Sashe 24
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dafe kansa Junaid ya yi ya ce. "Ni yanzu a ina zan samo maƙullin nan, kuma ina da tabbacin cewa yana wajan wannan ƴar dabar nan ta ɗazu, to a ina ma zan ganta?, kuma muƙullin nan yana da mahimmanci sosai, gashi mai martaba ba zai barni na fita daga masarautar nan ba. Yanzu ya zan yi kenen?". Ya tambayi kansa.
********
Æangaren Umar kuwa yana tsallaka wa ya sauko da Amrah daga kan bishiya yayin da ya ga fuskarta shaÉ“e-shaÉ“e da hawaye babu abin da take yi sai kuka.
Damuwa ne ya lulluɓe fuskar Umar. Kallonta ya yi ya ce. "Amrah me ya faru?, kina son ki koma wajan ƴan uwan kine?".
Babu tsanmani ya ga ta girgiza masa kai. Mamaki ne ya kama shi. Cike da farin ciki ya ce. "Kina iya fahimtar abin da nake cewa?".
GyaÉ—a kai ta kuma yi a karo na biyu.
Hamdala Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen naji dad'i tun da kina iya fahimtar abin da nake cewa. Yanzu dai kina so ne na kaiki wajan Æ´an uwan ki ko".
Gyaɗa masa kai ta yi. Tare da fara kalle-kalle. Nan ta hango ruwa wanda ya zuba a ƙasa.
Murmushi ta yi tare da wafce hannunta ta nufi in da ruwan yake.
Ganin hakan ya sa Umar bai yi ƙasa a gwiwa wajan bin bayanta ba.
Tana isa bakin ruwan datti da ya zuba a ƙasa ta tsugunna kan gwiwowinta tare da kokarin kai hannunta kan ruwan domin ta sha.
Ganin hakan ya sa Umar saurin dakatar da ita. Mikar da ita ya yi ya ce. "A'a Amrah karki damu in dai ƙishin ruwa ki ke ji zan siya miki ruwa ba saiki sha na datti ba, maza tawo mu je".
Ya faÉ—a tare da jan hannunta. Ba musu Amrah ta bi bayanshi yayin da babu abin da take ta faman yi illa kallon jama'ar da ke wajan tare da tufafin da ke sanye jikin su. Kallon jikinta ta yi ta ga dai ita nata tufafin da nasu da iri É—aya ba ne domin naya na ganye ne.
Binta jama'ar wajan kawai suke da kallo.
Wani ƙaramin super market Umar ya samu ya shiga da Amrah yayin da ya yi order ruwa. Cikin lokaci ƙalilan aka kawo masa ruwan roba. Karɓan ruwan Umar ya yi tare da buɗe murfin roban ruwan sannan ya miƙa wa Amrah.
Bin roban da kallo kawai Amrah ta yi tare da kawar da kanta.
Sauke ajiyan zuciya Umar ya yi sannan ya ce. "Ki karɓa ki sha ruwa ne fa, maza karɓi ki sha idan ya so muje na kaiki gidan mu ina da ƙanne za su kula da ke kinji".
Karɓar roban ruwan Amrah ta yi tana mai jujjuyawa a hannunta. Taɓe baki ta yi sannan ta fara kwararar da ruwan a ƙasa.
"Ya Salam". Umar ya furta yana mai dafe kansa. Karɓar ruwan ya yi sannan ya fara bata da kansa. Take ta shanye ruwan tasss.
Mamaki ne ya kama Umar ganin lokaci ƙalilan ta shanye ruwan roba ɗaya. Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. Tashi mu tafi ko.
Gaba É—aya mutanen super market É—in sai binsu Umar suke da kallo most especially Amrah wanda suka ga shigar ta sakk irin na Æ´an jeji.
Lura da Umar ya yi cewa mutanen wajan su suke kallo hakan ya sa shi miƙe wa tsaye sannan ya je ya bada kuɗin ruwan roban da ya siya. Tare da jan hannun Amrah suka fice daga wajan.
Tafiya suka fara yi yayin da Umar yake ta faman kallon Amrah. Wai shi ne yau tare da mace yana lallaɓa ta kamar ƙwai. Abun ba ƙaramin mamaki yake ba shi ba.
Ba zato ya ga Amrah ta ƙwace hannunta daga nasa ta fara gudu. Zaro ido Umar ya yi tare da saurin bin bayan ta.
"Amrah ina za ki je?, ki dakata, oh my God hanya ban É—aura ruwan dafa kaina ba kuwa ni Umar?".
Abin da ya sa Amrah gudu kuwa bakomai ba ne fa ce gani da ta yi wata mai ciki za ta tsallaka titi ga mota ya tawo sai faman sharara gudu yake.
Hakan ya ja hankulan mutane yayin da suka fara ihuuu taimako.
KaÉ—an ya rage mota ya buge matar da sauri Amrah ta sha gaban matan tare da matsar da ita gefe.
Nan take motan ya buge Amrah. Zaro ido jama'ar wajan da Umar suka yi.
Ga mamakin su kuwa sai gani suka yi ta tashi sama tare da sauka ƙasa ta tsaya chakk tamkar ba ita mota ya buge ba.
Sakin baki mutane suka yi ganin abun mamaki da ya faru a dai-dai lokacin.
Æangaren Umar kuwa abin ba Æ™aramin mamaki ya bashi ba ganin yadda mota ta kaÉ—e ta amma bata faÉ—i ba.
Saurin zuwa bakin titin Umar ya yi tare da jan hannun Amrah. Janyo ta ya yi har izuwa in da motar sa yake sannan ya tsaya ya dube ta ya ce. "Kina da hankali kuwa?, chan fa tsakiyar titi ne ba kamar dajin ku ba ne wanda za ki dinga tsalle kina shiga da fice yadda ranki yake so, yanzu da a ce wani abu ya same ki fa, kin san wane hali zan shiga". Ya ƙarasa maganar yana mai kallonta.
