Sashe 41
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taɓe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "To Allah ya bar soyayya".
Amsa wa Aliyu ya yi da "Ameen".
"Shi ke nen, ni zan tafi, zanje in siyo abu ne a wannan kasuwan kada na daɗe kuma wan can yariman ya zo ya fara balbale ni da masifa, ni bai san ma ɗaga mai ƙafa kawai nake ba".
Zahra ta faɗa tana mai ƙoƙarin tafiya.
Saurin dakatar da ita Aliyu ya yi sannan ya ce. "A'a karki tafi bari nayi miki rakiya, ai yanzu mum zama abokai ko, don haka duk abin da ki ka siya ni nan zan riƙe".
Dariya Zahra ta yi ta ce. "Kai kuwa ka san me zan siyo?, ba za ka iya riƙe wa ba, idan na ce zan baka duk abin da zan siya sai dai ma na saka kuka domin ba za ka iya ba, kawai dai kayi tafiyarka".
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai, ni fa ba ragon namiji ba ne, ni jarumin jarumai ne, kedai kawai ki bari muje tare zan baki mamaki".
Murmushin mugunta Zahra ta yi ta ce. "Tom shi ke nen malam É—an sanda muje, ni ba zan ana ka ba".
Ta faÉ—a tana mai tafiya. Saurin bin bayanta Aliyu ya yi tare da farin cikin ya samu shiga jikin Zahra saura kuma yadda zai yi ya sace ta.
_________________________
Su Umar ba su suka iso Kano ba sai wajan la'asar. Yayin da kai tsaye suka wuce gidan zoo.
Bai É—auke su lokaci ba suka isa gidan zoo dai-dai lokacin da ake kiran sallah.
Parking gaba ɗaya suka yi yayin da suka fito daga cikin motocin. Kallonsu Ramlat da Usman Umar ya yi ganin hankalin Amrah yana wani wajan da ban, ya sashi faɗin. "Na san ba za'a rasa wasu namun jeji a nan ba, kuje ku kaita ta gansu na san koba komai dai za ta ɗauka ƴan uwanta ne. Kai kuma". Ya faɗa yana mai kallon Usman, "maza biyo ni muje muyi Sallah a masallaci". Ya ƙarashe maganar yana mai yin gaba.
Bin bayansa Usman ya yi suka wuce masjid domin gabatar da Sallah.
Maida kallonsu su Khairiya suka yi kan Amrah sannan suka riƙe hannayenta suka fara shiga ɓangaren dabbobi da ita. Gani suka yi gaba ɗaya dabbobin sun ragu babu wasu dabbobi chan sosai.
Daga nesa Amrah ta hango wasu birurruka cikin zagaye. Da sauri ta wafce hannunta tare da nufar wajan da mugun gudu, a sa'inda jama'ar wajan gaba É—aya suka bita da kallo.
Da sauri su Khairiya suka bi bayanta a matuƙar tsorace.
Ƙarasa wa wajan Amrah ta yi tana mai aye wa kan ragar birurrukan. Da sauri su Khairiya suka je tare da kokarin saukar da ita. Saukar da ita suka yi. Sannan suka fara kwantar mata da hankali.
Shiru Amrah ta yi sannan ta ƙura wa birurrukan idanuwa. Girgiza kai ta fara yi tana mai ja da baya, tana mai faɗin. "A'a, waɗan nan samm ba su ba ne". Saurin maida kanta ta yi kansu ta ce. "Ina ku ka kai su?, kun kashe su ko?, me ya sa ku ka yi min ƙarya?".
Ta faÉ—a tana mai fashe wa da kuka.
Kallon juna Ramlat da Khairiya suka yi yayin da bakinsu ya kasa furta komai.
Share hawayenta Amrah ta yi jin kukan yaro ƙarami wanda ya karaɗe wajan. Saurin waiga wa ta yi domin jiyo ta idda wannan kukan ke fitowa. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani yaro a ƙasa sai faman kuka yake.
Da sauri Amrah ta isa idda yaron yake sannan ta É—auke shi tare da sakin murmushi ta ce. "Daina kuka yaro za ka yi wasa?, bara muyi wasa ko". Ta faÉ—a tana mai cilla yaron sama.
Take mutane suka saki ihuu ganin yadda ta jefa yaro chan sama sosai.
Da sauri su Khairiya suka dube ta suka ce. "Ke Amrah kinyi hauka ne?, maza ki sauke wannan yaron".
Ko kula su Amrah ba ta yi ba, saima cigaba wa da ta yi. Nan ta ci gaba da jefa yaron sama yana ihuu yana kururuwa. A sa'inda jiri ya É—ebi yaron ya suma.
Bayan ya dawo hannunta ne ta ga yaron ya yi shiru. Murmushi ta yi ta ce. "Kun gani ko, yaron ma har ya yi bacci abunsa hankali kwance".
Dafe kanta Ramlat ta yi ta ce. "Mun shiga uku, Amrah me ki ka aikata aka?, kin fa sumar da shi".
Dai-dai lokacin da wata mata take ƙaraso wa wajan hannunta riƙe da leda alamun ita ce mahaifiyar wannan yaron.
"Me yake faruwa ne na ga mutane sun taru a nan wajan?, ina É—ana yake?". Ta faÉ—a a yayin da idanuwanta suka sauka kan yaronta da ke hannun Amrah.
Ɗora hannayenta ta yi a kai tana mai fasa ihuu!. "Innalilahi wa innahilahir rajihun!, me ku ka aikata wa ɗana, me ya faru da shi. Wallahi idan wani abu ya samu ɗana ba zan ƙyale kowa ba". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin wafce ɗanta a hannun Amrah.
