Sashe 15
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyan zuciya nurse ɗin ta sauke sannan ta ce. "Komai da ki ke gani a duniyar nan muƙaddari ne, ki ci-gaba da kai kukan ki ga ubangiji ko za ki ji sassaucin abin da ke damun ki".
"Shi ke ne". Kawai nurse Nadiya ta faɗa sannan ta ya miƙe tsaye tare da koma wa baki aikin ta.
**************************
*DAJI*
Kwance Amrah take kan jibgegen bishiya, yayin da iska mai ni'ima ke kaÉ—awa yana shiga kowane sashi na jikinta. Lumshe green eyes É—inta tare da buÉ—e su gaba É—aya. Kallon aku wato parrot dake kusa da ita ta yi sannan ta ce. "Shin bayan wannan duniya tawa akwai wata duniyar da ta kai wannan kyau?".
Girgiza mata kai akun ya yi. Jinjina kai Amrah ta yi sannan ta ce. "Toh indai haka ne zan so in ga ya birni yake, ni dai na san ba za ta kai duniyata kyau ba. Kuma sannan su ya halittar su take?". Ta faɗa tana mai ɗora hannunta kan haɓar ta.
Jin kururuwan dabbobi ya sa ta saurin miƙe wa daga kan bishiyar. Yayin da ta yi tsalle ɗaya ta dira daga kan bishiyan.
Gudu ta fara yi tamkar wata zakanya, yayin da ta fara bin hanyar inda take jiyo kururuwan dabbobin.
Daga chan nesa ta hango kura da dila suna faɗa a tsakaninsu yayin da suke kaiwa juna hari. Ganin hakan da Amrah ta yi ya sa ta ƙara saurin gudun nata. Ganin kura tana ƙoƙarin kaiwa dila cizo ya sa Amrah buga tsalle ɗaya tare da shiga tsakiyar su sannan ta yi musu alamu da hannu da su dakata.
Chakk suka tsaya yayin da sauran. A fusa ce ta dubi su biyun ta ce.
"Mene ne yake damun ku?, shin kun rasa tunanin ku ne?, me ya sa a koda yaushe ku ke yawan faɗa ne?, shin ba zai yu ku zauna lafiya bane?. To daga yau ku saurare ni muddin na ƙara ganin kun ƙara faɗa saina yi muku hukuncin da baku taɓa tsanmani ba sannan daga ranar ba zan ƙara kula ku ba".
Maida kallonta ta yi kan dila sannan ta ce. "Ke kuma kin san da cewa kura ya fi ƙarfin ki amma ki ke ƙoƙarin faɗa da shi, yanzu idan ku ka je ku ka illatar da kanku fa?. to ku sani cews gaba ɗaya zan ɓata muku rai idan baku daina faɗa ba". Tana kaiwa nan ta juya musu baya alamun ta yi fushi da su.
Nan take gaba ɗaya suka sunkuyar da kawunansu tare da nufar inda take. Shafa jikin ta suka fara yi yayin da suka je gaban ta tare da ɗurƙusawa, sannan suka sunkuyar da kai ƙasa alamun suna bata haƙuri.
Ganin sun sunkuyar da kai ƙasa ya sa ta nufar inda suke tare da ɗurƙusawa kan gwiwowinta sannan ta janyo su jikinta ta ce. "Ku sani cewa kune komai nawa, kune dangi da kuma iyaye na, ba zan juri naga kuna faɗa a tsakanin ku ba, ku daina kunji ko".
Maida kallonta ta yi kan sauran namun jejin sannan ta ce. "Maza gaba É—aya ku zo mu yi wasan tsere ko. Idan na riga ku zaku É—auke ni gaba É—aya kunji ko. Dan haka ku tawo muje mu yi wasa". Duk abin da take faÉ—a da yaren dabbobi take yi.
Da gudu ta bar wajan fuskarta É—auke da annashuwa. ganin hakan ya sa suma namun jejin suka bita da gudu.
************************
"Mai gida ya kamata a ce ka yafe wa Æ´arka, ita É—in fa Æ´ar mu ce. Yanzu haka ta riga da ta rasu, bai kamata a ce har yanzu kana fushi da ita ba".
Cewar wata dattijuwar mata.
Ɗago da kansa mutumin dake kan wheel chair ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Yafiya?, kina nufin na yafe wa Laila cin mutunci da zubar mana da kima da ta yi a shekarun baya?. Abun da ta yi ya daɗe da faruwa amma ina jin shi sabo ne a cikin zuciyata, kin san dai ba bu abin da na fi tsana sama da na ga mutunci na da na ahalina ya zube. Ta ci amanata, samm bata cancanci na yafe mata ba, ni na tsani ma jin sunanta a inda nake, kada ki ƙara kawo min irin wannan maganar na faɗa miki. Kuma abin da ta yi wanda ya sa a yanzu jika na Aliyu yake fama da cutar mantau, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ba zan taɓa yafe mata ba, dan haka ki ƙyale ni".
Girgiza kai matar ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen, amma ka sani cewa cutar mantau na Aliyu ba laifin Laila bane, tsautsayi ne kawai bada gangan ba, dan Allah a matsayina na uwa nake roƙan ka, dan Allah ka yafe wa Laila ko ruhinta sai samu salama". Ta ƙarashe maganar hawaye na gangaro kan fuskarta.
