Sashe 14
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zuwa ta buɗe murfin roban sannan ta watsa wa Aliyu ruwan a jiki. Nan take Aliyu ya buɗe idanuwansa tare da dafa kujera domin ya miƙe tsaye. Taimaka masa Dad ya yo ya miƙe sannan ya zauna a kan kujerar three seater.
Kallon shi Dad ya yo sannan ya ce. "Aliyu me ya tsorata ka game da Safeera?, shin blue eyes É—in ta ne ya tsoratar da kai ko kuwa?".
Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya fara kalle-kalle. Zumbur ya miƙe tsaye yana mai fuskantar su. "Ta ya ya na zo nan wajan?, wace ce kuma Safeera".
Sakin baki gaba ɗaya suka yi suna kallonsa. Cike da mamaki Dad ya kalle sa ya ce. "Kana nufin baka san yadda ka zo nan ƙasar ba?".
Amsa Aliyu ya ba shi da cewa. "Ƙwarai ban sani ba, ni dai na san zan shiga cikin magarƙama ne amma ban san ta yadda na zo nan wajan ba, ya kamata na tafi domin ina da hayyuka a gaba na".
Jikin Dad ne ya yi sanyi. Ji ya yi kamar ya kurma ihuu saboda takaici. Cikin ransa ya ce. "Tabbas akwai matsala babba, ta ya ya zan aura wa Æ´ata wanda yake da cutar mantau?, tun da yanzu ya ce bai san ta ba, wata ran idan sun yi aure ma haka zai ce ba matarsa bace. Shi ke nen tun da ya manta ba zan aura masa ita ba, zan barta kawai ta ci gaba da karatun ta a Nigeria".
Dawo wa ya yi daga duniyar zancen zucin da ya shiga, sannan ya dubi Safeera ya ce. "Kada ki damu Æ´ata, ba zan yi miki aure yanzu ba kunji".
Murmushi Safeera ta yi tare da gyaÉ—a kai sannan ta shige cikin É—akin ta.
Maida kallonsa Dad ya yi kan Aliyu sannan ya ce ya shi ke nen Aliyu za ka iya tafiya. Amma me zai hana ka bari zuwa next week muma zamu koma Nigeria da zama saboda anyi min transfer É—in wajan aiki. Kaga sai mu koma tare, koya ka gani?".
"Shi ke nen". Kawai Aliyu ya furta. Ɗaukar jakar Aliyu Mom ta yi sannan ta yi masa rakiya izuwa ɗakin baƙi.
Safeera na shiga ɗaki kuwa, ta buga tsalle yayin da ta fara murna cewa Daddyn ta ba zai yi mata aure ba. "Shi ke nen yanzu ba bu ni ba bu auren wancan mutumin. Wayyo daɗi kashe ni, zan ci gaba da zuwa makaranta, daga ƙarshe na zama babban Barrister ko lawyer. Sai dai a ji a cikin kotu hana cewa. "Barrister Safeera can you come forward please. Nima daga nan na tashi domin kare wanda haka cuta sannan na tsaya tsayi daka domin ƙwatar wa mutane haƙƙinsu. Wow abin ya burgeni, daga ƙarshe dai zan zama Barrister". Safeera ta faɗa tana mai tiƙan rawa a cikin ɗakin.
*NIGERIA CIKIN MAGARƘAMA*
Zama Zahra ta yi a É—akin tana mai fuskantar Hajiya Binta. Girgiza kai Hajiya Binta ta yi sannan ta ce.
"Wai me ya sa ki ke da zafin zuciya ne Zahra?, ba daman mutum ya yi miki wasa shi ke nen za ki É—auki zafi".
Turo baki gaba Zahra ta yi sannan ta ce. "Zan iya wasa da komai amma banda mahaifiyata, a kan me ya sa zai zage ta?, dan yana matsayin ɗan sanda shi ne haka ce ba zai san bambancin dai-dai da kuma ba dai-dai ba?, wallahi da a ce baki zo ba ɗazun nan Allah da saina koya masa hankali. Ni da so samu ne Allah na bar cikin magarƙamar nan domin na gaji da zaman cikin ta, ba bu wani freedom sosai, daga aiki sai wasa sai a zo a bawa mutum abinci wanda ko akuya ta ci ba lallai ta ji daɗinsa ba". Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora idonta a kan wani babban littafi.
Ajiyan zuciya hajiya Binta ta sauke sannan ta ce. "Ai idan har na sake na barki ki ka fita daga cikin magarƙamar nan to sai dai ba bu rai a jiki na, domin kuwa rayuwar ki yana cikin hatsari. Ba bu wanda ya san da cewa kina raye, da a ce sun san da cewa kina raye da tunan an sace ki domin ki je ki dangwala hannu a kan wasu dukiyoyi wanda yawan su ba zai misaltu ba. Yanzu dai ba lokacin wannan magana bane, ki tashi ki fita wata warder ta ce tana nemanki".
Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen Aunty bara naje". Ta faÉ—a tare da fice wa daga cikin É—akin.
******************
"Hello yallaɓai, yanzu nan nake jin labarin cewa ɗan ka Umar ya sauka a Nigeria".
