← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 59

Sashe 27

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ɗayan ɓangaren Mk ya bashi amsa da cewa. "ƙwarai da gaske yaranka tare da matarka Laila gaba ɗaya suna raye".

Ajiyan zuciya dattijon ya sauke!, tare da yin hamdala sannan ya ce. "Alhamdulillah Allah na gode da ya kasance matata tare da yarana suna raye. Dan Allah ka tabbatar da kana kula da shige da ficen su, bana son su kasance cikin kaÉ—aici kowanen ka shiga cikin rayuwarta domin kare ta, kai É—in jami'i na ne kuma na yarda da kai É—ari bisa É—ari, ina so kayi min wannan alfarman dan Allah".

Daga ɗayan ɓangaren Mk ya ce. "Kai ɗin kamar walihi ka ke a gare ni Sir Bashir, a kan me ya sa ba zan yi abin da zai faranta maka ba, bayan kuma kai ka faranta mu tare da iyalaina, ka fito da ni daga cikin magarƙama kuma ka sa an maida ni kan aiki na, dole nayi maka duk abin da ka ke so. In sha Allah zan shiga rayuwar kowacce a cikin su domin kare su. Ba zan taɓa barin Gov.Musa Muhammad ya ci galaba ba". Yana kaiwa nan ya katse wayar.

Ajiyan zuciya Sir Bashir ya sauke!, sannan ya kwanta kan lallausar gadon sa ya ce. "Tabbas na aikata babban kuskure, na san ba za ki yafe min ba Laila, duk abin da ya faru ba laifi na ba ne, ban zo nan ba domin na sa a cutar da ke, na zo ne kawai saboda mahaifin ki ya bani umarnin yin hakan. Ina matuƙar ƙaunar ki matata".

**********************
*NIGERIA*
Safeera kuwa, bayan likita ya duba ta ya ba ta magani ta sha. Cikin ƙankanin lokaci bacci ya yi hawon gaba da ita. Yayinda Grandma ta saka su Zuwaira da Salma su yi mata farfesun kaji".

Fita suka yi suka bar iya Aliyu da kuma Safeera a ciki É—akin.

Tsaya wa Aliyu ya yi yana kallon kyakkyawar fuskar Safeera. Tagumi ya yi cikin ransa ya ce. "Yarinyar nan ba dai kyau ba, duk wanda ya same ki gaskiya ya yi sa'ar mata". Ya faÉ—a cikin ransa yayin da ya ci gaba da kallo yadda take fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali.

******
Bayan Umar ya dawo ya tarar da su Khairiya su haÉ—a wa Amrah shayin. Shiga cikin É—akin suka yi a tare. Cikin mamaki kuwa suka tarar ba ta cikin É—akin.

Zaro idanuwa waje gaba É—aya suka yi yayin da Ramlat ta ce. "Ina kuma ta je?".

Dafe kansa Umar ya yi sannan ya ce da su. "Maza ku bincika cikin gidan nan gaba É—aya, na san ba za ta wuce cikin nan ba".

Haka gaba É—aya suka bazu cikin gidan suna nemanta, yayin da Umar ya saka jami'ai suma suka shiga bincika wa.

Neman duniya sunyi amma basu ganta ba.

Nan take wani tunani ya faÉ—o wa Umar. Da sauri ya nufi garden yayin da suma su Usman suka bishi a baya. Dube-dube suka fara yi.

Tsayawa Umar ya yi chakk jin musharin mutum. Ganin ya tsaya ya sa suma suka tsaya. Shiru kowanensu ya yi.

Kasa kunne Umar ya yi domin jin ta ina musharin yake fitowa.

Babu zato ya ji Khairiya da Ramlat sun fasa ihuu!.

Da sauri ya dube su sannan ya ce. "Mene ne ya faru?".

Baki na rawa suka haÉ—a baki wajan faÉ—in. "Ka duba sama kan bishiya".

