Sashe 16
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Æangaren Umar kuwa ba abin da yake yi sai aikin kallonta, yayin da ya ji kanshi cikin sabon yanayi da shi kanshi bai san dalilin faruwar akan ba. Fitowa ya yi daga cikin motar tare da Æ™ura mata idanuwansa. "She is so pretty and cute". Ya faÉ—a cikin zuciyarsa.
Ɗago da idanuwanta Amrah ta yi tare da sauke su a kan na Umar. A matuƙar fusa ce ta ƙwace kanta daga riƙon da jami'an suka mata, yayin da ta fara dukansu tana ɗaga su sama tare da wurga dasu ƙasa.
Saida ta gama da su sannan ta fara yowa inda Umar yake. Saida ta je har gabansa da zimmar dukansa. Tsayawa ta yi chakk saboda ganin irin ƙwar jinin da ya yi mata.
Gurnani ta fara yi tana mai nuna dabba da suka buge. nan take ta fara hawaye tana dukan motan da ya bude dabban.
Jikin Umar ne ya yi sanyi yayin da ya ji jikinsa ya mutu. Kallon tufafin da ke jikinta ya yi. Ganin gaba ɗaya ganye ne sanye a jikinta akan ya ƙara tabbatar masa da cewa Amrah ƴar daji ce.
Jin kukan Amrah ya sa sauran namun jejin fitowa izuwa harabar wajan. Ganin Amrah durƙushe tana kuka, ya sa suka fara gurnani yayin da suka fara nufar inda Umar yake da zafin nama.
Ganin suna nufo inda yake ya sa Umar ya fara ja da baya-baya.
Ɗago da rinannun green eyes ɗin ta Amrah ta yi tare da sauke su akan namun jejin. ganin suna nufar inda Umar yake da zimmar illata shi ya sa ta sauri miƙe wa, yayin da ta tafi da gudu tare da shan gabansu.
Da sauri jami'an suka miƙe tsaye. Yayin da a dai-dai lokacin yan hukuman row suka ƙaraso wajan.
Dakatar da dabbobin Amrah ta yi da hannunta sannan ta ce da su. "Maza ku ja da baya, kada ku ce zaku cutar da shi, bada sane suka buge É—aya daga cikin Æ´an uwan mu ba, dan aka maza ku koma. In ba aka ba gaba É—aya rayuwar mu tana cikin hatsari".
Gani suka yi tana yin magana ba tare da fahimtar abin da take cewa ba.
"Sir Umar ka bamu dama domin mu kashe dukanin dabban dake cikin dajin nan, domin nan mallakin ka ne ba ta su ba".
Dakatar da shi Umar ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kada kuyi komai ba tare da izini na ba, gaba É—aya kuna under control ne don aka be careful. Maza ku tawo mu bar nan sannan yarinyar nan ku saka ta a mota ku tawo da ita".
"Yes Sir". gaba É—aya suka faÉ—a, yayin da suka nufi inda Amrah take tsaye tana faÉ—a wa dabbobi da su koma. Juyawa dabbobin suka yi tareda barin wajan.
Ba zato ta ji sun rirriƙe ta. Da sauri ta dube, sannan ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta.
A matuƙar hassale ta gantsara wa ɗaya daga cikin su cizo. Nan take ya saki wata iriyar azababbiyar ƙara. Buga tsalle Amrah ta yi tare da ƙwace kanta daga gare su.
FaÉ—uwa gaba É—aya jami'an suka yi. Ganin haka ya sa Amrah ta fara gudu yayin da ta fara aye wa kan manya-manyan bishiyun dake cikin dajin tsalle suka ga ta fara yi tamkar Æ´ar biri, tana aye wa kan bishiyu É—aya bayan É—aya.
Da sauri jami'an suka bi bayan ta. Sannan suka fara sakin harbi.
Ganin sun fara harbi ya sa Umar dube su yana mai cewa. "Don't shoot". Ko saurarensa basu yi ba aka suka ci gaba da harbin bishiyun domin su samu Amrah.
*********************
*Magarƙama*
"Gani nan naji ance wai kuna nema na". Zahra ta faÉ—a ba bu alamun tsoro a tattare da ita.
Tsayawa Æ´an sandan da warders suka yi suna kallonta. ÆŠaya daga cikin su ne ya ce. "Zahra wai me ya sa ki ke da wannan jiji da kai ne?".
Kallon wacce ta yi maganar Zahra ta yi sannan ta ce. "Ki tambayi wacce ta haife ni zata baki amsa".
Da kallon mamaki suka fara binta da shi. ÆŠaya daga cikin Æ´an sandan ne ya ce da ita. "Ta ya ya zata tambayi mamarki bayan bata raye?, koda yake dole ai a tambaye ta tun da uwa Æ´ar daba ita ma É—iya Æ´ar daba. Wannan dai gadon hali ku ka yi".
Danne fusho dake ƙoƙarin ta so mata Zahra ya yi sannan ta ce. "Ɗan sanda ka iya bakin ka, mahaifyata ba abar wasa bace, kada ka tunzurani na aikata abin da raina bai so ba".
Sakin baki É—an sandan ya yi yana kallonta. "Idan ban iya bakin nawa ba duka na za ki yi?. To ki sani cewa mahafiyar ki babbar sheÉ—aniya ce, ba bu wanda ya kaita sheÉ—anci kuma sannan ita ce sanadin mutuwan rayukan mutane a lokacin baya. Don haka ko kina so ko bakya so da kallon Æ´ar sheÉ—aniya zamu dinga kallon ki. Ni a duniyar nan akwai wacce ta kai Mrs Laila arha kuwa?, domin ko a gidan karuwai albarka".
