← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 59

Sashe 45

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyan zuciya Grandma ta sauke sannan ta ce. "Wane hoto kenen?".

Amsa Safira ta ba ta da cewa. "Wani photo kwanaki da na taɓa gani a parlour".

Sauke ajiyan zuciya Grandma ta yi a karo na biyu. Sannan ta ce. "Kina nufin Æ´ata Lailah?".,

Girgiza kai Safira ta yi alamun eh sannan ta ƙara da cewa. "Tana ina ne?, ita ɗin bata da ƴaƴane ko kuwa bata nan ne?".

Amsa Grandma ta ba ta da cewa. "Lailah ko ta na raye ko ta mutu Allah ne masani, sannan maganar Æ´a tabbas a shekarun baya an kawo Æ´ar da ta haifa a gidan yari aka kawo ta mahaifin Lailah ya yi rejecting É—in yarinyar. A yanzu haka bamu sani ba ko tana raye ko kuma ta mutu, amma fatana shi ne idan suna raye gaba É—aya Allah ya cigaba da kare su sannan kuma Allah ya dawo da su wannan family É—in mu koma yadda muke a da, mu cigaba da rayuwa cikin farin ciki, shi ne kawai fatana".

Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "Amma mene ne ta yi da har Grandpa yaƙi karɓar yarinyar ta sannan kuma ita mene ne ta aikata da har aka kaita gidan yari?".

Murmushi Grandma ta yi sannan ta ce. "Labari ne mai dogon zango ko ni kaina ban san tushen labari ba, amma ni na san da cewa Lailah ba zata taɓa aikata abinda haka ce tana yi ba domin na yarda da ita ɗari bisa ɗari, Lailah tana da kyakyawar zuciya. Tana gudanar da aikin Company tana taimaka wa talakawa marasa ƙarfi, sannan ta saka yaransu a makaranta yayin da ta buɗe gidan marayu na marasa iyaye. Duk don ta taimaka wa al'umma amma shi ne haka ƙaƙala mata sharri haka ce duk tana hakan ne saboda kuɗi".
Ta ƙarasge maganar tana mai fashe wa da kuka.

Tausayin Lailah ne ya kama Safira hakan ya sa ta ƙudiri aniyar cewa duk sanda ta zama lawyer saita wanke Lailah.

*******
"Ya ƙuri na taka ka bada sani na ba". Cewar Sooraj.

Murmushi MK ya yi sannan ya ce. "Ƙwarai na san ba da sanin ka kayi hakan ba domin hakasari ma ni ne nan wanda na sa ƙafata a wajan da zaka wuce".

Nan take fuskar Sooraj ya sauya daga walwalah zuwa ɓacin rai. "A kan me ya sa za ka saka min ƙafa a wajan tafiyata?, so ka ke na faɗi ko me?".
Cewar Sooraj

Girgiza kai MK ya yi ya ce. "A'a ko ɗaya, nayi hakan ne domin janyo hankalin ka izuwa gare ni. Shin mene ne alaƙar ka da Mrs Laila Abdullahi?".

Shiru Sooraj ya yi jin tambayar da bai san amsarta ba. Kallon mk ya yi ya ce. "Me ya sa ka ke son sanin alaqa ta da Mrs Laila, tukunan ma wane ne kai?, me ya sa ka ke bibiyar rayuwar mrs Laila da tawa?, ka faÉ—a min waya turo ka?".

Tashi tsaye mk ya yi daga kan kujerar da yake kai sannan ya ce. "Ni ne wannan É—an sandan da ya taimaka wa Mrs Laila Abdullahi a shekarun baya. Na É—auka Laila ta mutu, sai kuma daga baya na gane cewar taba raye bata mutu ba, hakan ya sani yin farin ciki, yanzu dai ina da good news da zan baka. A cikin yaran mrs Laila akwai guda É—aya a cikin masarautar ku".

Zaro ido waje Sooraj ya yi ya ce. "Da gaske ka ke?, wace ce?".

Murmushi MK ya yi ya ce. "Ba zan faÉ—a maka ba kai ka gano ta da kanka, ita ma É—aya daga cikin ma'aikatan masarautar ce. Abinda kawai zan faÉ—a maka kenan, na barka lafiya". Ya faÉ—a yana mai barin wajan.

Ruɗani Sooraj ya shiga tare da ƙoƙarin gano ko wace ce amma hakan ya cutura. Shiga cikin matarsa ya yi tare da tada wa yana mai barin harabar wajan.

*****
"Yahya Amrah na ƙoƙarin fita daga gida". Cewar Usman.

"What!". Cewar Umar, sannan ya ƙara da cewa . "Amrah kuwa, saboda me, muje na gani". Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye sannan suka fita suna zuwa suka tarar ta fice daga gidan.

Tarar da su Ramlat suka yi a zaune a jugun, ganin Umar ya fito ya sanya su faÉ—in. "Yahya Amrah ta tafi, mun bi bayanta amma bamu ganta ba".

Jin hakan ya sa hankalin Umar ya tashi, "Kamar ya baku ganta ba, muje mu nemo ta domin ba zan yafe wa kaina ba idan wani abu ya same ta". Ya faÉ—a suna mai shiga mota tare da barin gidan domin neman Amrah.

******
Zama Zahra ta yi tana mai bin komai na kitchen É—in da ido nan ta shiga tunanin ta ya ya zata fara girkin. Tunani ta yi ta duba google sai kuma ta yi duba da cewa ita É—in bata da waya.

Jungum ta yi tana mai cigaba da bin kitchen da kallo.

Daidai lokacin Gimbiya Saratu da Talatu suka shigo cikin kitchen É—in tare da kwashe wa da dariya.

