← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 59

Sashe 8

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maida kallonta ta yi kan mijinta sannan ta ce. "Kada ka ce haka mai gida, nayi wa Mrs Laila alƙawarin cewa zan yi iya bakin ƙoƙarina wajan ganin na taimaka wa yarinyar ta sannan na riƙe ta a matsayin ƴar da na haifa. Ita ɗin da yarinya ce kaɗai, bai kamata a ce laifim uwa ya shafi ƴa ba, yanzi idan ka ce na fitar da ita ina ka ke son na kaita?, rayuwarta zai kasance tana shan wahala ne, a yayin da kuma ba bu wanda zai share mata kuka ko ya sata farin ciki domin bata da uwa a kusa da ita. Ba ita kaɗai bace ba su uku ne matan kuma kaga tun basu san kan su ba haka raba su domin tseratar da rayukansu dana mahaifiyar su, sannan kuma domin su san mahimmanci da rayuwa take dashi. Dan Allah kada ka ce A'a kaji na roƙe ka". Ta ƙaradhe maganar tare da fashe wa da kuka.

**"Yanzu mene ne abin yi kenan?, mun bi diddigin mijin nata sannan munje gidan ance ya daɗe da barin ƙasar baki ɗaya, yanzu kenen dole dai a kai yarinyar nan gidan marayu". Cewar DPO wanda ke zaune kan bencin dake cikin magarƙamar a yayin da sauran ƴan prison ɗin suka zagaye jami'an suna kallon jaririya mai brown eyes ɗin da ke kwance kan cinyar ƴar sanda mace, a sa inda ba bu abinda jaririyar keyi sai kuka.

"Haka ne sir, nima abin da nayi tunani kenen, ina ga kawai best solution shi ne a kaita gidan marayu, dan ba lallai a samu wanda zai iya riƙe ta ba a nan dole dai chan za'a kaita domin sai ya fi mata alkhairy". Cewar ɗaya daga cikin warders ɗin.

"Shi kenen tom ku shiyar jami'ai, domin zamu kaita gidan marayun".

Daga sama suka ji an ce. "Ni ce nan nafi cancanta dana riƙe ta". Waigawa gaba ɗaya suka yi rareda zuba wa Hajiya Binta idanuwa.

Cikin rashin fahimta DPO ya ce. "Kamar ya ke ki ka fi cancanta da ki karɓi yarinyar nan?, kenen a tunanin ki mu baki ita ki lalata yarinyar mutane, so ki ke a barta cikin magarƙama ta zama irin ku?, ta ina ma ki ke da halaƙa da ita da har zaki buɗi wannan ƙazamin bakin naki kice ke zaki riƙe ta?".

Ta kowa Hajiya Binta ta fara yi, bata tsagaita da tafiyar ba har sai da ta tabbatar da isa gaban shi sannan ta jefa idanun ta cikin nasa ta ce. "A matsayina ta mai riƙo, kuma sannan nayi wa mahaifiyar ta alƙawarin cewa zan kula mata da ita sannan na bata ingantacciyar rayuwa. Kada kuyi tunanin ko saboda ni mai laifi ce ku gna bi yarinyar, samm abin da ku ke tunani ba haka bane ba. Na riga dana ɗaukar mata alƙawarin cewar ba zan taɓa barin hannun yarinyar ba har izuwa numfashina na ƙarshe sannan ba zan bari ta san mene ne hake nufi da kalmar hawaye ba, domin ba zan taɓa bari ruwa ya fita daga idanuwanta ba saidai idan bana raye, ba zan bari tasha wahala kamar yadda tasha a rayuwarta na yanzu ba. Kunji dan Allah ku bani ita ". Ta faɗa kanta a ɗuƙe.

Kallon juna jami'ai Da DPO suka shiga yi. Gyaran murya DPO ya yi sannan ya ce. "Zamu baki ita ne mundin kotu ta aminta da hakan, amma in har kotu taƙi amincewa to sai dai kiyi haƙuri dan ba bu abin da zamu iya yi a kai".

