← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 59

Sashe 30

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye cikin parlour suka shiga. Yayin da Zahra ta saki baki tana kallon yadda cikin fadan da parlourn ya yi matuƙar tsaruwa.

"Wayyo Allah na, wannan gida aka ko a mafarki ban taɓa ganin irin wannan gida ba".
Zahra ta faÉ—a cikin ranta.

Suna tsaka da tafiya kawai suka ga an sha gabansu.

Dakata wa suka yi da tafiya kana suka dubi matan da suka tsaya a gaban su. Motsa leɓenta Mami ta yi ta ce. "Saratu, Talatu mene ne kuma?".

Kallon juna waÉ—an da Mami ta kira Saratu da Talatu suka kana suka kwashe da dariya.

Dungure wa Mami Kai Talatu ta yi kana ta ja dogon tsaki ta ce. "wato har kin samu damar É—auko Æ´ar aiki ki kawo cikin fadan nan?, uban waye ya baki izinin yin hakan?".

"Rabu da ita Talatu, ai naji duk abin da ya faru a waje, har ƴar talakawan nan ta samu bakin da za ta iya furta wa ta faɗa wa ɗana Junaid magana, lallai dole na koya miki hankali A'isha. Dama yanzu ɗanki Sooraj baya nan balle ya ƙi barin kowa cikin sukuni a gidan nan, saimun ta galla za wa rayuwar ki. Idan ɗan naki ya dawo daga ƙasar da yaje sai ki faɗa masa. Ke kuma".

Gimbiya Saratu ta faÉ—a tana mai maida kallonta kan Zahra ta ce. "Ke kuma Æ´ar talakawa, wato kenen kina tunanin kin zo gidan masu arziki ko za ki iya shoshale kuÉ—in mu ko, to maza ki fice daga cikin masarautar nan kafin na saka yara mata su zo suyi min waje da ke".

Murmushi Zahra ta yi kana ta fara ƙoƙarin gaya wa Gimbiya Saratu maganar da za ta tsufa tana jimamin shi. Ji ta yi Mami ta riƙe mata hannu tare da girigza mata kai . Nan hawaye ya fara sauka kan ƙuncin Mami ta ce. "A'a Zahra kada ki furta komai ke ɗin ƴar aiki na ce, kada kiyi magana dan Allah".

Wafce hannunta Zahra ta yi kana ta ce. "A kan me ya sa ba zan yi magana ba?, baki ji yadda suke gaya miki maganganu marasa dad'i ba ne. Chabb Gaskiya wannan masarautar tana da buƙatar gyara sosai. Kuma ni nan zan gyara mutanen cikin ta".

Da sauri Mami ta ja hannun Zahra kana ta nufi part É—in ta da ita.

***********
"Wow Amrah wallahi kinyi kyau sosai. Maza muje ki nuna wa yaya Umar kwalliyar ki". Ramlat ta faÉ—a tare da jan hannun Amrah wacce ta yi zuru zuru da idanuwa tana kallon su. Kai tsaye parlour suka nufa da ita yayin da suka nufi in da Umar yake wanda ke zaune kan kujera.

Kamar an ce ya É—ago kansa. ÆŠaga kansa ya yi tare da É—ora wa kan Amrah. Bai sanda bakinsa ya furta kalmar masha Allah tabarakalla ba.

Ajiye system ɗin da yake yin aiki ya yi kana ya miƙe tsaye ya ce. "Muje yanzu nayi muku siyayya tare gaba ɗaya".

"Laa yau yaya da kanka za ka kai mu shopping, wannan abu kamar a mafarki". Khairiya ta furta suna mai haÉ—a ido da Ramlat.

Dubansu Umar ya yi ya ce. "Mene ne a ciki dan na kaiku shopping da kaina?, na ga dai ba wani abu ba ne".

Sosa ƙeya Ramlat ta yi ta ce. "A'a yaya ba saika wahalar da kanka ba, mun riga mun faɗa wa yaya Usman ya ce zai kai mu da kansa, kuma sannan koda ma bai kaimu na ga dai akwai jami'ai a gidan nan za su kai mu, amma a ce da kanka ka kaimu ai abun ya yi wani iri".

Kallonsu ya yi kana ya ce. "Ni nayi ra'ayi bawai ku ka sani ba kun fahimta, don haka ni zan kai ku , karku É—auka wa saboda ku ne kun gane".

Girgiza kai Ramlat da khairat suka yayin da suka girgiza kai suka haÉ—a baki wajan faÉ—in. "Mun fahimta".

Dai-dai lokacin Usman ke sauko wa daga kan bene.

Ƙaraso wa in da suke ya yi ya ce. "Muje ko". Cewar Usman.

"A'a Usman ke kayi hayyukan ka, ni zan kai su, saboda bana son wani abu ya same su domin idan wani abu ya same su ba zan ji daÉ—in hakan ba, ana neman rayukan mu ruwa a jallo. Bayan kariyar Allah muma ya kamata mu kare kanmu. Don haka ni zan kai su kai ka koma kawai".

Girgiza kai Usman ya yi kana ya ce. "Tom yaya nima kuma akwai in da zan je Ramlat ta na ce wai saina kai su shopping. Yanzu kuma tun da ka ce za ka kai su shi ke nen, ni zan tafi in da zanje".

Ya faÉ—a tareda fita daga cikin parlourn.

Nan ya ci karo da Gov. Musa Muhammad wato Abban su. Gaishe shi Usman ya yi, yayin da Abba ya amsa kana ya shiga ciki.