Kamar yadda suka ce babu musu Umar ya duba sama. Abin da ya gani ne ya bashi mamaki. Ganin Amrah ya yi kwance kan bishiya sai sharɓan baccin ta take.

Dafe kansa Umar ya yi ya ce. "Ya salam!, wannan yarinyar ta riga da ta saba da zaman jeji, idan ba nan na maida da ta ba ba za ta taɓa iya zama damu ba".

"Ko ta ya ya ma ta iya hawa kan bishiyar nan". Usman ya faÉ—a.

Duban jami'an gidan Umar ya yi sannan ya saka su su ɗauko masa igiya. Kamar yadda ya umarta haka suka je suka ɗauko igiya mai matuƙar kauri sannan suka ɗaure cikin bishiya da shi tare da riƙe shi gamm a hannun su.

Kama igiyar Umar ya yi tare da fara hawa kan bishiyar. Yayin da jami'an suka ƙara riƙe igiyar sosai a hannunsu.

Jan igiyar Umar ya fara yi yana mai hawa kan bishiyar har ya isa in da Amrah take sannan ya janyo ta.

Zumbur ta miƙe tsaye. Nan take Umar ya ja da baya. Cikin rashin sa'a kuwa igiyar ta tsinƙe. Nan take su Ramlat suka saki ihuu domin kuwa Umar yana shirin faɗo wa ne daga saman bishiyan.

Ganin yana ƙoƙarin faɗi ƙasa ya sa Amrah saurin riƙe masa hannu yayin da ta fara jan shi kan bishiyar. Hawa da shi ta yi kan bishiyar yayin da Umar ya shiga sauke ajiyan zuciya.

Kallonta ya yi sannan ta ce. "Maza zo mu sauka ƙasa, bana son wani abu ya same ki, za ki iya faɗo wa ki karye".

Girgiza kai Amrah ta yi. Babu zato ya ga ta dira ƙasa ba tare da tsoro ba.

Zaro idanuwa waje gaba É—aya suka yi ganin yadda ta dira ba tare da wani tsoro ba.

Furzar da iska mai zafi Umar ya yi ciki ransa ta ce. "To ta ina zan fara sauka daga kan bishiyar nan?, hanya ban jawo ka kaina ba kuwa?".

Kallon saman bishiyar Amrah ta yi sannan ta yi mai nuni da ya sauko.

Ba tare da wani tsoro ba Umar ya fara bi ta jikin bishiyar yana sauko wa a hankali.

Kai hannunsa Umar ya yi domin riƙe bishiyar sosai. Cikin rashin sa'a hannun sa ya suɓuce ya tafi ƙasa daga kan bishiyar.

"Yahya Umar!". Gaba É—aya suka furta.

Ganin ya kusan faɗo wa ya sa Amrah ta buga tsalle tamkar ƴar biri tare da chafko Umar sannan ta ajiye shi ƙasa".

Sauke ajiyan zuciya suka shiga yi tare da yin hamdala.

Kallon Amrah su Khairiya suka tsaya yi sannan suka ce. "Wannan ita ce ma mace mai kamar maza, irin wannan ƙarfi haka, daga gani ƴar daji ce".

************
"Ta ya ya hakan za ta kasance?, farko na shiga room 8 na ga Amrah q ciki, bayan na kuma koma wa cikin room É—in da na baro Amrah na kuma ganinta a ciki. Tabbas babu ta yacce hakan zai yiwu dole dai mutum biyu na gani. Amrah green eyes ne da ita, sannan kuma Æ´aÆ´an Mrs Laila da na sani mai green eyes ne sai blue eyes, dole dai ta room 8 blue eyes ne da ita. Idan kuwa har da gaske ne blue eyes ne da ita to babu tantama Æ´aÆ´an Mrs Laila ne".

Aka Nurse Nadiya ta shiga yin magana ita É—aya kamar zautacciya.