Nan take idanuwan Zahra suka kaɗa suka yi jajir. Take ta sak wata iriyar ƙara mai matuƙar razanarwa!.
Shaƙe wuyar ɗan sandan ta yi da dukkanin ƙarfin ta. Tare da ɗaukar hannunta ta ƙwaɗa masa mari. Tare da fara naushin bakin sa da mugun ƙarfi.
Ganin abin da ke faruwa ya sanya sauran jami'an suka ƙaraso wajan, yayin da suka fara ririƙe ta tare da ƙoƙarin ƙwace ɗan sandan daga hannun Zahra. Da sauri suma ƴan magarƙamar suka ƙarasa wajan.
Hajiya Binta dake cutting grass ce ta hango taruwa mutane. Da sauri ta saki gatari da take cutting da shi tare da nufa wajan.
Riƙe shi Zahra ta yi ƙamm a hannunta yayin da ta ci gaba da nausar bakin sa. Cikin huci ta dube shi sannan ta ce.
"Mahaifiyata ce take da arha?, wato mahaifiyata ce ko a gidan karuwai
albarka ko?, yau za ka gane kuranka. Ka sani cewa zagin mahaifiyata da kay shi ne kuskuren da baka taɓa aikatawa ba a rayuwarka domin saina yi maka dukan kawu wuka, saina yi maka dukan da ko ƙauyen ku ka koma da ƙyar yaran ka su gane cewa kai babansu ne". Tana kaiwa nan ta ci gaba da sambaɗansa saida ta yi masa sambaɗe baɗe, sannan ta ci ka shi.
Isa wajan Hajiya Binta ta yi tare da janyo Zahra sannan ta kwashe ta da mari. Dafe ƙuncin ta Zahra ta yi, karo na farko a rayuwarta da hajiya Binta ta taɓa lafiya jikinta.
A matuƙar fusa ce Hajiya Binta ta kalleta sannan ta ce. "Me yake damunki Zahra?, shin kinyi hauka ne?, ɗan sanda da ki ka daka kin san abin da akan zata haifar?, dole ne na ɗau mataki a kan ki in ba aka ba za ki jawo min abin kunya ne".
ÆŠaya daga cikin Æ´an sandan ne ya ce. "Ba saikin É—au mataki ba, mu da kanmu zamu É—auki mataki a kanta. Don haka tun da harta sake ta É—ora hannunta a kan É—an sanda dole ta fuskanci mummunan hukunci. Jami'ai maza ku kama ta ku wuce da ita offishi sannan ku saka ta a cell yau saita gane cewar Allah É—aya ne".
Jin haka ya sa Hajiya Binta ta fara basu haƙuri. Ko kallonta basu yi ba haka suka kama Zahra tare da nufar inda motocin ƴan sanda suke. Ba tare da turjiya ba Zahra ta shiga cikin motan.
Shige wa suma suka yi cikin motan yayin da suka cinciɓi ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka sannan suka saka shi cikin mota. Fice wa suka yi daga cikin magarƙamar. A sa'in da motar da aka saka ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka ta wuce asibiti. Yayin da kuma sauram motocin suka wuce police station.
Suna isa chan suka fito daga cikin motocin yayin da suka kama Zahra sannan suka shigar da ita cikin police station tare da jefa ta cikin cell.
*****************
Æangaren Amrah kuwa neman ta suka yi suka rasa a cikin jejin.
Alama Umar ya yi musu da su koma cikin mota. Koma wa suka yi cikin mota gaba É—aya yayin da suka tada mota tare da barin harabar dajin.
Kai tsaye gida suka koma yayin da suka zayyane wa mahaifin Umar duk abubuwan da suka faru.
************************
*AMERICA*
Cikin harshen turanci ya dubi abokin nasa ya ce. "John ya kamata ka manta da abin da ya faru, Diana bata yi akan da son ranta ba, ya kamata ka manta da komai". Cewar abokin nasa.
Kallonsa John ya yi sannan ya ce. "A kan mene ne zai sa na rabi ita?, a gaban jama'a ta ɗauki hannu sannan ta kwashe ni da mari, ko zan yafe komai ba zan taɓa yafe wannan abin da ta yi min ba. Ya zama dole na ɗauki fansar abin da ta aikata, saina shayar da ita azabar da har abada ba zata manta da ni ba. Ya zama dole na aure ta domin ita ɗin tawa ce ta ni kaɗai, bayan na aure ta zan gana mata azaba, ba dai tana ji da kanta ba, ni nan zan sauke mata jiji da kanta".
Yana kaiwa nan ya fice daga cikin É—akin wanda ya gauraye da hayakin shisha.
******
Gaba ɗaya Aliyu ya rasa me kai masa dad'i. A duk sa'in da Safeera ta zo ta wuce ta gefen sa sai ya ga tamkar ya santa. Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗaukar wayar ya yi ya ga numbern Nigeria ke kiran shi. sunan yallaɓai ne bayyane kan screen ɗin wayar. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa. "Hello yallaɓai".
Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Ya batun maganar da muka yi da kai Aliyu?, kace za ka je ka ga MK a magarƙama har yanzu baka dawo bane?".
Cikin rashin fahimtar maganarsa Aliyu ya ce. "Ni kuma?, ni yaushe na ce zan je magarƙama?. Ni fa a halin yanzu ina America kwata-kwata bana ƙasar Nigeria, don aka ka bari idan na dawo Nigeria zamu yi magana". Yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Sakin baki mutumin ya yi yana mai kallon wayar dake hannunsa. "Lallai Aliyu ka cika É—an rainin wayo, za ka gane kuranka ne".
*******
Fitowa Safeera ta yi cikin ƙananun kaya wanda suka karɓi jikin ta tare da fara takawa tana nufar parlour.