Sashe 37
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina kai Zahra ta yi ta ce. "Gaskiya ne sai kace É—an gold. Ni har na matsu ma na ga Sooraj É—in".
Kallonta Mami ta yi ta ce. "Kada ki damu a yau za ki ganshi. Yauwa na ma tuna na ce zan aike ki da wasu daga cikin ƴan aikin masarautar nan zaku je ne kasuwa siyo mai special kayan girki wanda nake yi masa special domin baya cin abinci kowa in ba nawa ba. Sannan kuma yana matuƙar son black tea gashi kuma babu, shi ne nake so ku ɗan je driver ya kaiku ku siyo dan Allah".
"Aba Mami sai kin ma haɗa ni da Allah, kada ki damu in sha Allahu yanzu ma zamu je bara na ɗauko mayafi na". Ta faɗa tana mai shige wa ɗakin ta, lokaci ƙalilan ya ɗauke ta a ɗaki ta fito kanta sanye da mayafi blue colour.
Zuwa inda Mami take ta yi ta ce. "Shi ke nen bani kuÉ—in muje".
Miƙa mata kuɗaɗe Mami ta yi kusan dubu dari biyu.
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi baki na rawa ta ce. "Mami irin wannan kuɗi haka sai kace za'a biya kuɗin sadakin wata. Ina laifin dubu dubu ɗaya ƙarƙari ma mun kashe kuɗi da yawa 1500 amma shi ne za'a zuba uban kuɗi haka. Ni tunda nake ma ban taɓa ganin kuɗaɗe masu yawa haka ba sai yau".
Dariya zahra ta bawa Mami. Girgiza kai kawai Mami ta yi ta ce. "Zahra kenen, kina da abin dariya ke za ki ga kamar sun yi yawa ne amma kuwa babu yawa".
Saka hannu Zahra ta yi ta karɓi kuɗi salati riƙe a bakin ta.
Maida kallonta ta yi kan Mami ta ce. "Amma ni bana so naje da su Æ´an aiki".
"To da wa ki ke son ki je?". Mami ta tambayi Zahra.
Amsa Zahra ta ba ta da cewa. "Da su Samira nake son muje".
Zaro ido Mami ta yi waje. "Zahra ki rufa min asiri, ke kin san ba za su je ba wahalar da kai ne kawai".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Tabbas ni nan zan sa su suje, bakin ce suna matuƙar tsoron ɗanki ba, to ki jira ki gani".
Ta faÉ—a tana mai fice wa daga part É—in Mami. Chan ta hangi su Samira sai sha'anin su suke hankali kwance. Hamdala Zahra ta yi tare da nufar in da suke.
Binta suka yi da kallo ganin yadda ta yi cirko-cirko a kansu.
"Ke mene ne ki ka wani zo ki ka tsaya a kanmu?".
Amsa Zahra ta basu da cewa. "Yahya Sooraj ne ya bamu umarni da muje kasuwa yin siyayya tare". Jin Zahra ta ambaci sunan Sooraj ya suka miƙe tsaye jiki na rawa suka ce. "To ai sai ki faɗa mana tuntuni bawai ki tsaya a kanmu ba".
Nan suka nufi wajan parking space tare da shiga cikin mota. Yayin da driver ya tashi mota suka bar harabar masarautar.
Kai tsaye kasuwa ya nufa. Yana zuwa ya yi parking yayin da suka fita. Nan Zahra ta shiga cikin kasuwa tareda fara siyayyar abubuwan da Mami ta gaya mata. A sa'inda su Samira suka samu guri suka zauna a bunsu.
Saida Zahra ta gama siyayya tsaff sannan ta saka hannu domin ciro kuÉ—i a jikin ta. Wayam ta ga babu kuÉ—i ba alamar su. Zaro idanuwa waje ta yi tare da sakin salati.
"Yau akwai tashin balagan tsuntsaye. Wane ɓarawon ne ya sace min kuɗi, tabbas yau babi wanda zai fita daga kasuwan nan muddin ba'a fito da kuɗin nan ba".
*******
Jere fararen motoci ke tafiya kan titin wanbai. Tare da dokuna wanda suka mara musu baya da kuma fadawa wanda suka zagaye motocin yayin da jama'a suka shiga miƙa gaisuwa.
Cikin motan kuwa wani mature guy ne zaune cikin mota a ƙalla zai kai kimanin shekaru 35 zuwa 38 ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayin da news paper ke riƙe a hannunsa. Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga ubangiji wanda ya yi wannan kyakyawar halittar.
Sanye idanuwansa suke da broline glass yayin da hannayensa suke sanye da rolex wrist watch. Lumshe idanuwansa ya yi masu kama da madara. Yayin da suman kansa suka kwanta suka yi luff. Sajen fuskarsa masu taushi da laushi suka ƙara masa kyau.
Sanye yake cikin labcoart duban driver ya yi cikin cool voice É—in sa ya ce. "Ka wuce da ni kasuwa zan siya black tea".
Murmushi Driver É—in ya yi ya ce. "Aba ranka shi daÉ—e, mene ne amfanin mu?, yau É—in nan ka dawi Nigeria bai kamata ka shiga kasuwa ba idan muka isa fada Æ´an aiki za su zo su siya".
Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Kaine shugaba ko ni ne shugaba?, maza kayi yadda na ce".
"A gafarce ni ranka shi daÉ—e in sha Allahu zamu je. Amma me ya sa ba zamu wuce shopping mall ba sai cikin kasuwa?, ina ganin kamar hayaniya ta yi yawa a chan".
Shiru Yarima ya yi sannan ya ce. "Shi na gadaman zuwa kai mene naka?".
"Bakomai ranka shi daÉ—e ". Driver É—in ya faÉ—a.