Riƙe ƙugu Gimbiya Saratu ta yi sannan ta ce. "Ya dai?, kin kasa girkin ne?, an dai ji kunya".

Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ke Zahra ko mene sunanki, kin san ba za ki iya girka ba me ya sa ki ka cinye abincin?, gashi kuma shi Sooraj ba zai barki abinda ki ka yi ya tafi a banza ba dole ne ki yi girkin nan ko kin iya ko baki iya ba".

Murmushin takaici kawai Zahra ta yi tare da girigza kai ta ce. "Ban san me ya sa mutane suke shiga abin da babu ruwansu ba, sai kutsen jaraba kamar tinkiyoyi, mutane baka shiga harkar su ba amma dole su shiga harkar ka, sun shigo da wasu ƴan matan ƙafafuwansu sun zo suna min aushi".

Kallon ta Gimbiya Saratu ta yi rai ɓace ta ce. "Da wa ki ke?, abaici ki ke ko me?, wallahi ki shiga taitayinki domin ni ba sa'ar uwar.......
Maganarta ce ta tsaya chakk sakamakon tsawar da Zahra ta daka mata. Nan take suka sha jinin jikinsu.

Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Kada ki kuskure ki ƙarasa wannan kalmar, da a ce kin ƙara da yau za ki san bambancin jinin sarauta da kuma jinin talaka. Ban tanka muku ba dan haka ku barni, ni zan yi kayana da kai na".

Ba tare da sun so ba haka suka fice daga cikin kitchen ɗin. Shigowa ƴan aiki suka yi domin su taya Zahra girka abincin, amma Zahra taƙi amincewa da su tayata. Ba yacce suka iya haka suka fice suka bar mata kitchen ɗin.

Ganin zama ba zai finshe ta ba, ya sanya ta miƙe wa tsaye sannan ta fara shirye-shiryen girkin.

Haka ta cigaba da girki cikin tunani, yayin da duk abin da ta gani zuba wa kawai take ba tare da sanin mene ne shi ba. Bayan nan ta yi blending É—in kunun aya a blender sannan ta tace garin nan ta saka mai su flavour da dai sauran kayan da ba za'a rasa ba.

Haka ta cigaba da yin girkin ba tare da ta huta ba. Ba ita ta gama girkin ba sai bayan insha'i.

Zama ta yi tana mai yarfe zufan da ke ƙeto mata. "Tunda nake ban taɓa shan wahala irin ta yau ba, ba gaira ba dalili wan can banzan mutumin ya sani girkin dole, na san ma ba zai yi dad'i ba".

Ta faɗa tana mai jera abinci sannan ta fita daga cikin kitchen ɗin. Tare da nufar hanyar dining sannan ta ajiye abincin tare da fara ƙwalla wa gaba ɗayansu kira.

Cikin kankanin lokaci gaba É—aya suka hallara daidai lokacin shima Sooraj ke fitowa daga part É—in shi

Zama suka yi a kan dining É—in sannan Zahra ta zuba wa Sooraj abinci domin ya ji É—anÉ—anon. ÆŠaukar spoon Sooraj ya yi sannan ya ci chokali É—aya, ji ya yi abincin ya yi daÉ—i, amma dan kada ya nuna cewa yayi dad'i hakan ya sa ya haÉ—e rai. "Wannan wane irin abinci ne haka mara daÉ—i?, ko taste babu. Maza ku kwashe abincin nan ku kaiwa karnuka su ci".

"Ƙwarai kuwa domin mu ba zamu ci wannan ƙazamin abincin ba". Cewar su Gimbiya Saratu da su Samira.

Murmushin gefen baki Zahra ta yi, sannan ta cire ɗan kwalin kanta tare da ɗaura wa a ƙugu sannan ta rungume hannayenta a ƙirji, ta maida kallonta kan Sooraj ta ce. "Me ma kace?, a kaiwa karnuka abincin da na ɓata lokaci na wajan yinsa, kunsan hawanni nawa nayi ina girka abincin nan tare da haɗa su fruit salad da kuma kunun aya shi ne za ku ce ba za ku ci ba. Ai wallahi tallahi baku isa ba, na rantse da Allah sai kunci wannan abincin tass".

Ta faɗa tana mai nufar hanyar ƙofar parlour tare da saka wa ƙofar parlourn maƙulli sannan ta saka maƙullin a cikin aljihunta.

"Mene ne ki ke ƙoƙarin aikata wa?, wato muci wannan abincin, to ba za mu ci ba, kiyi abin da ki ka ga za ki iya". Cewar su Fasma.

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ashe yau za'ayi tashin balagan tsuntsaye a masarautar nan, chabb wallahi yau akwai tashin hankali a masarautar nan muddin baku zauna kun cinye abincin nan ba. Wato na gama shan ɓakar wahala shi ne za ku ce za ku kaiwa karnuka dan ma kun raina wa mutane wayo, to ku sani idan kuna yiwa kowa iskancin ku ba zaku yi min ba. Maza-maza ku fara ci dama ai kuna da hannu maza ku zuba da kanku kuci salin ali abunku ɗanoinoi".

"Ba za mu ci ba me za ki yi?". Cewar Sooraj.

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ohh nufin ku ba za ku ci wannan abincin ba?, haka ku ka ce ba za ku ci ba ko?, uhmm shi ke nen. Idan baku ci ta lallami ba za ku ci da ƙarfi da yaji". Ta faɗa tana mai shiga ɗakinta.

Tsayawa gaba ɗaya suka yi domin ganin me ta shiga ɗauko wa. Gani suka yi ta fito hannunta riƙe da igiya tare da turare.
Chapter 45 · 0% Book details