← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 59

Sashe 56

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda kin ce ƙarya muke miki ki ɗauki lemon ki sha, a nan ne zamu tabbatar baki saka guba ba". Cewar Gimbiya Saratu.

Furzar da iska waje Sooraj ya yi. Take idanuwansa ya sauka kan hannun Zahra wanda ke riƙe da ƙullin magani. Da sauri ya ƙarasa inda take tare da sa hannu ya karɓi ƙullin maganin ya shinshina. Da sauri ya kauda kai jin cewar tabbas wannan poison ne.

Ɗago da idanuwansa ya yi tare da ɗora su kan Zahra ya ce. "Tabbas Zahra kece nen ki ka zuba wa mahaifiyata guba a lemo, idan ba ke bace ta ya ya ƙullin magani ya zo hannunki?".

Nan su Gimbiya Talatu da yaransu suka saki murmushin mugunta.

Hawaye ne suka fara bin ƙuncij Zahra ta ce. "Ban san ta ya ya zan fara yi muku bayani ba, ni bani da sheda sai Allah. Allah shi ne sheda na, shi ne ya san wanda ya sa wannan guban. Wallahi bani ni ce..... Bata ƙarasa maganar ba Sooraj ya kwashe da marika har guda biyu wanda ya yi sanadiyar faɗuwa Zahra ƙasa.

"Mahaifiyar tawa za ki kashe?, wacce ta ɗauki ki tamkar ƴar cikinta?, a da ina tunanin ke ɗin mutuniyar kirki ce ashe ke ɗin mutuniyar banza ce. Na tsane ki, na tsani duk wanda yake ƙoƙarin cutar da lafiyar mahaifiyata. Wallahi da a ce mahaifiyata ta sha wannan poison ɗin, da saina tabbatar da kinsha baƙat azaba a rayuwarki, zan sa a kama ki a zartar miki hukunci. Yanzu aka ma baki tsira ba, domin yanzu zan kira ƴan sanda su kama ki".

Babu abinda Zahra ke yi sai kuka. take ta ji kewar iyayen ta da na danginta. Da a ce suna raye ba za'a dinga yi mata hakan ba.

Dakatar da Sooraj Mami ta yi ta ce. "A'a kada ka kira Æ´an sanda, bana son wannan abun ya isa kunnen mai martaba domin hukuncin zai fi haka, kawai ta tashi ta fice daga masarautar nan kuma kada mi sake ganin koda inuwarta a nan fadan".

Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tana mai share hawayenta.

Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Maza zo ki fice, bana son na sake ganin wannan fuskar taki" Ya faɗa yana mai yi mata nuni ga hanyar ƙofa".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Zan tafi amma kafin nan, zan sha wannan lemon idan ya so ni zan mutu a maimakon Mami".

Ta ƙarashe maganar tana mai nufar inda lemon yake. Da sauri Sooraj ya tafi domin dakatar da ita. Amma ina kafin ya isa, Zahra ta ɗauki kofin lemon tare da shanye lemon ciki kana ta wurgar da glass cup ɗin".

Zaro idanuwa gaba ki É—ayansu suka yi.

Take gaban kowanensu ya faÉ—i!.

Nan take Zahra ta faɗi a ƙasa.

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)
[12/14, 18:40] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣
_______________________
A matuƙar tsora ce Sooraj ya nufi inda Zahra ta faɗi da mugun sauri tare da ɗago ta ya fara jijjiga ta a razane da firgici yana mai faɗin Zahra me kika aikata haka? ya za ki sha wannan abunda kika san guba ce a ciki kina da hankali kuwa".

Hankalin Mami da sauran ƴan cikin falon ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Zahra ta fara fita daga cikin hayyacin ta. fusge jikin ta zahra ta yi daga jikin na Sooraj sannan ta miƙe tsaye a hankali nan take jiri ya ɗebe ta, ta faɗi a ƙasa . Da sauri Sooraj ya nufi inda take sannan ya dauke ta ya nufi waje da ita da mugun gudu saboda sauri ko ganin gabansa ba ya yi.

Kai tsaye inda motarsa yake ya nufa tare da nufar side ɗin ƴan zaman banza tare da buɗe ƙofar motar sannan ya saka Zahra a cikin mota sannan ya rufe ya juya tare da shiga mazaunin driver ya sa car key ya ta da motar tare da jan motan da gudu ya fita daga cikin masarautar. tafiya yake yi ba gaggautawa tare da wani irin gudun tuki tamkar ana tseren mota.

Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faÉ—a amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika É—auki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba".

Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali".

BuÉ—e idon ta guda É—aya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buÉ—e idonta gaba É—aya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?".

Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass É—in motan tare da tofar da poison din bakinta.

Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haÉ—iye poison din ba. "Wai dama ashe ba haÉ—iye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haÉ—iye?".

Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haÉ—iye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faÉ—a maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba".

girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haÉ—iye guban?".

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, É—azun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki".

"Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving.

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min".

Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba É—aya zan haÉ—a na kawo miki".

******************
Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah ka kaini gida Please".

Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu".

Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na Æ´an uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da Æ´an uwanki, za su samu dubbannin kuÉ—aÉ—en da ba za su misaltu ba".

"What!". Safira ta faÉ—a cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane Æ´an uwa ka ke magana a kai?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba".

Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?".

Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana É—aya daga cikin richest women in the world, ita É—in Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na".

"Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faÉ—a min waÉ—an nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba".

*************
"Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta".
Cewar warder.

Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe.
Chapter 56 · 0% Book details