← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 59

Sashe 3

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ɓacin rai Hajiya Binta ta kalleta ta ce. "Wato ta mutu a gaban idanuwan mu kenen koh? kotun banza kotun wofi na bi kotu da gudu ba wando. Idan ta rasa rayuwarta ba tare da haifar abin da ke cikin ta bah shin kun san da cewa babban laifi ne? Saboda kuna ji kuna gani tana buƙatar agaji ku ka ƙi agaza mata sannan kuma wallahi idan ta mutu sai kin fuskanci mummunar uƙuba tare da hukunci dan haka kuje a haɗa jami'ai a tafi da ita asibiti. Maza-maza yanzun nan".

Cikin ƙanƙanin lokaci warders suka tara jami'ai yayin da haka ɗauki Mrs Lailah Abdullahi haka shigar da ita cikin mota. Riƙe hannun Hajiya Binta Lailah ta yi sannan ta ce. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ta ke. Tana kaiwa nan ta saki hannunta alamun ta suma.

Jikin Hajiya Binta ne ya yi sanyi yayin da ta kalli jaririyar dake hannunta cikin tausayawa.

Tada mota jami'ai suka yi yayin da suka fita da ita daga cikin magarƙamar tare da nufa da ita babban asibiti.

Tun da suka shiga cikin asibitin mutane ke binsu da kallo yayin da suke ganin kamar Mrs Lailah ce a cikin motar. Nan da nan labari ya zagaye gari cewar Mrs Lailah Abdullahi tana cikin international hospital zata haihu yayin da Æ´an jarida suka cika wajan domin É—aukar rahoto da bayanai.

Bangare guda kuma Jami'ai sun zagaye asibitin hannunsu riƙe da bindigogi.

Fitowa Nurse's suka yi da gadon ɗaukar mara lafiya sannan suka ɗora ta a kai tare da shigar da ita labour room tare da shirya ƙwararrun likitoci domin karɓar haihuwa.

Nan likitoci suka shiga cikin labour room ɗin da haka ajiye ta sannan suka fara gudanar da aikinsu. Yayin da suka canza mata kayan dake jikinta suka saka mata na marasa lafiya. Sannan suka saka mata ƙarin ruwa. Su kuma suka saka hand glove da facemark tare da wular kai. Ganin sai naƙuda ta ke ta kasa haihuwa ya sa suka yi scanning ɗin cikin ta. Nan suka gano cewar ba guda ɗaya bane ke cikin ta yara biyu ne.

Ganin hakan ya sa ɗaya daga cikin doctor's ɗin faɗin ba za ta iya haihuwa da kanta bah dole ne a yi mata operation idan har muna son ceton ranta da kuma ƴaƴan dake cikin cikinta. a halin yanzu jininta ya zuba sosai dole muna buƙatar wanda zai yi donating ɗin jini domin a ƙara mata don kada ta rasa rayuwarta. Dan haka dole mu muyi mata operation to save her life.
Cewar wannan likitan.

Jin hakan ya sa suka kwaso kayan aiki yayin da haka canza mata position tare da direction na haihuwan. Sannan suka yi mata allurar kashe zafi da raÉ—aÉ—i. Sannan daga bisani suka yi mata allurar bacci.

Ganin bacci ya ɗebe ta ya sa suka fara gudanar da aikinsu. cikin ƙware wa suka tsaga cikin ta tare da fiddo yaran ciki.

🌎🪐🌎🌎🪐🌎🪐🪐
*mafarin kenen. Koh ya zata kasance gaba? Ta ya ya kowanen suka kasance a ɓangare daban-daban? Shin kuma da gaske Mrs Lailah Abdullahi safaran yara ta ke tare da miyagun laifuka? Domin jin amsoshin tambayoyin ku, ku kasance tare da ni domin jin yadda zata kaya*💃💃💃

*Yawan comments yawan post ina son na ga ruwan comments*🥳👌 🥳

*kuma wannan littafin zai dinga zuwar muku ne da zarar ina ganin comments 💃🥳da likes*

DON'T FORGET TO COMMENT AND SHARE PLEASE 🙏 🙏 🙏

ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣➡️4️⃣
*___________________________________________* kukan jariran ne ya kauraye gaba ki É—aya cikin room É—in. Hamdala likitocin suka yi ganin sun yi nasaran ceton yaran da kuma mahaifiyar su.

Nan ta ke daya daga cikin likitocin ya ɗauki ɗaya daga cikin jariran, yayin da bayan hannunsa ya kasance a kan bangon mahaifa wato ji ga gefen mahaifa. Sa'an nan kuma tare da yatsun hannunsa sannan ya miƙa hannunsa baya da gaba don raba mahaifa ya fara yi a hankali daga bangon mahaifa kadan-kadan, bai dakata bah har sai da ya ga mahaifar ta cire.

Ajiye jaririyar ya yi sannan ya É—auki É—ayar jaririyar ya cire mata mahaifa kamar yacce ya yi wa ta farko.

ÆŠaukar towel suka yi sannan suka saka su a ciki yayin da suka ajiye su a kusa da Mrs Lailah. Kallon jariran likitocin suka shiga yi ganin yadda Ubangiji ya yi musu baiwa ta halitta, juyawa suka yi tare da ficewa daga cikin room É—in suka bar iya Mrs Lailah Abdullahi da jariran.

A hankali ta fara buɗe idanuwanta tana lumshe su yayin da ta ji dukkan gaɓoɓin jikinta nayi mata ciwo. Miƙe wa ta yi zaune tare da maida kallonta kan jariran. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta yi tare da rintse idanuwanta jin yadda maranta ke yi mata mugun ciwo.