**********
*Daji*.
Babu abin da ka ke gani a wajan sai mata wanda aka ɗaɗɗaure musu hannu da baki. Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da cewa ba ƙaramin jigata suka yi ba. Yayinda ɓangare guda allurori ne a ƙasa wanda aka yi musu domin a kawar musu da tunani. Kuka sosai suke yi. Ɓangare daya kuma maza ne hannunsu riƙe da bindigogi yayin da fuskokinsu gaba ɗaya yake a rufe.

Baka iya ganin komai na fuskarsu sai iya ƙwayar idanuwansu.

"Your excellence, matan da muka yi kidnapping yanzu za su kai kumanin 250. Yanzu muna jiran cewar ka ne domin a je a siyar da su a kasuwa, za'a mu yi safarar su ne zuwa ƙasashen waje yayin da kai kuma kuɗaɗe ne kawai za su dinga shigo maka".

Murmushi mahaifin Umar ya yi sannan ya ce. "Well done guy's, aikin ku na kyau yadda ya kamata. Maza ku sa su a Bus, zan saka a ƙaro muku bus domin Bus ɗaya ba zai isa ba. Sannan kuma kamar yadda muke yi abun nan cikin sirri bana son ɗana da kuma ƴan sanda su sani, domin idan suka sani abun ba zai yi min daɗi ba".

"Yes Sir". Mutumi ya faÉ—a.

Ɗaya daga cikin matan wajan ne ta yi nasarar kunce kanta da kuma kunce bakin ta. Zumbur ta miƙe tsaye tare da kallon Gov. Musa Muhammad sannan ya ce.

"Kai mugu azzalumi, ka sani cewa ƙarshen ka ba zai yi kyau ba, kana ɗaukar mu da ƴaƴan mu wanda muka damƙa maka su a matsayin amana kana safarar su izuwa ƙasashen waje". Duban kanta dattijuwar ta yi tare da tsugunna kan gwiwowinta ta ce. "Da wannan hannun nawa na ɗauki dutse na bugi Mrs Laila da shi. Tabbas na aikata kuskure, nayi zaton Mrs Laila ita ce muguwa ashe kaine asalin tantiri, ka ɓata mata suna a idanun duniya, ka sani cewa koda mun barka Allah ba zai barka ba. Kuma ka sani cewa Allah saiya tona maka asiri".

Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi tare da kwashe wa da dariya.

***********
Ɓangaren Zahra kuwa bayan anyi mata treatment ta samu bacci ya ɗebe ta. Saida ta ɗau hawanni biyu tana bacci kana daga bisani ta buɗe idanuwanta.

Nan take idanuwanta suka sauka a kan mahaukaciyar da ta gani kwanaki.

Miƙe wa ta yi zaune tana mai kallon matar da ke zaune kusa da ita.

Shafa fuskarta mahaukaciyar ta yi murmushi É—auke kan fuskar ta.

Lokaci ɗaya Zahra ta ji ƙaunar matar ya shiga ranta ba tare da sani dalilin hakan ba.

Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Wace ce ke?, me ya sa a koda yaushe ki ka ƙoƙarin zuwa in da nake?, shin kin san ni ne?".

Girgiza kai kawai mahaukaciyar ta yi.

Shigowa likitoci suka yi yayin da suka kama hannun mahaukaciyar domi fitar da ita. Fuffuzgewa mahaukaciyar ta fara yi.

Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "ku ƙyale ta mana ya za ku wani kamata kamar yarinya za ku fita da ita, wannan sam ba adalci ba ne".

Kallonta É—aya daga cikin likitocin ya yi sannan ya ce. "Ita É—in fa mahaukaciya ce, yanzu shekaru ashirin kenen tana cikin wannan asibitin. Kuma yanzu aka ma magani zamu je mu ba ta bawai cutar da ita zamu yi ba".
Chapter 27 · 0% Book details