← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 59

Sashe 59

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Chan cikin dajin suka isa. Tsayar da motar suka yi tare da fitowa. Sannan suka fito da Zahra da Sooraj kana suka É—aÉ—É—aure su jikin bishiya sannan suka nufi inda su Amrah suke domin fito da su.

Dai-dai lokacin shima Mk ya ƙaraso wajan. Da sauri ya nufi inda su Sooraj suke sannan ya bashi inhaler ya shaƙa.

Dubansa Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah ka kunce mu".

"Shiiiiii!". Mk ya yi mata alama da hannu da ta yi shiru.

A hankali Mk ya fara kunce su yana mai waige-waige.

******************
"Wai ni kamm Yahya Usman ina su Amrah da Yahya Umar suke?, har yanzu shiru basu dawo gida ba, ni fa ina tsoron kada wani abu na cutarwa ya cutar ds su.
Cewar Khairiya.

Kallonta Usman wanda ke zaune kan 3seater ya yi ya ce. "Babu abinda zai same su, insha Allah suna cikin ƙoshin lafiya, ni na matsu su dawo mu koma jigawa".

Kallon su Ramlat ta yi ta ce. Ni fa ina ganin kamar akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba, tabbas akwai wani abu da Yahya ke ɓoye mana, kuma baya son mu sani".

Kallonta Usman ya yi ya ce. "Mene ne to Yahya zai ɓoye mana?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Jiya na kira Abbah, munyi waya to a lokaci da muka gama wayar ya manta bai kashe wayar ba, naji yana yin magana da wani bansani ba ko mace ce ko namiji, naji yana cewa ya tabbatar su Yahya basu tsira daga gare shi ba, sannan a tabbatar an tafi da Amrah Lagos daga nan a wuce da ita ƙasar waje. Na kasa gane me ke faruwa".

Kallonta Usman ya yi ya ce.
"Kina nufin Abba ya sace su Amrah?".

Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa tabbas ya sace su. Kenen dama Abba ba mutumin kirki bane?"

*********

Ɓangaren su Umar kuwa su kidnappers ɗin na zuwa suka ga babu kowa a wajan in banda Amrah da kuma Umar. Ɗaga bindigar su suka yi kan Umar sannan suka ce. "Ina sauran mutanen suke".

Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Mun kunce su, sun gudu".

"Zaku ga abinda za mu yi muku maza ku fita".
Cewar É—aya daga cikin kidnappers É—in.

Da sauri Umar ya riƙe hannun Amrah sa'anan suka fita waje.

Bayan Mk ya gama kunce su Zahra. Sooraj ya riƙe hannun Zahra suka fara gudu suna nufar inda kangon yake.

Dai-dai lokacin da su Amrah ke fitowa daga wajan.

Take Amrah ta buge Zahra cikin rashin sani. Da sauri Zahra ta juya domin ganin waye.

Dai-dai lokacin suka haÉ—a ido da Amrah.

Chakkk Zahra ta dakata yayin da gaban kowanensu ya buga da mugun ƙarfi. Zaro idanuwa waje Umar da Sooraj suka yi.

Sakin baki Zahra ta yi tare da shafa fuskantar. Kallonta Amrah ta yi domin ganin mai kama da ita sakkk.

"Me nake gani haka?, wayyo Allah babu maraba dani da ita". Cewar Zahra wacce ta ƙura wa Amrah kallo. Yayin da itama Amrah abinda take yi kenen.

"I can't believe this". Cewar Sooraj.

"Wayyo Allah shin gamo nayi ko kuwa". Amrah ta faÉ—a cikin zuciyarta.

"Babu maraba tsakaninsu, abinda ya bambanta su shi ne ƙwayar idanuwa". Cewar Umar wanda ya saki baki yana kallo.

******
Riƙe hannun Safira Aliyu ya yi sannan ya fita da ita.

Zagayawa suka yi daidai inda su Zahra suke.

Cikin rashin sa'a ƙafar Safira ya buge itace. Hakan ya sa ta sakin ƙara!.

Waigawa gaba É—aya suka yi nan take idanuwansu ya sauka kan Safira. Yayin da ita ma Safira nats idanuwa suka sauka kan su Zahra.

Nan take gabanta ya faɗi!, yayin da wata iriyar razananniyar ƙara! .

ÆŠora hannu Zahra ta yi a kai ya ce. "Na shiga uku wai masu kama dani É—in har guda nawa ne?, shin mafarki nake yi ko kuwa".

Nan Zahra, Safira da Amrah suka haÉ—a baki wajan faÉ—in.

"muÉ—in su waye?".

Jiri ne ya fara ɗiban su ukun. Nan take kowacce a cikin su ta faɗi ƙasa sumammiya.

Ba tsammani su Umar suka ga an fara wani irin iska mai haÉ—e da guguwa wacce karaÉ—e ilahirin dajin baki É—aya.

WASA FARIN GIRKI🤸‍♀️💃💃💃🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️

END OF BOOK 📚 1

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
ZINARIYAR JAJIRTATTU
Chapter 59 · 0% Book details