Sashe 51
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ya sa bakya jin tsoro na Zahra?".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Hakan me zan dinga jin tsoron ka kaida ba maye ba, aini babu wanda nake tsoro sai Ubangiji na".
Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Kin san ina zanje ne kika zaɓar min Ishirinka a maimakon genzna?".
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Ina za ka je kuwa in banda wajan ƴan matan ka, dan yadda na ga ranka ya yi mugun ɓacin nan nasan cewa akwai wata a ƙasa. Koma dai mene ne, ni ban ana ka zuwa wajanta ba zaka iya tashi ka tafi".
Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Samm ni bana da Æ´an mata balle budurwa, zanje wajan mahaifiyata ne".
Jin maganar sa ya sa Zahra shiga cikin ruÉ—ani. Dubansa ta yi ta ce. "Wace mahaifiyar kuma bayan Mami?".
Amsa ya bata da cewa. "Ƙwarai Mami ita ce asalin mahaifiyata, kuma ita ma waccan tamkar mahaifiyata na ɗauke ta, yanzu haka na san tana asibiti tana jira na".
Shiru Zahra ta yi ta ce. "To ita bata É—a ko Æ´a ne?".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Zomu je chan zan baki amsa".
Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye tare da fice wa daga gidan. Babu gardama ta bisa a baya.
Motar da ta ga ya shiga ta shiga, a sa'inda ya tada mota tare da fita da su daga cikin masarautar, kai tsaye asibitin da Mrs Laila take suka nufa.
************
Umar kuwa hawanni ƙalilan ne ya ɗauke shi ya isa Jigawa kai tsaye gidan su ya nufa, bai gama parking ba ya fito daga cikin mota tare da shiga cikin babban parlour.
Nan ya tarar da mahaifin shi zaune kan kujera yana shan juice.
Furzar da iska mai zafi Umar ya yi waje sannan ya dubi mahaifin na shi ya ce. "Abba".
Sai a lokacin Gov. Musa ya lura da zuwan Umar wajan. Saurin miƙe wa tsaye ya yi sannan ya ce. "Son yaushe ka shigo?, ina su Khairiya suke?".
"Abba ban taɓa tunanin zaka iya aikata abinda aka faɗa min saboda kuɗi ba". Umar ya faɗa a yayin da idanuwansa suka yi ja tamkar an zuba garwashi.
Rass! Gaban Gov. Musa ya faÉ—i. Cikin ransa ya ce. "Kodai Umar ya gano munanan hayyukana ne?".
Kallon Umar ya yi ya ce masa. "Umar ban fahimci inda ka dosa ba, me kake nufi da hakan?, ka fahimtar da ni".
Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Really?, wato baka san me nake nufi ba, wai tukun nama shin kai mahaifi na ne ko maƙiyi na?, me ya sa za ka sa a sace Amrah?, wato kenen aikin ka shi ne safaran mata ko. Karka manta ni jami'i ne mai gaskiya, kuma duk wanda yake yin laifi burina shi ne a hukunta shi, koda kuwa ƙanne na ne balle kuma kai. Ba zan yi duba da cewa ko kai mahaifi na ba ne, dole na miƙa ka domin a hukunta ka".
Koma wa gov. Musa ya yi kan kujerar da ya tashi tare da zama yana mai fuskantar Umar ya ce . "Wato harma wani zai zo ya faÉ—a maka mummunar magana a kaina kuma ka yarda?, banyi tunanin hakan daga gare ka ba, kai É—in É—ana ne mafi soyuwa s gare ni, ni ne nan na É—ora ka a matsayin da ka ke a halin yanzu".
"A'a, samm ba kai ba ne ba, jajircewa ta da kuma ƙwazo na ne ya kaini wannan matsayin ba kai ba, ka faɗa min gaskiya shin kana aikata abinda ake tuhumar ka da shi?". Cewar Umar.
Shiru Gov. Musa ya yi na É—an wasu lokaci kana daga bisani ya ce. "Kenen dai baka yarda da ni ba?, well shi ke nen, tunda yanzu babu yarda tsakanin mahaifi da É—a me ya rage, kawai ka zo ka saka min handcuf ka kaini kotu a yanke min hukunci. Ba aka ka ke so kaji na ce ba. So ka ke na faÉ—i abinda banyi ba na ce nayi".
Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. "Shi ke nan Abba, bama sai ka faɗa min ba, ni da kaina zan gano. Kuma ka sani cewa muddin da gaske ne abinda aka faɗa a kanka ba zan bari ka tsira ba, domin saina sa an yanke maka hukuncin da zaka gwammace baka haife ni ba, dole a bi wa mtane haƙƙin su domin suma mutane ne kamar kowa, kuma suma suna da madu sonsu bawai babu. Kuma ka sani cewa muddin wani abu ya sami Amrah, ba zan rabu da kai ba". Ya ƙarashe maganar tare da fice wa daga cikin parlourn.
Murmushin mugunta Gov. Musa ya yi ya ce. "Umar kenen, ba zaka taɓa samu wata hujja a kaina ba".
*********************
"Safira ina son ki bani haÉ—in kai, bana son kiyi min gardama, maza yanzu ki biyo ni". Aliyu ya faÉ—a yana mai kallon Safira.
Banzan kallo Safira ta watsa masa sannan ta ce. "Idan kai ka isa da ni to ka sa na bika"
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke ya ce. "Okay tom idan baki je ta lallami ba za ki je ta dole". Ya faÉ—a tare da jan hannunta.