Nan take Amrah ta riƙe hannun matar ta ce. "Ba zan baki shi ba har sai ya farfaɗo".
Wafce hannunta matar ta yi daga na Amrah sannan ta ce. "To maza farfaÉ—o da shi".
Kwantar da shi Amrah ta yi sannan ta hura mai iskar bakinta kan fuskarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci yaron ya farfaɗo. Nan take mutane suka fara mamaki. "Dama iskar baki na iya farfaɗo da wanda ya suma?, kodai ita ɗin ba mutum ba ce, don yadda ƙwayar idanunta suke green ma za ka tabbatar da cewa wannan ba mutum bace?". Abin da suka shiga furta wa kenen.
ÆŠaukar É—anta matar ta yi cikin farin ciki sannan ta juya tare da barin wajan ba tare da ta yi wa Amrah godiya ba.
MK da ke zaune cikin mota duk abin da ya faru a gaban idanuwansa. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ya yi ya ce. "Da a ce a wajan iyayenku ku uku ku ka taso da rayuwarku ba ta kasance haka ba, amma haka Allah ya riga ya kaddara cewar ba za ku taso da mahaifiyar ku ba. Ina fatan duk in da mrs Laila take ya kasance tana ƙoshin lafiya, har izuwa yanzu ban sani ba ko tana raye ko kuma ta riga mu zuwa gidan gaskiya. Amma ina fatan duk in da take ya kasance tana cikin rahamar ubangiji".
Ya faÉ—a yana mai tada mota sannan ya bar harabar wajan.
___________
"Hello your Excellency yanzu haka muna cikin gidan zoo É—in, umarnin ka kawai muke jira".
Daga ɗayan ɓangaren gov. Musa ya ce. "Perfect, ni na san Aliyu ba zai iya wannan aikin shi ɗaya ba shi ya sa na tura ku chan. Ina son ku sace Amrah kai tsaye ku wuce da ita hanyar Airport ku wuce ƙasar waje domin a sata a kasuwa. Amma fa ku tabbata Umar bai ganku ba sannan ku rufe fuskokin ku kada ku kuskure ku buɗe".
"Shi ke nen yallaɓai kamar yadda ka ce". Mutumin ya faɗa yana mai kashe wayar. Nan take su biyar da ke cikin mota suka kalli juna a yayin da lokaci ɗaya gaba ɗaya suka rufe fuskokinsu da mask. Sannan suka fito daga cikin mota.
Kai tsaye in da Amrah ke tsaye suka nufa wacce ke ta faman kallon dabbobin cikin wajan.
Suna isa wajan suka rirriƙe hannunta tare da ƙoƙarin tafiya da ita. Nan take hankulan mutane da nasu Ramlat ya karkata izuwa kansu.
Dai-dai lokacin da su Umar ke ƙarasowa wajan.
Ganin abin da ke faruwa ya sa Umar ya yi saurin nufar wajan tare da ƙoƙarin ƙwace Amrah daga gare su. Gani Umar na shirin dakatar da su ya sa ɗaya daga cikin su ya kai mishi naushi a ciki. Faɗuwa Umar ya yi a matuƙar zafafe ya miƙe tare da yin kansu sannan ya fara kokawa da su. Nan take mutane suka fara ɗaukar video ganin yadda ɗan gidan govnor musa yake faɗa da ƴan ta'adda.
Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin su ya kai masa naushi cikin sa a karo na biyu. Faɗuwa Umar ya yi yana mai sakin ƙara.
Zaro idanuwa waje su Ramlat suka yi a matuƙar tsora ce suka nufo kan ɗan uwansu.
Ganin abin da suka aikata Umar hakan ya sanya ran Amrah ya fara tafarfasa yayin da ta saki wata iriyar razananniyar ƙara mai matukar firgitarwa.
Ba ta yi wata-wata ba ta shaƙe wuyan mutane biyu daga cikin su tare da ɗaga su sama sannan ta naka su da ƙasa. Ganin hakan ya sa sauran ukun suka yi saurin ja da baya.
Da sauri É—aya daga cikin ya É—auki sanda sannan ya buga wa Amrah.
_________________
"Mom!!!!!". Safira ta faɗa da mugun ƙarfi tana mai dafe kanta. Da sauri su Mom da ke zaune a parlour suka fito garden in da Safira ke zaune.
Dubanta Mom ta yi ta ce. "Mene ne ya fara ki ka saki uban wann ƙarar haka?".,
Rintse idanuwanta Safira ta yi ta ce. "Mom ina ji wani iri a jiki na, gaba É—aya bana jin daÉ—in jiki na, ina ji kamar wani abu mara kyau na shirin faruwa da ni".
Zama kusada ita Grandma ta yi ta ce. "Kiyi addu'a kinji ƴata, in sha Allahu komai zai zo miki da sauƙi, babu abin da zai faru sai alkhairy".
Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "A'a Grandma gaba É—aya jiki na ciwo yake yi, ba zan iya jure wa ba, jiki na yana min ciwo kamar wacce ta yi dambe da mutane".
"Tashi zo mu shiga ciki na É—ora miki ruwan zafi ki gasa jikin ki". Cewar Grandma. Tashi tsaye Safira ta yi cikin jin ciwo sannan ta bi su Grandma suka shiga cikin gida".
Nan dai Grandma ta ɗora mata ruwan zafi sannan ta fara gasa mata jikin ta. Cikin mamakin su kuwa abun sai ƙara tsamari yake, a maimakon ya ragu saima ƙaruwa da ya yi. Gani hakan ya sa hankulan gaba ɗayansu ya tashi.
"Wai Safira me yake faruwa da ke ne haka?". Cewar Daddy.