Nuna ta dattijon dake kan wheel chair ya yi sannan ya ce. "Amina kada ki kuskure ki fusa ta ni nayi miki abin da ba za ki ji daɗin sa ba. Ta ya ya za ki ce ba ita ce silar cutar mantau ɗin Aliyu ba, shi kanshi mijin ta tun da haka kaita magarƙama bai taɓa zuwa ya duba ta, saboda ya san ba mutumiyar kirki bace. Laila ta karya min duk wani yarda ta a kanta, ita ce dalilin zama na a kan wannan wheel chair ɗin. Laila ta ci amanar yardar da nayi mata, ta zalince ni, duk dukiya da companies da take dasu basu ishe ta ba, sai ta haɗa da miyagun laifuka, eh?, na ce duk basu ishe ta ba sai ta haɗa da safaran yaran mutane. ta saka bana iya fita saboda abin kunyar da ta janyo wa wannan ahalin. Har abada ba zan yafe mata abin da ta yi ba".
"Aba mai gida, Allah ma muna yi masa laifi yana yafe mana balle mutum ɗan adam. Ni ina da yaƙinin cewa Laila bata aikata kowane laifi ba, ita ɗin fa mai gaskiya ce da riƙon amana. Amma ba bu damuwa na san dai wata rana gaskiya zata yi halinta, kuma ramin ƙarya ƙurarre ne dole dai wata ran gaskiya zata fito".
***********************
"What!, Umar ka san abin da ka ke faɗa kuwa?, kana nufin a yau zamu je wannan dajin?, yau ɗin nan da ka dawo ku hutawa baka yi ba, ka bari zuwa next week mana, ka ga kafin nan gaba ɗaya engineers da architecture da kayan aiki za su kasance a shirye. Wannan wajan naka ne amma akwai namun jejin dake zaune a cikin dajin, waje ne mai matuƙar hatsarin gaske, ba zai yiwu kaje ba. Kawai kayi zaman ka a gida in ya so idan haka kori namun jejin wajan sai ka zafi filin da ka ke so a wajan".
Ɗago kai Umar ya yi ya kalli mahaifin nasa sannan ya ce. "Saboda me za'a kari dabbobin dake zama a cikin dajin?, su kenen basu da ƴanci na rayuwa ne ko me?, kana ji ba za'a taɓa ɓangaren su ba, za'a gina company ne a wani guri a cikin dajin amma banda ban yarda a taɓa ɓangaren inda dabbobin suke zama ba, kuma a yau nake so na je na ga wajan".
"Amma Umar wajan nan fa gaba ki É—aya mallakin ka ne, kuma gaba É—aya wajan ne namun jeji ke zama, ko dai za ka sauya wani jejin da ban muje na Kano?".
Amsa Umar ya ba shi da cewa. "A'a, ni wannan dajin nake so, kuma yanzu nake so na je".
"Shi ke nen Umar, tun da haka ka ke so zan yi wa engineers magana za'a tafi da kayan aiki domin a fara gudanar da aikin company". Cewar mahaifin na shi.
Bayan hawanin biyu da misalin ƙarfen biyar na yamma gaba ɗaya suka shirya tsaff yayin da haka haɗa rukuni na jami'ai da bindigogi suka nufi hanyar dajin.
Tun da suka fara tafiya Umar ke jin gabansa na tsananta faɗuwa, ya rasa me ke masa daɗi, gaba ɗaya ya shiga wani irin yanayi. Lokaci ƙalilan ya yi musu a cikin dajin su Amrah.
Shiga suka fara yi da motoci cikin dajin yayin da suke tattaka itacuwa da ganyayyaki saboda ba bu wata hanya ta mota a wannan jejin. Suna cikin tafiya ƙwatsam suka buge ɗaya daga cikin dabbobin dake bin Amrah a baya. Tsayawa motocin suka yi a tare. Sannan gaba ɗayansu suka fito daga cikin motan banda Umar wanda ke zaune a bayan mota securities sun zagaye motar da yake ciki da bindigogi.
Juyawa Amrah ta yi sakamakon jin ƙaran ɗaya daga cikin namun jejin da ta yi. Zaro idanuwa ta yi waje tare da sakin wani irin ƙara! mai razanarwa.
*TOH FAH YANZU HAKE YINTA, KOYA ZATA KASANCE TSAKANIN AMRAH DA UMAR?. MUJE DAI ZUWA*
KADA KU MANTA DA COMMENTS DA KUMA SHARING PLEASE 🙠ðŸ™
ALƘALAMIN âœï¸
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)
Follow the 💖 A'ISHA M.Bâœï¸ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*ðŸªðŸŒŽðŸª.
Daji 🌲
Magarƙama🢠da kuma
BirniðŸ™ï¸
WRITTEN & DIRECTED BY âœï¸ A'ISHA M.B 💞💞💞
(ZinariyarðŸ§â€â™€ï¸Jajirtattu)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 âœï¸
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Æ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauÆ™i_.âœï¸
*DIAMOND 💎 STARâ*
*LADIES ðŸ§â€â™€ï¸ðŸ§ðŸ¼â€â™€ï¸ðŸ§â€â™€ï¸*
*(We stand together)*
ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤
بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1ï¸âƒ£5ï¸âƒ£â–¶ï¸1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
*_________________________________________________*
Da mugun gudu Amrah ta isa inda dabban yake, sannan ta fara duba shi, ganin cewa ba bu alamun rai a tattare da shi, ya sa ta ɗago da green eyes ɗin ta wanda suka ƙara rinewa saboda ɓacin rai sannan ta ɗora a kansu.
Gurnani Amrah ta fara yi. Da sauri ta miƙe tare da nufar inda suke. Ganin tana nufo inda suke ya sa jami'an suka yi saurin zagaye motar Umar yayin da suka saita bindigun su kanta.
Tsalle ɗaya Amrah ta yi tare da dira kan motan da Umar ke ciki. Zabura gaba ɗayansu suka yi. Nan take suka janyo ta ƙasa ta faɗi, sannan suka fara ririƙe ta.