Nan take idanuwan Gov. Musa Muhammad ya sauka a kan idanuwan Amrah. Nan take gaban shi ya faɗi!, yayin da ya ji kamar an buga masa ƙararrawa a kai. Salati ya saka sannan ya ce. "Who is this fine beb?". Ya tambaya.

Kawar da kai Umar ya yi kana ya ce. "Am sorry to say Sir, but this is none of your business, please mind your self, banzan ji dad'i nayi maka rashin kunya ba. Wannan da ka ke gani rayuwata ce kuma a kanta babu wanda ba zan iya faɗa da shi ba muddin wani ya ce zai yi ƙoƙarin taɓa ta to lallai ya janyo wa kansa bala'in da babu wanda zai iya cetar sa daga ciki".

Ya faÉ—a tare da jan hannun Amrah kana suka bi ta gefen Abba suka wuce.

Baki sake gaba É—aya suka bisu da kallo.

Maida kallonsa Gov. Musa Muhammad ya yi kan su Ramlat kana ya ce. "Ita É—in wace ce?".

Amsa Khairiya ta ba shi da cewa. "Ita É—in Æ´ar daji ce yaya ne ya kawo ta ya ce mana a nan za ta dinga zama har sai ya gano in da ainiyin iyayen ta suke. Bayan nan bamu san komai ba".

Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Shi ke nen kuna iya tafiya". Kamar jira suke ya ce su tafi m nan suka ruga a guje tare da fice wa daga cikin parlourn.

Samun waje Gov. Musa ya yi ya zauna kan kujera tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya furzar da iska mai zafi tare da sakin murmushi ya ce. "Umar kenen mai zuciyar ƙarfe. Amma fa ba laifi yarinyar nan ba dai kyau ba, ga green eyes masu tafiya da hankali. Tabbas idan nayi safarar wannan ba ƙaramin kuɗaɗe ƴan ƙasar waje za su bayar ba, za su bada fiye da millions ma, ya zama dole na san yadda zan yi na sace ta. The girl is so beautiful and sexy". Haka Gov. Musa ya shiga yin magana shi ɗaya kamar wani zautacce.

Bayan su Umar sun shiga cikin mota ne Umar ya tada mota yayin da Amrah ta zauna a mazaunin gaba. Nan Umar ya tuƙa motar suka bar harabar gidan baki ɗaya.

Kai tsaye hanyar shopping mall suka nufa

**********************
*KAUYEN GUJINGU*

"Malam wallahi abin da ke faruwa da ƴata ya wuce s kaita asibiti sai dai wajan malamai shi ya sa muka zo gare ka. A da chan ba ta yin hakan. Amma kwanan nan kawai sai mu ga tana faɗi ƙasa ita ɗaya ba tare da anyi mata wani abu ba". Daddy ya ƙarashe maganar damuwa ɗauke kan fuskarsa.

"Ƙwarai da gaske Malam, saboda wannan abun da ke damunta ne ya sa muka baro America mu ka zo Nigeria domin neman mafita. Dan Allah ka taimaka mana".
Cewar Mom.

Murmushi dattijon ya yi wanda ke zaune kan wata katifa wanda aka zagaye shi da kara. Yayin da É—akin gaba É—aya rubutun Qur'ani ka ke gani tare da magunguna kala-kala na cututtuka da na aljanu.

Kallonsu malamin ya yi kana ya ce. "Shin ku kuka haife ta?".

Nan take gaban Mom da Daddy ya faÉ—i!, kallon juna suka yi yayin da suka haÉ—a baki wajan faÉ—in "Eh mu muka haife ta".

Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "kuma kuna da tabbacin cewa ita É—aya ce ba ta da wasu Æ´an uwan wanda basua tare da ita?".

Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Eh babu ita kaÉ—ai kawai muka mallaka a duniyar nan".

Girgiza kai Malamin ya yi kana ya ce. "To Æ´ar ku ba ta da wani aljanu, samm babu aljanu ko sihiri ko kuma maita a tattare da ita. Wannan abun da ke faruwa da ita ba wai haka kawai ba ne dole dai akwai dalilin faruwar hakan. Amma batun cewa ko aljanu ke damunta, samm ba gaskiya ba ne".

"To Malam idan ba aljanu ba ne mene ne?, Sannan kuma mene ne abin da zamu yi ya daina?". Cewar Grandpa.

Amsa Malamin ya ba shi da cewa. "Babu abin da zamu iya yi ya daina domin da wannan abun haka haife ta, sannan alamu ya nuna cewa wannan ahali naku sun aikata wani babban kuskure a baya wanda a yanzu ba za ku iya gyara wann kuskuren ba domin kuwa lokaci ya riga ya ƙure. Dole a chan baya kun cutar da wata wanda ba ta ji ba, bata gani ba, sannan kuma kunyi shedar zurr hakan abin da ba ta aikata ba, to ku sani cewa ƴaƴanta su ne za su ɗaukar mata fansar abin da haka aikata mata".

Cikin rashin fahimta gaba É—aya suka dubi malamin kana suka haÉ—a baki wajan faÉ—in. "Bamu fahimci abin da ka ke magana a kai ba".

Murmushi Malamin ya yi kana ya ce. "Baku da wata ƴa a ahalinku ku ka kore ta ba tare da tabbatar bincike da kuma ƙwaƙwarar hujja hakan abin da ba ta aikata ba".
Chapter 30 · 0% Book details