← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 59

Sashe 32

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu zato suka ji an banko ƙofar cikin ɗakin. A zabure gaba ɗaya suka juya tareds sauke idanuwansu a kan matan da ke tsaye bakin ƙofa babu abin da suke ta faman yi sai tauna chewgum yayin da suka ɗora hannuwansu kan ƙugu. Sanye kansu yake da gashin ƙari wanda ya sauko musu har gadon baya yayinda ko ina na jikin su ke sanye da azurfa masu kyau da sheƙi. Kallo ɗaya za ka musu ka tabbatar da cewa su ma ƴaƴan wannan masarauta ne.

Ƙaraso wa ciki mata ukun suka yi sannan suka buga tsaki. Daya daga cikin su ce ta ce. "Ke Mami me ya sa har yanzu baki je kin wanke min panties ɗina ba?".

Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Mami su waye kuma waÉ—an nan almajiran?".

Kallonta Mami ta yi kana ta ce. "Su É—in ba almajirai ba ne, Æ´aÆ´an kishiyoyi na ne, Samira, Yusra, da Fasma".

A matuƙar fusa ce ƙaramar cikin su ta dubi Zahra ta ce. "Su wane ne almajiran, nan ɗin gidan ubanki ne. Tsaya ma tukun nan ke ɗin wace ce daga wane duniyar ki ka zo nan". Cewar Fasma.

Yusra ce ta dubi Fasma ta ce. "Dalla ƙyale ta Fasma zamu ji da ita daga baya. Yanzu wajan wannan banzar matar muka zo, ta zo ta wanke mana kayan mu, domin ni yau bana sha'awar saka kaya a cikin washin machine da hannu nake so a wanke mu".

Idan ran Zahra ya kai dubu to ya ɓaci. Cikin ɓacin rai ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku san da cewa wannan matar ba sa'ar iyayen ku mata ba ce, amma shi ne ku ke cewa ta zo ta wanke muku panties da kaya, lallai kamm banga ta zama ba a gidan nan domin daga yanzu ya kamata na soma aiki na".

Rai a ɓace su ukun suka tunkari in da Zahra take kana suka ce. "Eh mun aike ta ɗin wace ce ke da za ki dakatar da mu?".

Nuna su gaba ɗaya Zahra ta yi kana ta ce. "Zai iya kasance wa kun daɗe kuna yi mata abin da ranku ya gada ma, like mothers like daughters ko, to tun da na riga da sanya ƙafafu na cikin wannan masarautar komai ya zo ƙarshe domin kuwa ba zan bar koda iyayen ku mata su ƙara ci mata mutunci ba balle ku ƙananun ƙwari".

Nan take Samira ta saka ƙafarta wanda ke sanye da takalmi mai tsini ta taka ƙafar Mami da shi. Nan take Mami ta saki wani irin azababbiyar ƙara!.

Nan take ran Zahra ya ɓaci yayin da ta kai hannu tare da fizge gashin dokin da ke kan Samira sannan ta kama ƙwaƙwidon kan Samira kana ta kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu. Nan take su Yusra suka ja da baya.

Shafa kan Samira Zahra ta yi ta ce. "Wai dama ba gashin ku ba ne, ashe gashin doki ne, ji gashi kamar ammatar ɗan iska". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya sannan ta maida kallon ta kan Mami ta ce. "Mami kada ki damu za ki riɓanya hakan abinda ta yi miki kiyi mata times 2".

Girgiza kai Mami ta yi kana ta ce. "Ki rabu da ita Zahra, bana son matsala".

"A'a Mami ba zai yu ba, me ya sa koda yaushe waÉ—an da suke da shiru-shiru su haka fi raina wa ne?, ke sa'ar su ce da za su wai ki wani wanke musu kaya da panties, idan ba rashin tarbiya ba wa ye zai faÉ—i hakan?". Cewar Zahra.

Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra umarni nake baki ba shawara ba maza ki sake ta".

Jin hakan ya sa Zahra sakin gashin Samira tare da shinshina hannunta. Nan take ta ji wani mugun wari ya bugi hancin ta.

"Ya subha'anallahi!". Zahra ta furta kana ta ce. "Wannan kai ne ko kashin akuya?, ji wani wari da ke fita daga kan wannan Samira kamar mutacce alade. Chabb ashe duk gayun da iyayin na banza ne tun da ba'a iya tsaftace jiki".

Node Kai su ukun suka yi kana suka ce. "Za ki san mu ki ka taɓa wallahi yau kin taɓo wa kanki bala'i, kuma za ki gani". Suka faɗa tare da fita daga cikin ɗakin.

Duban su Zahra ta yi ta ce. "Zan ga alkhairy ba tsiyar ku ba, shegun yara kawai".

Su Samira na fita kuwa suka je suka sanar da su Gimbiya Saratu da Talatu duk abubuwan da Zahra ta yi musu. Nan take gaba ɗaya suka miƙe tsaye yayin da suka nufi kitchen daga mai ɗaukar wuƙa saime ɗaukar chokali. Yayin da su Yusrah kuma suka ɗauki wayar chaza suka nufi ɗakin Mami.

