← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka yarda da ni yanzu na chanza, baka gani ba ina kuka ɗazu, ina dana sani ne, idan muka koma gida ma zan je na bawa su Gimbiya Saratu haƙuri, ni yanzu na chanza kuma chanza wa na har aba........ Maganarta ya tsaya chak sakamakon taka ta da wata matashiyar budurwa ta yi.

Nan take Zahra ta zaro idanuwa waje tare da fara kutuntuma ashar. "Kutumeli chan, idan na yarda shegiya nake, har ni zata wuce ta taka kuma taƙi bani haƙuri saboda shegiya ce, zata gane kuranta ". Ta faɗa tare da ƙoƙarin bin bayan budurwar.

Da sauri Sooraj ya dakatar da ita sannan ya ce. "Yanzu fa ki ka ce min za ki chanza, amma kuma kinga abinda ki ke yi".

Girgiza kai Zahra ta yi jikinta na tsuma ta ce. "Na san na faÉ—i akan. Amma ka bari na fara koya mata hankali kafin nan saina chanza".

Ta faÉ—a tare da nufar hanyar da budurwar ta yi.

Dafe kansa Sooraj ya yi ya ce. "Wallahi Wannan yarinyar duk wanda ya aure ta zaiga bala'i, domin wannan annoba ce". Ya faÉ—a tare da bin bayanta.

Ƙara sauri Zahra ta yi yayin da kafafuwanta na harɗe wa dana juna saboda tsananin sauri da kuma bala'in da take.

Ganin budurwar na ƙoƙarin shiga mota ya sanya ta fara gudu harta isa inda budurwar take.

"Ke!". Zahra ta daka mata tsawa.

A razane budurwar ta É—ago idanunta tare da duban Zahra ta ce. "Who are you?, me ki ke nema, kinga kiyi tafiyar ki bani da chanjin da zan baki, dan haka ku baratan nan ku ke da zarar kun ga mai kuÉ—i ku ke kiÉ—ime wa".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Yau akwai ƙura, wato ni ce mabaraciya ko?, kin taka ni kin wuce shi ne ko ki iya bani haƙuri".

Kallon sama da ƙasa budurwar ta bi Zahra da shi sannan ta ce. "Ai na san na taka ki, kuma ina sane nayi hakan, dan aka ki ɓace min daga gani".

Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Idan kinga kin bar wajan nan to bani bace. Kalle ni nan wallahi ni bana ɗaukar raini, kina wani tafiya kamar wata lanƙwasashiyar sanda. Ke daɗin abun ma baki da wani kyau balle kiyi wa mutane iyayi, kalli fa fuskarki yadda ka san wata akuya wacce ta yi shekara ta jin yunwa, ga kunnuwa fala-fala, kamar gwargwaron amarya, kin buɗe ƙwaƙwidon kanki a waje ko gashin ma babu yadda ka san gashin hammatar ɗan iska, kina wani fallewa kamar injin markaɗe. To wallahi ki sani cewa muddin baki bani haƙuri ba saina ci ubanda ya yi tattalin goron auren bikin uwar... Da sauri Sooraj ya rufe mata baki.

Wafce jikinta Zahra ta yi daga nasa sannan ta ce. "Me ya sa za ka dakatar da ni".

Maida kallonsa Sooraj ya yi kan budurwar ya ce. "Zubaida kada ki damu da abinda ta faɗa miki kiyi haƙuri kiyi tafiyarki ".

Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Daman ka san wannan mahaukaciyar?".

Amsa Sooraj ya ba ta da cewa. "Ba mahaukaciya ba ce ita É—in wacce zan aura ce".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai cewa. "Akwai ƙura kuma a akwai kallo. Gaskiya babu mai mummunar sa'a a duniyar nan kamar kai, duk rashin sa'an wasu ya biyo bayanka. Kai yanzu me ka gani a jikin wannan mai kama da jaɓar?".

"Ki iya kalaman ki Zahra, auren haɗi za'a yi mana, kuma bana son ki ƙusa baki ciki". Cewar Sooraj.

Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Abun qauna, me ya sa ka ke yawo da wannan ballagazar, kodai budurwar ka ce?, yanzu kenen cin amana ta ka ke ban sani ba".

A fusa ce Zahra ta ce. "Yaci amanar taki É—in me za ki yi?, ke zanci bala-balan banki bariki.......

Bata ƙarasa ba taji an kwashe ta da mari. Dafe ƙuncinta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj, mari na kayi, ni ka mara?".

Girgiza kai Zahra ta yi cikin jin aushi ta fita daga asibitin.

Da sauri Sooraj ya koma inda motarsa take tare da tada motan sannan ya fice da sauri daga cikin asibitin tare da bin bayan Zahra.

*********************
Ɓangaren Aliyu kuwa Kano ya nufa da Safira tare da kaita kangon dake cikin daji. Sannan ya yi parking tare da fito da Safira yana mai shigar da ita cikin kangon tare da ɗaure ta. Tana kuka haka ya kammala ɗaure ta sannan ya dube ta ya ce. "Ba za ki san dalilin da ya sa nake miki hakan ba, amma nan bada jimawa ba zaki fahimta".

*****************
Umar kuwa yana cikin tuƙi wasu ƴan daba suka tsayar da motarsa. Nan suka buɗe motar tare da fesa mai hoda wanda ya sanya shi fita daga cikin hayyacin shi. Nan take ya suma. Shiga motan suka yi da shi tare da tada motan suka bar wajan.

Cikin motan kuwa Amrah ce kwance bata cikin hayyacin ta. Chan kangon da Aliyu ya nufa da Amrah aka nufa.

Yayin da aka jefa su a ciki.