Kai tsaye kasuwa ya nufa da su. Yayin da ya tarar da taru jama'a sun yi zagaye da alama wani abu ne ke faruwa.
Æangaren Zahra kuwa babu abin da take sai surfa bala'i yayin da ta rikita kasuwar a lallai sai an fito da wannan kuÉ—i.
Babu abin da mutane ke yi sai kallo.
Fitowa Yarima Sooraj ya yi daga cikin mota. Daga nesa su Samira suka hango shi. Nan take cikin su ya É—uri ruwa. A hankali suka silale daga wajan.
Ƙarasawa wajan Sooraj ya yi. Nan idanuwan shi ya sauka a kan Zahra wanda sai faman masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Takaici ne ya kama Sooraj, dubanta ya yi ya ce. "Ke baki da hankali ne za ki zo ki tada wa mutane hayaniya a wajan nan". Ya faɗa cikin ɓacin rai.
Dubansa Zahra ta yi nan suka haÉ—a ido a tare. take gaban kowanensu ya faÉ—i!, yayin da suka fara jin wani irin yanayi na da ban.
Galla masa harara Zahra ta yi ta ce. "Kai malam waya gayyace ka nan?, shin ka zo ka biya kuÉ—in da haka sace ne?, to maza ware daga nan".
Nan take ran Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci. Take ya ji tsanarta ya shiga cikin ransa ya tsani mace mara kamun kai da rashin sanin darajar kai.
Juya wa Yarima Sooraj ya yi tare da barin wajan. Shiga cikin mota ya yi yayin da driver suka tada mota suka bar wajan.
Kai tsaye masarauta suka nufa.
Bayan tafiyar Sooraj ne Zahra ta ga kuɗin a dunƙule s ƙasa. Hamdala ta yi tare da bawa mutanen gurin haƙuri. Miƙa wa mai kayan kuɗin ta yi tare da karɓar abubuwan da ta siya.
Waige-waige ta fara yi domin gani su Samira amma ba ta gansu. Haka ta ci gaba da cigiyar tmds ta ga ba zata iya ba ta shiga cikin mota yayin da driver ya ja ta suka bar kasuwan.
Shiga ciki motocin su Sooraj ya yi cikin masarauta. Nan take dakarai da fadawa suka shiga durƙusawa suna kwasar gaisuwa tare da yi masa ƙirari.
Fitowa Yarima Sooraj ya yi tare da amsa gaisuwar tasu.
Yayin da su Gimbiya Talatu suka sha jinin jikinsu. Gaishe da mai martaba Yarima Sooraj ya yi cikin girmama wa tare da gaidar da su Gimbiya Saratu. Sama-sama su Gimbiya Saratu suka amsa.
Part ɗin sa ya nufa tare da nufar ɗakin ajiyar sa sannan ya saka thumbprint ɗin sa. Nan take ƙofar ta wangale gani ya yi an tsaftace ɗakin an gyara shi ba kamar yadda yake ba. Mamaki ne ya bayyana kan fuskarsa. Da sauri ya fita daga cikin ɗakin tare da fitowa harabar fada yana mai ƙwalla kiran kowa na wannan masarautar. Kan ka ce me mutane sun taru a fada.
Kallon kowanensu ya yi sannan ya ce. "Wane ne wanda ya shiga ɗakin ajiya ta?". Shiru gaba ɗaya suka yi babu mai bakin magana. Dai-dai lokacin da Mami da su Samira ke ƙarasowa wajan.
Daka musu tsawa ya yi yana mai faɗin. "Na ce wane ne ya shiga ɗakin ajiya ta?". Ya faɗa rai a matuƙar ɓace. Sannan ya ce. "Tabbas ko wace ce wannan ƴar leƙen asiri ce kuma ba zan rabi da koma wane ne ba. babu wanda ya san password ɗin wannan ɗakin sai ni kaɗai, ta ya ya haka iya buɗe wa bayan ni kaɗai ne na san password ɗin?".
Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Eh wata sabuwar Æ´ar aikin mu ce sunanta Zahra. Laifi ta yi shi ne mai martaba ya ce za ta dinga share wannan É—akin kuma babu ranar da za ta tashi ta faÉ—i ba ta share ba".
"Where is she?". Yarima Sooraj ya tambaya cikin tsananin ɓacin rai.
Dai-dai lokacin da motar su Zahra ke shigowa. Parking motan ya yi yayin da ta fito tare da kayayyakin da ta je siya.
Maida kallonsu suka yi baki É—aya kanta. "Yauwa ka ga Æ´ar halak ita ce wannan". Mami ta faÉ—a tana mai nuna Zahra.
Take rab Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci ganin yarinyar da ya gani a kasuwa. Ƙarasawa wajan Zahra ta yi ganin yadda gaba ɗaya suke binta da ido ya sa ta kawar da kanta gefe.
Nan take ta haɗa ido da Sooraj. Take gabanta ya faɗi!. Sakin kayan da ta riƙo ta yi gaba ɗaya suka faɗi ƙasa. Sannan ya fara tafa hannunta tare da riƙe haɓarta ta ce. "Iyyeeh!, wato har gida ka biyo ni kenen, ƙara ta ka kawo ko me?, dama ina ganin fuskar ka na san kai ba na Allah ba ne. To maza zo ka fice daga cikin masarautar nan kada ka bari Yarima Sooraj ya shigo ya tarar da kai a nan domin ba za ka ji da dad'i ba".
Murmushi Yarima Sooraj ya yi ya ce. "Au aba da da gaske?".
Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske nake ko zaci ƙarya nake?. Idan ka bari Yarima Sooraj ya zo ya ganka a nan ba za ka ji da dad'i ba".
Kallonta Mami ta yi ta ce. "Wane Yarima Sooraj kuma bayan gashi nan a gaban ki".