"Ke Zahra, nan fa ba kamar gidan ku ba ne, za su ya cutar da lafiyar ki ni kuma ba zan bari hakan ta faru ba, tun da ki ka ji sun ce za ki gani to sun tafi ne su haÉ—a dabar su za su iya cutar da ke, ya kamata ki bar masarautar nan yanzu".
Cewar Mami.

Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Mami ki barsu su zo dai-dai nake da kowaccen su, nayi da wanda yafi su ma balle su ƙananun tantirai. Jira nake su ƙaraso a nan za su tabbatar da cewa Allah ɗaya ne, domin duk saina koya musu hankali".

Ta faɗa tana mai hango dorina a ajiye kan table. Da sauri ta nufi in da dorinan take tare da ɗauka ta riƙe a hannunta tana mai jiran shigowar su Samira.

********************
💃💃💃💃💃💃💃💃
*KAI ZAHRA KINA ƘAMSHI MUNA BINKI DA UMRAH, INA YINKI OVER😂, MA ZA KIYI MANA MAGANIN SU. SU SAMIRA JIKIN KU ZAI FAƊA MUKU DOMIN ZAHRA BA ABAR RAINA WA BACE. ALIYU DA KUMA UMAR FA SUN RIKICE, SUN KASA GANE SAFEERA DA AMRAH. KOYA ZA TA KASANCE MUJE DAI ZUWA💃💃💃.*

*KADA KU MANTA DA LIKING, SHARING DA KUMA COMMENTS FISABILILLAH🌹🫠🫠🥰💞*

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣3️⃣▶️3️⃣4️⃣
*_________________________________________________*
Saida su Gimbiya Saratu suka zo dai-dai lokacin da za su shiga part É—in Mami ne suka ci karo da Junaid.

Shan gabansu Junaid ya yi sannan ya dube su ya ce. "Mene ne ku ke shirin yi haka?". Maida kallonsa ya yi kan Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Ammi what's going on?, kar dai wajan Mami za ku je?".

Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Koma wajan ta zamu je ina ruwan ka?, maza ka bamu hanya mu shiga. Har ma ta kai da har za ta kawo wata Æ´ar aiki cikin fadan nan kuma ta saka Æ´ar aikinta ta É—aga hannu ta mari Samira saboda ta cika tangararriyar Æ´ar iska".

Fashe wa da kuka Samira ta yi ta ce. "Wallahi yahya kome za ka yi ba zan rabu da ita ba, É—aga hannu da ta yi ta mare ni kawai ka bamu hanya mu shiga don wallahi saina yi mata tsinannen duka".

Sauke ajiyan zuciya Junaid ya yi sannan ya ce. "Kun san dai mai martaba yana nan. Kuma idan har ya ji abin da ku ke shirin aikata wa to ran mu ne gaba ɗaya zai ɓaci. Hanyar zaman lafiya a bita da shekara. Yanzu me ku ke so ita ƴar aikin ta yi muku?".

Amsa Gimbiya Talatu ta bashi da cewa. "In dai tana so mu rabu da ita to dole ne ta zo ta durƙusawa har ƙasan gwiwowinta ta bawa Samira haƙuri kuma bayan nan za ta wanke musu kayan su. Wannan shi ne". Ta ƙarashe maganar hannunta riƙe da ƙugunta

Furzar da iska Junaid ya yi waje, sannan ya dube su ya ce. "Shi ke nen kuje ku zauna a parlour zan kira ta za ta zo ta baku haƙuri gaba ɗaya har da ma ita Samiran".

Ya faɗa yana mai shige wa part ɗin Mami sallama riƙe a bakin sa.

Su Gimbiya Saratu kuwa jin abin da Junaid ya faÉ—a ya sanya suka koma parlour tare da zaman jiran fitowar Zahra.

Ƙarasawa ciki Junaid ya yo yayin da Zahra ta bishi da kallo. Murmushi Mami ta yi ta ce. "Junaid kaine a wannan lokacin".

Cikin jim kunya ya ce. "Eh Mami ni ne". Ya faÉ—a yana mai maida kallonsa kan Zahra.

Mamaki ne ya kama shi ganin dorina kan hannun Zahra.

Baki sake ya bita da kallo sannan ya ce. "ke kuma me ki ke da dorina?, me za ki yi da shi?".

Kallonsa Zahra ta yi sannan ta bashi amsa da cewa. "Zan daki ƙannen ka da shi ne, ko za ka rama musu?".

Kawar da kai Junaid ya yi gefe cikin jin haushin furucinta ya ce. "Ki fito babban parlour yanzu nan ko kuma ranki ya ɓaci". Yana kaiwa nan ya fice ya bar musu ɗakin.

Dogon tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza, ni gaba ɗaya ma zaman magarƙamar ma ya fi ƴanci a kan nan wajan".

Binta da kallo Mami ta yi ta ce. "Kije Zahra zai iya yiwu wa sun kai ƙarar ki wajan mai martaba".

Zama Zahra ta yi kan kujera ta ce. "Ni babu in da zani ina nan tare da ke".

Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi haƙuri ki tashi ki je ko kuma mu je tare kinji ni".

"Shi ke nen Mami zanje ne kawai saboda ke, amma da ba dan haka ba babu abin da zai sa na ɗau ƴan matan ƙafafuwa na naje wajan su".

Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta fita daga cikin ɗakin. Ganin hakan ya sa ita ma Mami ta bin bayan Zahra.
Chapter 32 · 0% Book details