Sashe 40
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya shiga É—akin sa tare da haÉ—a kayan sa cikin travel box. Bayan ya gama saka kayansa ne ya nufi É—akin su Grandpa sannan ya sanar da su yana son yin tafiya sainan da sati zai dawo. Addu'a suka yi mai. Daga bisani ya saka kayansa cikin mota. Babu abin da Safira kai ta faman yi sai satar kallonsa.
Babu zato suka haÉ—a ido da Safira, saurin kawar da kanta Safira ta yi gefe. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Kodai za ki je ne?".
Taɓe baki Safira ta y ta ce. "Nop, ni kam babu in da zani". Ta faɗa tare da shige wa ciki gidan.
Girgiza kai kawai Aliyu ya yi tare da tada mota sannan suka yi sallama da mutanen gidan gaba É—aya daga bisani ya fice daga gidan. Bai zarce ko ina ba sai hanyar Kano.
_________________________
Zahra na fita ta hangi kuloli a jere kan dining hakan ya sa ta haɗiye yawu. Da sauri ta je ta zauna kan table ganin zaman kujera ba zai finshe ta ba, ya sa ta kwashe gaba daya kulolin ta jera a ƙasa sannan ta zauna a ƙasa ta fara buɗe kulolin. Take wani irin ƙamshi ya bugi hancin ta hakan ya sa lumshe idanuwanta sannan ta sake buɗe su. Tuwon shinkafa ne miyan taushe ya ji naman turkey yayin da bangare ɗaya kuma fried rice ne ya ji coslow da naman kaza. Sai ɓangare ɗaya kuma kunun aya cikin jug da kuma lemo mai sanyi tare da Fruit salad.
Ganin ba za ta iya ɗauke ido kan wannan abinci ba, ya sa ta cire duka chokulan kan trey ɗin abincin ta zubar a ƙasa. Hakan ya sa ƙaran chokulan suka bada wani irin ƙara.
Jin ƙara daga parlour ya sa su Gimbiya Saratu da Talatu tare da ƴaƴanta fitowa. Yayin da ita ma a dai-dai lokacin Mami ta fito daga cikin ɗakin ta domin ganin meke faruwa. Dai-dai lokacin kuma Junaid ke dawo wa daga fadan mai martaba.
Fitowa Sooraj ya yi daga cikin É—akin sa. Tare da nufar hanyar parlour. Tsaya wa chakk gaba É—aya suka yi ganin yadda Zahra ke É—ura wa ciki ta abinci. Cin abinci ta take hankali kwance ba tare da tsoro ko wani tunani ba. Sai loma take ta kwara abincin da lemo tare da kunjn aya. Haka ta cigaba da cin abinta ba tare da ta kula da zuwansu Sooraj wajan ba.
Baki sake gaba É—aya suke kallonta. Zahra kuwa sai da ta cinye Tuwon shinkafan tass sannan ta koma kan fried rice. Haka ta na ci tana sumbatu. "Wayyo dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni, dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni"
Sannan ta ƙara da cewa. "Gaskiya kuɗi duniya ne, Allah kayi mu yadda muke so. Yoo ƴan banza ba dole su dinga tumbi ba suna cin abinci mai daɗi da gina jiki. Daɗin ta ma ba za su ci ba, kinga kenen zanci sosai na ƙoshi, naci na ci na bar na bari. Shi ya sa wannan Gimbiya Talatun bakinta yake wangalele kamar na akuya tunda tana cin abinci mai daɗi dole, sai kuma waɗan nan ƙwalaye ukun nan su Samira ko, dole su dinga yadda suka gadama tun da suna cin kayan dad'i. Yanzu ni duk ba wannan ba hanyar da zanbi na koya wa wannan mai ƙaton kai hankali nake Sooraj yake ko, saina koya mai hankali, ba an ce ni ce zan dinga kula da shi ba, kawai idan Mami ta bani abinci shi na cinye sai in kai mai ragowa ya ci". Ta ƙarashe tana mai bushe wa da dariya.
Duk abin da take a gaban idanunsa. A sa'inda ɓangare ɗaya Gimbiya Talatu ta yi mugun ƙulu wa. Jin abin da Zahra ta faɗa game da halittar bakinta. Sooraj kuwa mamaki kawai ya shiga yi ganin yadda take ta sumbatu tana cin abinci duk ba ga san suna tsaye a wajan ba.
Saida ta gama da komai da cikin kulan tass sannan ta kora da kunun aya da fruit salad. Ji ta yi cikin ta ya yi mugum cika. Gatsa ta yi ta ce. "Ya kamata ki kwanta Zahra domin abincin da ki ka ci su zazzage". Ta faɗa tana mai kwanciya a ƙasan wajan tana mai fuskantar saman silin. Gabanta ne ya bada wani rass!, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku ganin gaba ki ɗaya ƴan gidan tsaye a kanta.
Zumbur ta miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin ta.
Kallonta Sooraj ya yi tare da kallon kulolin da ta cinye abincin ciki sannan ya girgiza kai ya ce. "Sannunki da aiki, yanzu mutum in banda dabba waye zai iya cinye uban abincin nan, to ki sani cewa baki ci a banza ba domin kuwa sai kin koma kasuwa kim siyo duk abin da ki ka ci sannan kin sake dafa irin shi komai da komai".
Rai a ɓace Gimbiya Talatu ta ce. "In banda iskanci ƴar talakawa har ta samu matsayin da za ta ci abinci a kulan da muke cin abinci. Sannan kuma har ta samu damar ta ce wai ni mai wangalellen baki. Lallai kam wuyarki ya isa yanka".