Miƙe wa tsaye ya yi sannan ya mika wa hajiya Binta jaririyar. Hannu Hajiya Binta ta sa tare da karɓar yarinyar.

Kallonta DPO ya yi sannan ya ce. "Ni zan ɗauki nauyin kula da yarinyar nan, kama daga abinci, tufafi, da dai sauran abubuwan da ba za'a rasa ba. Yanzu dai zan saka wasu daga cikin jami'ai suje su suyo baby food domin ga dukkanin alamu jaririyar nan yunwa take ji, kuma ya kamata a ce shayar da ita a kayi bawai a bata abinci ba, don haka yanzu ki riƙe ta, zanje na samu alƙali da sauran jami'ai indai har yarinyar ta dace ta zauna a nan to za'a barta, idan kuma suka ƙi amincewa ko wani nata yazo to zamu damƙa masa ita ne. Kin amince da hakan?".

Girgiza kai Hajiya Binta ta yi ta ce. "Na amince". Ta faÉ—a tare da rungume jaririyar kan kirjinta.

*"Mrs Laila ki dakata, jami'ai za su iya ganinki sannan su maida ki magarkama, kuma hukunci da za'a yi miki zai ninka na da ne domin guduwa ki ka yi". Tsayawa Mrs Laila ta yi tana mai fuskantar sa ta ce.

"Dama bayan rataya akwai hukuncin da ya ninka shi?, rataye ni da za'a yi, to faɗa min wane hukunci ne ya ninka rataya?, ni na gwammace su kamani su yi min abin da yafi rataya dana bi ka. Da a ce kasan irin ƙuncin da mutane suka dasa mun a cikin rayuwata da ba zaka faɗi hakan ba. Dan haka ni ko kuma ƴata bamua da buƙatar taimakon ku". Ta faɗa tare da ci-gaba da tafiya.

Ƙaran motocin ƴan sanda be ya karaɗe ilahirin wajan. Jin hakan ya sa ɗan sandan ya fara ƙwalla kiran Mrs Laila tare da cewa. "Ga sunan sun zo kama ki, ki tawo mu gudu kada suyi nasarar ɗauke ki, don idan suka kama ki za su raba ki da ƴarki kuma rabuwa ta har abada".

Jin hakan ya sa Mrs Laila waigawa tana mai fuskantar ɗan sandan. Kafin ta yi wani yinƙuri. Ƴan sandan suka zagaye su da motocin su.

"Sir gata nan mun ganta tare da wani, yanzu haka ƙoƙarin kama su muke".
Cewar ɗaya daga cikin jami'an wanda waya ke riƙe a hannun shi.

Murmushi ya saki ta cikin waya sannan ya ce. "Very good, aikin ku na kyau kuyi maza-maza kumata domin muna da bukatar fingerprint É—in ta yanzu".
Mutumin dake kan waya ya faÉ—a.

Ganin suna ƙoƙarin kama su ya sanya ɗan sandan ya yi hanzarin jan hannun Mrs Laila tare da bangaje wasu daga cikin jami'an suka fara gudu. Ganin hakan ya sa jami'ai suka gyara zaman bindigogin su sannan suka fara shooting ɗin bullet.

Da gudu suka tafiya ba bu gaggautawa yayin da jaririyar dake hannun Mrs Laila keta faman kuka. Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin bullet ɗin da jami'an suke harba wa ya samu wajan ƙafar ɗan sandan dake tare da mrs Laila. Nan take ya faɗi ƙasa yayin da jini ya fara fita daga ƙafar. Ƙara mai sauti ya saki!, da sauri Mrs Laila ta koma kan shi tare da ƙoƙarin ɗaga shi. maida kallonsa kan mrs Laila ya yi sannan ya ce mata.

"Maza ki tafi ki tseratar da rayuwarki da kuma ta Æ´arki, kada ki tsaya, maza kije".