***********
"Zahra kiyi haƙuri ki shigo mu tafi". Cewar Sooraj yana mai cigaba da bin bayan Zahra.

Harara Zahra ta galla mai ta ce. "Ba zan shigo ɗin ba, yanzu ka gama mari na kuma kace na shigo, to ba zan shiga ba. Kaje chan da riɓaɓɓiyar motar ka".

Ganin Zahra ba zata bashi haɗin kai ba ya sashi tsaida mota tare da fito wa daga ciki sannan ya nufi inda take, bai bata lokaci wajan ɗaukar chakk ya ɗora a ƙafaɗa. Fusge-fusge Zahra ta fara yi amma samm Sooraj bai ajiye ta ba har saida ya isa motarsa sannan ya direta tare da sakawa motan key. Sannan ya zagaya ya shiga yana mai tada motan suka bar wajan.

Kai tsaye Masarauta suka nufa a sa'inda babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka isa. Mamaki ne ya kama Zahra da Sooraj ganin yadda fadawa da dogarai tare da ƴan aiki da mai martaba tare da su Gimbiyoyi suka taru guri ɗaya.

Fitowa Zahra da Sooraj suka yi daga cikin motan.

Fashe wa da kuka Gimbiya Saratu da Samira suka yi. Kallon su Sooraj ya yi ya ce. "Me ke faruwa ne naga mutane sun taru?".

Share hawayenta Samira ta yi ta ce. "An nemi sarƙar zinaren Ammi an rasa, shi ne aka ce kowa ya fito, wasu fadawa ne da dogarai ne suke searching kowane saƙo da lungu na gidan kuma duk wanda aka ganshi a ɗakinsa shi ne ɓarawon".

Mami kuwa babu abinda take in banda addu'ar ganin gold É—in.

Zahra taɓe baki ta yi dan ta san bata ɗauki wani gold ba.

Saida suka shafe kusan awa guda a tsaye kana daga bisani suka jiyo muryoyin fadawa na faÉ—in an ganshi.

Ƙarasawa wajan fadawa guda biyar suka yi tare da miƙa wa mai martaba gold.

Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "A ɗakin wa ku ka ga sarƙar gold ɗin?".

Amsa É—aya daga cikin fadawan ya bada da cewa. "A É—akin É—aya daga cikin ma'aikatan masarautar nan wato Zahra".

Zaro idanuwa waje gaba ki É—aya jama'ar da ke wajan suka yi.

"Zahra kuma!". Mami ta faÉ—a cikin shiga ruÉ—ani.

Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Wannan ƙarya ne, ni ta ya ya zan ɗauki gold bayan ban san ma da shi s fadar nan ba, wallahi bani bace".

"Ƙarya ki ke, dama ba yau ki ka fara yi mana sata ba, kin daɗe kina yi shi ne yau Allah ya tona asirinki, dama an ce rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya". Cewar Gimbiya Saratu.

Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zahra ya ce. "Zahra da gaske ke ki ka saci wannan gold É—in?, me ya sa za ki aikata hakan".

Hawayen da Zahra ke ƙoƙarin riƙe wa ne suka suɓuce mata. Dubansu ta yi ta ce. "Wallahi bani bace ba, sharri kawai suke suyi min saboda a kore ni daga masarautar nan saboda ina muzguna wa rayuwarsu. Amma wallahi sata ba hali na ba ne".

Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra babu sharri ko ƙarya a nan an ga sarƙa a ɗakin ki, ta ya ya to sarƙar ta shiga ɗakin naki?, ko ita sarƙar ce zata kai kanta ɗakin?".

"Kenen kema Mami baki yarda dani ba?". Cewar Zahra wacce duk ta bi ta rikiÉ—e.

"Waye ma zai yarda da ke, ɓarauniya, dama aka ku talakawan nan ku ke da zaran kun samu guri, ku ke iskanci yadda ranku ke so". Cewar Gimbiya Talatu.

"Maza zo ki fice daga cikin masarautar nan bamua son sake ganin fuskarki". Cewar Sooraj wanda ranshi ya yi matuƙar ɓaci.

"Dakata!". Suka ji an furta. Juyawa gaba ɗaya suka yi domin ganin wane ne, MK ne tsayem ƙarasowa wajan su ya yi sannan ya dubi kowanne daga cikin su ya ce. "Zahra tafi ƙarfin ta saci gold. Kun san wace ce mahaifiyar ta. Idan da a ce kun san wace ce Zahra da kun dinga yi mata hidima. Mahaifiyar ta na ɗaya daga cikin masu kuɗi na duniya wanda kowa ya san da hakan".

Mamaki ne ya kama kowanensu.

Mamaki ne ya kama Zahra dan ita ta san dai ba ƴar masu kuɗi bace. Kallon Mk ta yi ta ce. "Bana son kayi min ƙarya ni mahaifiya ta ma ban taɓa ganinta ba, kuma ni ɗin ba ƴar masu kuɗi bace asali ma ni ɗin a kurkuku na taso, dan haka karka yi min ƙarya dan ka kare ni".

Murmushi Mk ya yi sannan ya ce. "A wajan ki ke ƴar talakawa ce, amma a zahiri ke ɗin ƴar gidan masu arziƙi ce. Idan da a ce ana siyan masarauta, to tabbas babu tantama a cikin dukiyar ki ƙarami daga ciki zai siyi Masarautar nan har sau biyar".

Jin hakan ya sa kowanensu ya zaro idanuwa waje.

MANAGE PAGE PLEASE 🙏 🙏 🌹. KUN JINI SHIRU KWANA BIYU, WAYATA CE TA LALACE, AMMA YANZU NA GYARA DA YARDA ALLAH ZAN DINGA MUKU UPDATE A KAI A KAI.

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)
[12/2, 19:56] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Chapter 52 · 0% Book details