← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsa likitan ya ba shi da cewa. "Lafiya ƙalau munyi nasaran cetan ta domin kuwa yanzu harta samu bacci. Hamdala DPO ya yi sannan ya ce. "Yanzu zamu iya shiga mu ganta?".

"Eh za ku iya, amma dan Allah banda hayaniya". Yana kaiwa nan ya bar wajan.

Shiga ciki gaba ki É—aya suka yi, yayin da suka tarar ba ta kan gadon. Zaro ido gaba É—aya suka yi ganin ba ta kan gadon. Kallon jami'an DPO ya yi ya ce. "Me ya sa muka yi sakaci har ta fece daga nan".

Daga sana suka ji muryarta na cewa. "Yallaɓai DPO gani fa a ta nan". Zahra ta faɗa tana mai sakin murmushi.

Kallon ko ina suka yi basu ganta ba. Nan take suka maida kansu kan gado.

Kallonta DPO ya yi ya ce. "Ta ya ya kuma ki ka dawo kan gado bayan bakya nan?".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ta ya kuma, kune dai baku duba ba da kyau amma ni dai ina nan banje ko ina ba".

Ajiyan zuciya DPO ya sauke sannan ya ce. "Shi ke nen ta so mu ta fi tun da kin samu lafiya".

MurguÉ—a baki Zahra ta yi sannan ta ce. "Ku fita to zan yi wani abu".

Duk abin da za ki yi kiyi babu in da zamu je, wato so ki ke ki gudu ko?".

HaÉ—e rai Zahra ta yi ta ce. "Idan na gudu ina zanje?, wa na sani a wannan garin?, zan yi turoso ne shi ya sa".

"Shashasha kawai". DPO ya faÉ—a tare da fita daga cikin É—akin. Fice wa sauran Æ´an sandan suma suka yi daga cikin É—akin.

Tsaki Zahra ta ja ta ce. "tsohon banza kawai, idan an girma a san an girma. Ya tsaya yana biye wa sa'anin Æ´aÆ´an sa. Guduwa ce kuma ya zama dole, domin tabbas saina gudu, haka kurun za'a kaini wani gidan gyaran hali sai ka ce wacce take rashin É—a'a".

Ta faɗa tana mai waige-waige. Nan take wani dabara ya faɗo mata. Tashi ta yi tsaye tare da nufar ƙofar window sannan ta buɗe tare da fita ta wajan.

"Yess". Ta faÉ—a cike da farin ciki". Sauri-sauri take domin ta fice daga cikin asibitin. Babu zato ta ji an rungumeta ta baya.

Zaro ido waje ta yi tare da juyawa. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa?, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku. Take ta tsinci kanta cikin baƙon yanayi.

Sakinta matar wacce ta yi burzuzu da gashin kanta tamkar mahaukaciya ta yi. Kallonta matar ta yi ta ce. "Ki fitar da ni daga nan ni ba mahaukaciya ba ce kinji, ina so na koma ga ahali na, ina son na ga yarana".

Nan take jikin Zahra ya yi sanyi dubar matar ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri ki koma, magani suke miki fa". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin barin wajan.

Da sauri likitoci suka ƙaraso wajan suna mai rirriƙe matar. Kallon Zahra suka yi sannan suka ce kiyi tafiyar ki yarinya, ita ɗin mara lafiya ce, kada ki damu da duk abin da za ta faɗa miki".

Girgiza kai Zahra ta yi tare da fice wa daga cikin asibitin. Ta rasa me ya sa tun da ta ga wannan matar hankalinta ya kasa kwanciya.

Zama ta yi a bakin titi tana mai hasko matar a cikin idanuwanta. "To wannan matar wace ce?". Ta tambayi kanta. Basar wa ta yi sannan ta ce. "To koma wace ce ina ruwanki zahra, kiyi abin da zai finshe ki kawai".

Dafe cikinta ta yi jin yadda yake murɗawa saboda yunwa. Daga nesa ta hangi shopping mall. Da sauri ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Dole na je na ci wani abun don ba zan zauna da yunwa ba".

Ta faɗa tare da nufar wajan. Nan take ta ga fadawa da securities na fito wa daga cikin wajan. Yayin da ta ga mutanen wajan gaba ɗaya sun ɗuƙa ƙasa.

Shiga cikin wajan ta yi yayin da ta ga kowa gwiwar sa a ƙasa. Sakin baki ta yi tana kallonsu. "To me ya mi waɗan nan mutanen kuma na ga kowa a durƙushe. Koda yake wannan ba damuwar ki ba ce ba". Ta faɗa tana mai ƙara shige wa cikin wajan.

Chan ta hangi ma'aikacin wajan a durƙushe a ƙasa. Ƙarasawa ta yi wajan sannan ta ce. "Ina son a bani snacks ko lemo duk abin da ku ke da shi wanda zai ƙosar da ni".

Alamu mutumin ya yi mata da ta yi shiru. Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Bangane ba, na ce ka zo ka saida min da abu ka ce nay shiru, saboda me?, ko kyauta ku ke bayar da kayan naku ne?". Ta faÉ—a cikin É—aga murya.

Daga sama ta ji an ce. "Wane ne yake mana wannan tsawan?". Nan take mutanen wajan suka sha jinin jikin su.

Juyawa ta yi da zimmar zuwa ta ɗauki abin da ranta yake so. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani handsome mature guy mai jini a jiƙa.

