. Nan taci karo da Mami wacce ta ci kwalliya cikin shigarta na alfarma.

Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin Mami da kallo. "Mami irin wannan kyau haka, meke faruwa a ne?".

Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "Magajin wannan masarautar ne zai dawo wato gawurtaccen ɗana Sooraj, duk waɗan nan kwalliya da yadda haka ƙawata masarautar nan duk saboda shi ne, s duk sanda zai dawo daga ƙasar waje to ana taruwa ne ayi masa tarba mai kyau".
Chapter 36 · 0% Book details