Cikin kuka Mrs Laila ta ce. "Ba zan iya tafiya na barka a cikin wannan mawuyacin halin ba, idan nayi hakan ban kyauta ba, karka damu kafin su iso zaka tashi". Ta faÉ—a tana mai fashe wa da kuka.

"Ki tafi ki barni, ni ba zan iya tafiya ba daga nan. Dan haka ki tafi!". Ya faÉ—a cikin É—aga tsawa.

Miƙe wa tsaye Mrs Laila ta yi yayin da taga jami'an sun kusan ƙaradowa inda suke. Da sauri ta bar wajan sannan ta ci gaba da gudu.

Ƙarasowa wajan jami'an suka yi yayin da wasu suka tsaya tare da kama ɗan sandan sannan wasu suka bi Mrs Laila a baya.

Tun da ta fara gudu bata san inda take nufa ba, yayin da ƙafafuwanta suka ji rauni saboda bata sanye da takalma.

Haka ta ci gaba da gudu ba tare da ta dakata ba. Yayin da zufa suka bi suka lulluɓe jikinta baki ɗaya. Cikin rashin sa'a kafarta ya bugu wani dutse. Nan take ta faɗi tare da fara gangarawa cikin daji mai cike da bishiyu da namun daji.

Haka ta ci gaba da gangarawa a ƙasa harta faɗa a cikin wani kogi mai wanda ya cika da ruwa. Nutse wa ta yi cikin ruwan yayin da kukan jaririyar ya karaɗe gaba ki ɗaya ilahirin dajin.

Wani itaciya ta hango daga chan nesa da sauri ta fara swimming harta isa ga wannan itaciyar sannan ta saka hannu tare da riƙe itaciyar ƙamm a hannunta sannan ta fara yinƙurin fitowa. A hankali ta fara jan itaciyar yayin da ta fara sama daga cikin ruwan. Cikin rashin sa'a itaciyar ta tsinƙe yayin da mrs Laila ta faɗa a ciki ruwan.

Nan take ruwa ya shige mata baki da hanci, yayin da hakan ya jawo ta kasa numfashi sosai. Nan da nan namomin daji suka fara fitowa. Birririka ne gaba É—aya suka zagaye kogin.

Da sauri Mrs Laila taja da baya tana mai ambatar sunan Allah. Fuskanta suka yi da cewar tana da buƙatar taimako, hakan ya sa suka fara tsalle kan bishiyu suna ciccire itacuwan dake jikin bishiyoyin sannan suka fara haɗa igiya dashi tamkar mutane. Nan da nan suka ɗaure igiyar jikin wata ƙatotuwar bishiya sannan suka jefa wa Mrs Laila dake jikin ruwa igiyar a yayin da su kuma suka ja da baya.

Riƙe igiyar Mrs Laila ta yi ƙamm a hannunta sannan ta fara jan igiyar tana yin sama. Saida taje sama daga ciki kogin sannan ta ajiye yarinyar tare da yi wa Allah godiya da ceton su da su birrirukan suka yi. Cikin farin ciki ta kalli yarinyar sannan ta ce. "Bayan wuya sai dad'i, Allah ya yi wa rayuwarki albarka. Daga yau sunanki zai kasance Amrah". Ta faɗa tare da rubuta sunan da jinin dake fita daga hannunta a jikin ƙaramin dutsen dake kusa da ita a kogin.

Bayan ta gama rubutawa ta fara ƙoƙarin fitowa daga cikin kogin da igiyar dake hannunta. Nan take taji saukar bindiga a saitin zuciyarta, yayin da jininta ya fesu jikin jaririyar da dutsen. Nan take ta saki igiyar yayin da ruwa ya yi hawon gaba da gangan jikinta.

Nan take birrirukan suka hau jami'ai tare da fara yayyaƙushi su da cizo. Ihuuuuu! Jami'an suka yi yayin da suka fara guduwa tare da barin ilahirin dajin baki ɗaya.

Komawa kan jaririyar suka yi jin yadda take ta faman kuka ya sanya sauran namun jejin fitiwa baki É—aya.
Chapter 8 · 0% Book details