Kallonta ya yi da idanuwansa masu matuƙar rikitarwa sannan ya ce. "Me ya sa ke baki tsungunna ba bayan kowa dake cikin nan ya durƙusa min, kin san wane ne ni?".

Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin shi da kallon rainin wayo. Kallon sama da ƙasa ta yi mishi sannan ta ce. "First of all matsa min daga hanya". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.

Ƙara tunkaro in da take ya yi sannan ya ce. "Idan na ƙi fa?, kin san waye ni? , ni ɗin yarima ne understood?".

Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce"au haba da gaske?, amma sam baka yi zubin ƴan sarauta ba, ka san da irin su wa ka ke kama a jigawa?, kana kama ne da ƴan daƙo, domin kuwa wannan kayan da ke sanye a jikin ka su ƴan daƙon jigawa suke sawa".
Ta faÉ—a tana mai kuma fashe wa da dariya a karo na biyu.

A fusa ce. "Yariman ya ce. "Za ki san ni ki ka gaya wa wannan maganar".

Nan take yanayin Zahra suka sauya izuwa ɓacin rai sannan ta dube su baki ɗaya ta ce. "Idan kun isa ku tunkaro in da nake".

**************************
Umar na isa asibiti, likitoci suka saka Amrah kan gado yayin da suka shiga yi mata aiki domin cire bullet ɗin da ke ƙafarta.

Fita ya yi tare da koma wa cikin mota sannan ya nufi hanyar gida. Da mugun gudu yake tuƙa motan yayin da yake ji kamar ya tashi sama domin zuwa in da mahaifinsa yake. Mintuna ƙalilan ya yi masa a gida. Ko gama parking bai yi ba ya fito daga cikin motan tare da nufar hanyar gida. Ƙafar sa na dama ya sa tare da ɓalla ƙofar parlourn.

Nan take mahaifinsa tare da jami'an dake cikin wajan suka miƙe tsaye.

Kallonsu gaba ɗaya Umar ya yi sannan ya ce. "Me ya sa ku ka je ku ka kashe kowane halitta a cikin wannan dajin?, ba na ce bana buƙatar wajan nan ba?, to me ya sa za ku kuma koma wa wajan?, why Abba?".

Ajiyan zuciya Gov. Musa Muhammad ya sauke sannan ya ce. "Nayi hakan ne saboda farin cikin ka son".

Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Farin ciki na?, kayi hakan ne saboda farin cikin ɗanka, baka ji kunyar abin da ya fito daga bakin ka ba, ka tsayar da fari cikin wasu domin samar min da gurɓatacciyar fari ciki mara ɗore wa, kuma a hakan ka ke kiran kanka ɗan siyasa?, shin dama haka shugabanni suke wa waɗan da basu ji ba basu gani ba?".

"To gaba ɗaya ku saurare ni kuji, muddin wannan yarinyar ta mutu ba zan ƙyale kowane mutum daga cikin ku ba hatta kai Abba, kuma sannan wannan farin cikin da ka ke faɗa to za ka rasa shi na har abada ne, domin kuwa ba za ka sake sanya idanuwanka a kaina ba".

"A'a Umar, kada ka yi haka, in sha Allahu babu abin da zai same ta kaji, kada ka nesanta kanka da ni Please".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya yi sannan ya ce. "Saboda gudun abin da zai bata min rai hakan ya sa na koma london da zama, kuma duk saboda kai, me ya sa ka ke ƙoƙarin cusa min tsanar ka a cikin zuciyata Abba?. To zan faɗa zan ƙara maimaita wa muddin yarinyar chan ta mutu saikun gane kuranku baki ɗaya. Kuma sannan shi companin ma bana da buƙata, domin bana son koda naira goma daga cikin dukiyar ka, bana so".

Yana kaiwa nan ya fice daga cikin É—akin.

Kallon jami'an Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Shashashan banza ku sani cewa muddin ɗana ya yi nesa da ni saina ga bayan ku, maza ku ɓace min daga gani".

Fita jami'an gaba É—aya suka yi. Wayarsa ya ji tana ringing.

ÆŠaukar wayar ya yi yayin da ya ga private number bayyane kan screen É—in. ÆŠaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa.

Daga ɗayan ɓangare haka ce. "Barkan ka dai govnor Musa Muhammad. Na san za ka yi mamaki to ni ne, ban mutu ba ina raye. Na kira ka ne domin sanar maka da bad news a gare ka, mrs Laila wacce kayi sanadin rugujewar rayuwarta har izuwa yanzu tana raye".

Zumbur gov. Musa Muhammad ya miƙe tsaye. Yayin da zufa ya fara ƙeto masa ta kowane sashi na jikinsa. Duda iskan AC da ke kaɗawa a cikin parlourn hakan bai hana shi yin zufa ba.

Cikin rawar jiki Gov. Musa Muhammad ya ce. "Waye kai?".

Amsa mutumin ya ba shi da cewa. "Ni ne ɗan sanda wanda ku ka saka haka rufe tsawon shekaru, ni ne MK wato Mubarak. Ka ɗauka ban san duk wani shirin ka ba?, na san da cewa ka aiki ɗaya daga cikin masu ta ya ka aikata miyagun laifuka domin ya yi magana da ni a cikin magarƙama domin neman in da yarinyar Mrs Laila take. Amma sai dai kafin ya zo waje na wata ta dakatar da shi. Ka san wace ce?, to ƴar Mrs Laila ce".
Chapter 20 · 0% Book details