Zumbur mutumin ya miƙe daga kan kujeran da yake, sannan ya ce. What!, kana nufin Umar ya shigo Nigeria?, me ya sa ku ka bari ya sauka a Nigeria bayan na faɗa muku cewa rayuwarsa tana cikin hatsari. Ɗazun nan muka gama waya da shi ya ce min wai sai next week zsi dawo Nigeria. Ta ya ya kuma yanzu za'a ce min wai ya shigo Nigeria?. Yanzu haka gurɓatattun ƴan sanda da ƴan daba neman sa suke ruwa a jallo. Saboda ya kama ɗaya daga cikin babban mai laifi wanda gaba ki ɗaya ƙasa ke nema, kuma sannan ya ƙwace ƴan mata wanda hake ƙoƙarin yin safaransu a ƙasashen waje, sannan ya yi siezing ɗin miyagun ƙwayoyin da hake shigo da su shi da abokin sa wanda yake aikin custom. Yanzu dai abin da nake so da kai shi ne, na san da cewa yana da jami'ai securities wanda ke ba shi kariya. Ina son ka tara jamiai ku dinga binsu a baya har sai sun iso gidan nan lafiya".
"Shi ke ne". Jami'in ya faÉ—a, daga bisani ya kashe wayar.
Tafiya motar su Umar suke a kan titin layin ɗan masara. Chan na hangi wani katafaren gida mai matuƙar kyau da tsaruwa. Tabbas kuɗaɗen sun yi kuka wajan gina wannan katafaren gidan.
horn jami'an suka yi. A take masu gadi suka fara buÉ—e gate . wayyo Allah wanan gidan shi hake kira aljannar duniya .
inda hake parking motoci suka nufa tare da yin parking. Kashe motocin suka yi, gba ɗaya motoci ne ya zagaye gidan kai kace wajan saida motoci ne saboda yawa. gaba ɗaya gidan zagaye yake da sojoji, inda gefe ɗaya kuma flag of nigeria ne a sama. dakuma flag na jami'ai. gaba ɗaya jami'an gidan riƙe suke da bidigogi
chan nesa kuma baban gida ne da alama É—akin karnuka ne wato police dogs
daga gefe kuma swimming pool ne babba mai matuƙar faɗi da girma. chan gefe kuma ɗakin lantarki ne da kuma ɗakin gana wa masu laifi azaba.
cctv cameras ne kewaye a gaba ki É—aya gidan. gidan babba ne yadda ka san gidan shugaban kasa saboda yadda ya zagaye da sojoji. Idan na ce zan tsaya gaya muku yadda gidan nan ya haÉ—u sai na gama page É—in nan ina bayyana irin kyau da gidan yake da shi.
Kai tsaye cikin labari.
wasu maza uku ne sanye da kakin soja suka nufo inda suke, ɗaya daga cikin su ne ya bude side ɗin Umar tare da buɗe masa ƙofar mota sannan ya sara masa.
ÆŠaga mai hannu Umar ya yi da ya dakatar da sarawan. Fitowa ya yi daga cikin motan tare da shige wa cikin gidan. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da parlourn gidan. Gaba É—aya kayan furnitures É—in gold ne.
Biyo shi securities suka yi da box É—in shi.
Juyawa ya yi tare da kallonsu sannan ya ce. "Ku ajiye Æ´an aiki za su zo su É—auka". Ajiye wa suka yi tare da fice wa daga parlourn.
Fitowa gaba ki É—aya family gidan suka yi tare da yi mishi barka da zuwa. ÆŠaga musu hannu kawai ya yi daga bisani ya shige part É—in shi. Baki sake suke binshi da kallo.
Wata budurwa ce sanye da atamfa riga da siket ce ta dubi sauran ƴan uwan nata sannan ta ce. "Wai me ya sa yahya Umar yake haka ne?, kwata-kwata shi bashi da wata farha?, ya kamata a ce Abba ya yi masa magana, mu fa ƙannensa ne ba maƙiya ba". Ta ƙarashe maganar damuwa bayyane a kan fuskarta.
Ɗaya daga cikin su huɗun ne ya dube ta ya ce. "Khairiya kin san dai ba yau ne ya fara ba, tun da mahaifiyarsa ta yi hatsarin mota ts rasu shi ke nen ya chanza a gidan nan, walwala da kuma dariya shi ya guje. Abba ma bai ƙyale shi ba balle mu. Kunga ku tawo mu bar nan kafin ya fito ya tarar da mu".
Kallonsa khairiya ta yi sannan ta ce. "Allah ya bayyana wanda zata sauya Yahya Umar ya dawo yadda yake a da".
"Ameen thumma Ameen". Gaba É—aya suka furta.
Bayan Umar ya shiga ɗakin ya shiga toilet tare da watsa ruwa. Fitowa ya yi tare da nufar ɗakin Abba, sallama riƙe a bakin shi ya shiga cikin ɗakin.
**************************
*HOSPITAL*.
Zaune take a kan kujera yayin da ta zurfafa cikin tunani, ta rasa me ke mata daɗi. Dafa ta ɗaya daga cikin nurse's ɗin ta yi ta ce. "Nurse Nadiya wai me yake damunki?, tun a kwanakin baya na fahimci cewa kina cikin damuwa, kuma a wasu lokutan idan naga kin idar sallah ina yawan ganin kina kuka kina haɗa hannayen ki guri ɗaya, kuma ni hakan ba ƙaramin kasalar min da jiki yake ba. Ya kamata a ce ki fauwala wa Allah komai Allah shi ne mai jiƙan bayinsa". Cewar nurse ɗin.
Share hawayen dake gangaro mata nurse Nadiya ta yi sannan ta dubi nurse ɗin ta ce. "Ba za ki taɓa fahimta ta ba nurse, koda a ce zan faɗa miki abin da ke ci min tuwo a ƙwarya ba za ki gane ba. Ina cikin halin tsaka mai wuya, na ɗauki alƙawari kuma ban cika ba. Ban san me zan yi ba, gaba ɗaya na ji duniyar ma ta ishe ni, ji nake kamar na mutu na huta". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.