Wafce hannunta daga nasa Safira ke shirin yi amman akan ya cutura. Nan take ta fashe da kuka tana mai dukan bayansa tare da cizon hannunsa, amma hakan bai sa ya sake ta ba. Jefa ta ya yi a cikin mota sannan ya É—aure ta a jikin mota kana ya tada mota ya bar wajan.
*****************
Parking Sooraj ya yi tare da fitowa daga cikin mota. Nan ita ma Zahra ta fito daga cikin motan. Yayin da ta fara bin asibitin da kallo. "Kamar na taɓa zama a asibitin nan". Zahra ta faɗa cikin ranta.
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi sakamakon riƙe mata hannu da Sooraj ya yi. Nan take ta ji gabanta ya tsananta faɗuwa.
Murmushi Sooraj ya saki kana suka shiga daga ciki. Nan likitocin asibitin suka shiga kwasar gaisuwa.
Kai tsaye inda É—akin Mrs Laila yake suka je. Tare da shiga ciki.
Nan take Zahra ta haɗa ido da Mrs Laila. Take gabanta ya ƙara faduwa ƙarasa wa ciki ta yi tare da bin Mrs Laila da kallo.
Gaishe ta Zahra ta yi ta amsa yayin da suka shiga kallon juna.
Zahra kuwa tunani take a ina ta taɓa ganin matar nan. Sai a wannan lokaci ta tuna cewa tabbas a wannan asibitin ta taɓa ganin ta.
Kallon Zahra Sooraj ya yi ganin yadda ta nutsu ya sa shi sakin murmushi sannan ya ce. "Zahra kenen, to wannan ita ce mahaifiyar tawa da nake baki labari".
Shiru Zahra ta yi sannan daga baya ta ce. "Ina asali Æ´arki ko É—anki yake?".
Ta faÉ—a tana mai kallon mrs Laila . Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Ni ba wai Æ´a É—aya gare ni ba, yara uku ne, amma sai dai na rabu da su saboda na ceci rayuwarsu da tawa. A halin yanzu dai ban san ko suna raye ko sun mutu ba, amma ni yanzu fata na shi ne na gansu ko a karo na biyu ne kafin na bar duniyar nan ".
"Amma shin baki bawa kowa riƙo ba?". Cewar Zahra.
Amsa mrs Laila ta bata da cewa. "Mutane biyu na bawa riko, ɗaya kuma na ajiye ta a daji sakamakon lokacin ƴan sanda suna ta bibiyata, ban samu na tafi da ita ba, amma na saka mata suna Amrah, sannan ɗuk ƴaƴan nawa uku suna matuƙar kama da juna, sai dai kowanne da irin kalar ƙwayar idanuwansa. Amma kinga maƙiya na duk sun sa na rabu da su, duk dan saboda abin duniya ". Ta ƙarashe maganar hawaye na sauka kan ƙuncinta.
Tausayin matar ne ya kama Zahra. Sai a lokacin ita ma ta tuna da cewa bata da uwa. Share wa Mrs Laila hawayenta ta yi sannan ta ce.
"Kinga kamar yadda kika rasa Æ´aÆ´an ki, aka nima bani da uwa, ban sani ba ko ta mutu ko kuma tafiya ta yi ta barni, amma a kullum a jikina sai ina jin cewa wata rana zan ganta. Ina son ki É—auke ni a matsayin Æ´ar da ki ka haifa dan Allah".
Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Shi ke nen ƴata". Ta faɗa tana mai rungume Zahra jikinta. Lokaci ɗaya zuciyar ta ya buga da ƙarfi.
Kallon su Sooraj ya yi tare da taɓe baki sannan ya ce. "Ni kuma shi ne aka ware ni a gefe ko?, yanzu Mama shi ne kika share ni ko?".
Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Aba my son, to kaima tawo nan kaji É—an Mommy".
Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "A'a ba saina zo ba".
Saida suka taɓa hira kafin daga nan suka shirya domin su tafi.
Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta dubi Mrs Laila ta ce. "Tunda yanzu ke mamata ce, zan taimaka miki wajan neman sauran Æ´aÆ´anki saboda nima yanzu Æ´an uwa na ne".
Ta faɗa tana mai fice wa daga ɗakin. Kallon Mrs Laila Sooraj ya yi ya ce. "To mu dai zamu tafi, karki damu an kusan sallamar ki daga cikin wannan asibitin, sannan kuma zan cigaba da neman yaranki har sai inda ƙarfi na ya ƙare". Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin.
Nan ya tarar da Zahra a gefen motarsa ta tsaya tana share hawaye".
Mamaki ne ya kama Sooraj ganin karo na farko ya ga Zahra na hawaye. Dubanta ya yi ya ce.
"Dama akwai abinda zai iya saki kuka ban sani ba?".
Share hawayenta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj ka yafe min, na san na ɗan wahalar da kai kaɗan a gidan ku, amma yanzu na chanza in sha Allahu zan daina tsiwa sannan zan kasance mai haƙuri a kome za'a yi min, kaji idan ma hukunta ni za ka yi a kan rashin kunyar da na dinga yi maka zaka iya ɗauka".
Harara Sooraj ya yi mata ya ce. "Na yafe miki, amma ni na san ba za ki chanza ba, ko duka jikina ƙunne ne ba zan yarda za ki iya chanza wa ba".