Lura da ya yi cewar gaba É—aya hankalin ta ba'a kansa yake ba yana wani wajan da ban ya sa shi faÉ—in. "To wai wannan ina take kallo?".
Ya faÉ—a yana mai bin in da take kallo da kallo. Mai mangwaro ya hango zaune a bakin junction.
Kallonta ya yi ya ce. "Shima mangwaron sha za ki yi?".
GyaÉ—a masa kai ta yi.
Takaici ne ya kama shi ya ce. "Ke yanzu komai ki ka gani za ki sha?, to ai yanzu dai bamua kusa da wajan saiki tawo mu tafi".
Ya faɗa tare da juyawa sannan ya buɗe mata ƙofar ƴan zaman banza. "Zo ki shiga". Ya faɗa hin shiru bata shiga ba ya sa shi juyawa.
Zaro idanuwa ya yi waje ya ce. "Ina kuma ta shiga?". Daga chan tsallake ya hango ta wajan mai mangwaro babu abin da take ta faman yi sai gwawuyan mangwaro kamar ta samu goruba.
Ɗora hannunsa biyu Umar ya yi a kai ya ce. "Ya Allah!". Tafiya ya fara yi tare da tsallaka wa bakin titin ganin ta sha mangwaro sun kai biyar hakan ya sa ya ciri kuɗi a aljihun shi ya biya mai mangwaron. Maida kallonsa ya yi kanta tareda fara janta. janta ya fara yi ya ga dai taƙi jawuwa. Ganin hakan ba zai finshe shi ba ya sa shi ɗaukarta chakk sannan ya nufi in da motar sa take.
Tafiya ya yi sosai kafin daga baya ya isa in da motar sa take sannan ya saka ta a cikin motan tare da saka wa ƙofar lock.
Koma wa ya yi mazaunin driver sannan ya tada motar suka bar harabar wajan.
A takure ta zauna a cikin motan yayin da iskan AC ya addabe ta. Hannu ta saka tana mai ƙoƙarin fasa glass ɗin motan domin ta shaƙi iskar waje.
Ganin tana ƙoƙarin fasa glass ya sa Umar saurin kashe Ac ɗin.
**********
"Yanzu dai munyi magana da Doctor ya ce kin samu sauƙi sosai zamu iya tafiya da ke".
Murmushi Safeera ta yi ta ce. "Na gode Daddy amma yanzu Airport zamu wuce ko?".
Amsa Daddy ya bata da cewa. "A'a dole sai mun je mun fara ganin su grandma da grandpa É—in ki tukun".
Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen, amma muna zuwa zamu koma America, saboda i can't stay here".
Fita suka yi gaba É—aya tare da shiga cikin motan taxin da ya É—auko su daga airport sannan suka fice daga harabar asibitin. Kai tsaye hanyar gidan Grandpa suka nufa.
Dai-dai junction suka tsaya sakamakon goslow da ya cike wajan.
Daga nesa Safeera ta hango mai mangwaro. Murmushi ta yi ta ce. "Laa Mom dama akwai Mango a Nigeria?, ina so zan sha please Mom".
Kallonta Mom ta yi ta ce. "A'a Safeera nan titi ne ki bari Aliyu zai zo ya siya miki daga baya".
"No Mom gaskiya ni ba zan iya jira ba". Tana kaiwa nan ta fice daga cikin motan tare da tsallaka wa ɗayan ɓangaren.
Ganin hakan ya sa Mom fita daga cikin motan sannan ta bita a baya.
Safeera na zuwa ta kalli mai mangwaron ta ce. "Hey you, I need one mango how much dollar is it?".
Ƙura mata idanu mai mangwaron ya yi yayin da mamaki ya bayyana kan fuskar shi.
Kallonta ya yi ya ce. "Bake ba ce yanzu ki ka sha mangwaro guda biyar da tufafin Æ´an daji?".
Ƙarasawa wajan Mom ta yi ta kalli Safeera ta ce. "Ki tawo mu tafi babu Nigeria money yanzu a waje na, they don't deal with dollar okay let's go".
Miƙa mai dollar ɗaya Safeera ta yi ta ce. "Take it I need one mango".
Kallon kuɗin mai mangwaro ya yi ya ce. "Ni za ki kawo wa kuɗi bogi. yanzu-yanzu da ki ka sha mangwaro kusan biyar amma a ce har kin dawo za ki ƙara".
Kallon mai mangwaron Mom ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Ƴata kuma?, hanya kuwa?, yanzu fa ta zo nan wajan".
Girgiza kai mai mangwaron ya yi ya ce. "A'a Hajiya, ɗa zu ƴarki ta zo sai dai ba wannan shigar ba ne a jikinta, ita ne da wani ya zo ya ɗauke ta a nan suka tafi. Nayi mamaki ne ganin lokaci ƙalilan harta chanza kaya ta kuma dawo wa sannan kuma idanuwanta naga ba kalar da ɗa su ba ne na ɗazu kamar kore ne idanuwanta".
Sai a lokacin Mom ta tuna da mai kama da Safeera da ta gani a Tv.
Kallon Safeera Mom ta yi ta ce. "Babu shakka magana ta gaskiya ce, kenen da gaske ne akwai mai kama da Safeera?, to wai ta ya ya hakan ta kasance?, kodai Safeera Æ´an biyu ne, kenen hakan yana nufin ajiya biyu ne su É—in?".
💃💃💃💃💃💃💃💃
*LIKE SHARE & COMMENTS FISABILULLAH 🤌ðŸ™*