Ɗaukar jariran ta yi tareda ƙura musu ido. Zaro idanuwa waje ta yi ganin kowacce da kalar idanuwanta ɗaya blue eyes, sannan kuma ɗaya green eyes. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bata bah.

Rungume su ta yi a kirjinta ganin yadda suke ta faman kuka. Waige-waige ta fara yi ganin ba bu kowa a ɗakin ya sa ta ajiye jariran sannan ta miƙe tsaye a hankali. Tafiya ta fara yi a daddafe harta isa gaban ƙofar ɗakin.

Leƙawa waje ta yi ta jikin ƙofar. Nan ta ga jami'ai a tsatsaye tare da warders gaba ɗaya sun zagaye wajan. Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zarya bisa ƙuncin ta.

Koma wa ta yi ta zauna tare da ci-gaba da rusa kuka cikin shesheƙar kuka ta ce. "Mene ne na aikata dana cancanci irin wannan sakayyar? shin wane zunubi ne na aikata? me ya sa haka zata kasance dani?".

"Mutanen da na taimaka da hannuna na ciyar da su sannan na basu abubuwa na more rayuwa. Ina tunanin koda na shiga wata matsala nsn gaba zasu tsaya mun saboda abubuwam alkhairy dana dinga aikata musu. Sai kuma gashi yau da kansu suka juya min baya saboda abin duniya suka butulce yayin da idanuwansu ya rufe suka kasa gane gaskiya. Wannan wace iriyar zamani ce wanda ba bu yarda kwata-kwata s cikinta saima cin amana da yaudara".

"Ban yi tunanin zasu iya cin amana ta har haka bah, amma ba komai Allah shi ne abun dogaro sannan shi ne mai warware kowace matsala, ina da yaƙinin cewa nan gaba sai gaskiya ta yi halinta".

Ta faɗa tare da maida kallonta jikinta ta ga faba ɗaya ta ɓata gadon saboda ba ƙaramin bleeding take yi bah.

*"Yauwa Nurse Nadiya ina son ki É—auki ruwan zafi ki kai room 8 akwai patient É—in mu a ciki sannan kuma kiyi wa yaran wanka. Ga tea nan mai zafi a flask wanda haka kawo mata ki kai mata tasha, sannan kuma ki bata maganin relief tasha". Cewar Doctor É—in.

"Shi kenen sir in sha Allahu zan yi kamar yadda ka faÉ—a". Ta faÉ—a tare da kwashe kayan ta zuba su a troley sannan ta É—auki towel mai kyau tare da tissue da allura sai maternity pad da kuma bedsheet. Tana gama haÉ—a wa waje É—aya ta nufi room É—in da su.

Sai da taje har gaban room É—in zata shiga. Nan ta ke É—aya daga cikin jami'an mata ta dakatar da ita yayin da ta yi amfani da portable scanner ta fara scanning É—in jikin nurse É—in gudun kada ta kasance tana tare da abun cutarwa.

Ganin dai ba bu komai ya sa ta bata hanya nurse Nadiya ta shiga cikin room É—in. Ajiye troley É—in ta yi a gefe sannan ta shiga toilet tare da haÉ—a ruwan zafi a cikin babban baff. Fitowa ta yi tare da nufa wajan mrs Laila wanda ke zaune kan patient bed. kallon Mrs Lailah nurse Nadiya ta yi ta ce.

"Na gama haɗa ruwan ki zo ki ɗan gasa jikin ki sannan ki saka maternity pad don naga kina bleeding so sai, sannan kuma zan baki magani wanda bleeding ɗin zai tsagaita amma sai kin fara cin abinci tukun". Ta faɗa tare da cire zanin gadon dake kai wanda ya yi chaɓa-chaɓa da jini sannan ta ɗauki zanin gadon dake kan troley ta shimfiɗa a kai. Maida kallonta ta yi kan jariran sannan ta chanza musu position na kwanciya.

Shiru Mrs Lailah ta yi ma nurse ɗin tare da sakin murmushi wanda ya fi kuka ciwo. Maida kallonta nurse Nadiya ta yi kan Mrs Lailah sannan ta ce. "Madam kiyi haƙuri ki daure ki tashi kiyi wanka. Hana hakan ne duk saboda lafiyar ki sannan kuma gashi kina ta yin bleeding ya ƙi tsaya wa. Ya kamata ki tashi na taimaka miki ki shiga toilet ki gasa jikin ki. Ga jariran ki suna ta kuka da alama yunwa suke ji kuma kin ƙi ki shayar da su ga ruwan nono ya nata zuba a jikin ki. Nurse Nadiya ta faɗa tana mai zuba ma Mrs Laila idanuwanta.

Shiru Mrs Lailah ta yi mata a karo na biyu. Ajiyan zuciya ta sauke cikin dashashiyar murya ta ce. "Shin za ki iya yi min wani taimako?".

Cikin rashim fahimta nurse Nadiya ta ce. "Taimako kuma? wace iriyar taimako zan yi muku?".

Amsa Mrs Lailah ta bata da cewa, "Ina son ki taimaka min na fita daga cikin wannan asibitin".

Zaro idanuwa waje nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na taimaka miki ki futa kuma, ke ɗin fah babban mai laifi ce, ta ya ya zan taimaka miki ki gudu bayan kuma kina gama samun lafiya za'a mayar dake cikin prison. Gaskiya ba zan taɓa iya taimakawa makashiya bah".
Chapter 3 · 0% Book details