"Madam za ki iya mana shiru a nan". Cewar Sooraj. Tsaki Gimbiya Talatu ta ja tare da wuce wa part É—in ta ganin hakan ya sa Saratu ta bi bayanta. Sannan sauran ma suka watse ya rage Sooraj, Mami, da kuma Zahra.
Kallonsa Zahra ta yi bakin ta duk maiƙon kaza ta ce. "Yarima wallahi ban iya girki ba, ban taɓa yi ba, ta ya zan iya yin mai daɗin wannan?, kayi haƙuri dan Allah".
Gyara tsayuwar sa Sooraj ya yi ya ce. "My wish is my command, dole ki sake girka irin wannan kuma taste É—in dole ya zama iri É—aya.
Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin kalmarsa ta ƙarshe. "Ni na san ma sai dai nayi muku jagwab ɗin abinci don ban iya ba".
Bai ƙara cewa komai ba ya koma part ɗin sa.
Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi abin da ya ce karki damu da wajan nan da ki ka ɓata zan sa ƴan aiki su gyara, maza kije ki siyo ingredient ɗin, domin ya ce ba za'a taɓa na gida ba".
"Shi ke nen". Zahra ta faÉ—a tare da shiga É—aki ta saka saka hijabi. Fitowa ta yi yayin da Mami ta ba ta isashun kuÉ—aÉ—e domin siyan kayan abincin da ta ci. Bayan ta ba ta kuÉ—in ne fita daga cikin harabar masarautar tare da tarar mai napep ya kaita kasuwa.
Bayan Aliyu ya isa Kano ne ya samu wani guri kusa da kasuwar kwari ya yi parking. Sannan ya fara waige-waige. Chan ya hango mai tallan tsire. Hakan ya sa ya tare shi tare da siyan na dubu É—aya domin rage yunwar da take damun shi.
Zahra kuwa saida mai napep ɗin ya yi tafiya mai nisa sosai kafin nan ya isa kasuwar kwari. Chan ta hango tsayuwar Aliyu jikin motarsa. Tunani ta shiga yi kamar ta san wannan mutumin. "Wannan kamar wannan ɗan sandan da ya so raina min hankali a magarƙama ne ko?". Ƙara kura masa idanu ta yi. "Laa babu tantama kuwa shi ne". Dakatar da mai napep ɗin ta yi da ya tsaya. Ba tare da ta tsaya biyan mai napep kuɗin sa ba ta tsallaka titi da gudu tare da nufar in da Aliyu yake tana mai faɗin. "Malam ɗan sanda mai ɗagaggen wando kaine a garin Kano?".
Juyawa Aliyu ya yi ganin waye wannan mai furta wannan kalma. Nan take ya haÉ—a ido da Zahra. Take gabansa ya yi mummunar faÉ—uwa!. Nuna ta ya yi ya ce. "Safira!".
Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wace ce kuma haka?, wai Safira, kai ni ce fa baka gane ni ba a magarƙama da ka zagar min uwa na so nayi maka duka ka tuna?. Ba kai ne wannan ɗan sandan mai ɗagaggen wando ba?".
Dafe kansa Aliyu ya yi jin yadda kansa ke ƙoƙarin sara masa. Riƙe kansa sosai ya yi domin yin tunanin a ina ya santa. Ɗaga kansa ya yi ya kalle ta ya ce. "Kenen ba ke ba ce Safira ba?".
Haɗe giran ta Zahra ta yi tare da turnuƙe fuska ta ce. "Wace ce kuma Safira?, ni fa malam sunana Zahra ba Safira ba".
"I am totally confused, what's going on?". Aliyu ya tambayi kansa. Nan take ya fara tuna wan can ta magarƙamar. Rass gabansa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Tabbas wannan ita ce wanda na gani a magarƙama kwanaki mai brown eyes, sannan Safira ma tana kama da ita, ga kuma ranar nan na ga wata mai kama da Safira mai grey eyes. Kenen hakan yana nufin su uku ne?, idan kuwa hakan ta kasance to tabbas hasashen Mom gaskiya ne, kenen hakan yana nufin yaran Mrs Laila ne?!".
COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI 🙠ðŸ™
ALƘALAMIN âœï¸
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)
Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*ðŸªðŸŒŽðŸª.
Daji 🌲
Magarƙama🢠da kuma
BirniðŸ™ï¸
WRITTEN & DIRECTED BY âœï¸ A'ISHA M.B 💞💞💞
(ZinariyarðŸ§â€â™€ï¸Jajirtattu)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 âœï¸
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Æ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauÆ™i_.âœï¸
*DIAMOND 💎 STARâ*
*LADIES ðŸ§â€â™€ï¸ðŸ§ðŸ¼â€â™€ï¸ðŸ§â€â™€ï¸*
(We stand together)
ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤
بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3ï¸âƒ£9ï¸âƒ£â–¶ï¸4ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
*___________________________________________*
"Wai tunani me ka ke yi ne malam É—an sanda?". Cewar Zahra.
Murmushi Aliyu ya saki sannan ya ce. "Babu komai kawai dai ina mamaki ne, masha Allah gaskiya naji daÉ—in haÉ—uwa da ke. Idan babu damuwa shin zamu iya zama abokai?".
Harara Zahra ta galla mai sannan ta ce. "Ta ina ka taɓa jin ana aboki tsakani mace da namiji?, ni bana son wanda zamu fara abota ya kawo min zancen soyayya, atohh dai, dan na san yawancin ku daga abota za ku fara sai a zarce soyayya".
Dariya Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai karki damu ni ina da ma wacce zan aura, sunanta Safira".