← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 59

Sashe 43

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin takaici Zahra ta yi sannan ya ce. "A hakan ya ganni ya ce yana so, sannan kuma kada ka manta so babu ruwanshi da ballagazanci ko rashin kamun kai ko kuma kuɗi ko iko, ka gane Yarima, sannan kuma koma dai mene ne ina ruwan ka?, meya shafe ka da hakan?, wallahi karka kaini bango na faɗa maka maganar da za ka kwana ka tashi ba za ka manta ba, kada ka sa na faɗa maka maganar da za ta sanya ka rashin lafiya harta kai ga an kaila ƙasar waje operation ɗin zuciya, na gaya maka domin kuwa idan na gaya maka magana sai zuciyar ka ta fito ta bugi ƙasa sannan ta koma".

Jinjina kai Sooraj ta yi sannan ta ce. "Kin san kuwa da wa ki ke magana?, ni Sooraj ki ke gaya wa aka?. Shi ke nen kije ki girka duk abin da ki ka ci yanzu nan kuma za ki yi".

Harara Zahra ta galla masa ba tare da ya sani ba sannan ta ce. "Naji".

Ta faɗa tana mai shige wa ciki. Girgiza kai Sooraj ya yi yana mai ayyana irin ƙuntata wa Zahra da zai yi, zai nuna mata banbamcin ɗan sarauta da kuma ƴar aiki". Haka ya cigaba da ayyana maganganu sa kana daga bisani ya shiga ciki.

Zahra kuwa ba ta zarce ko ina ba sai cikin kitchen ajiye kayayyakin ta yi kan table sannan ta yi jugum tare da bin kayan da kallo.

"Zahra kin taro wa kanki match, yanzu ta ina za ki iya girka abin da ki ka ci". Su Samrah suka faÉ—a suna mai kwashe wa da dariya.

Binsu da kallo Zahra ta yi rai ɓace ta ce. "Zan yi kuma za ku gani, an gaya muku ban iya girki ba ne, to zan yi ma wanda yafi wannan dad'i, maza ku ɓace min daga gani".
Ta ƙarashe maganar tana mai maida kallonta kan ingredients ɗin.

Fice wa su Samrah suka yi suka barta a kitchen É—in.

Zama Zahra ta yi tana mai ɗora hannayenta guda biyu a kai sannan ta ce. "Na shiga uku!, yanzu ta ina zan fara?, ni da ko girki ban taɓa yi ba ta ina zan iya wannan abincin, gashi ba'a taɓa girki a gaba na ba balle na iya, yanzu ya zan yi. Kuma idan ban yi ba hukunci wannan Sooraj ɗin zai yanke min, ya kamata nayi abu. To me ma zan yi?". Ta tambayi kanta.

Ɗaukar babban tukunya ta yi tare da ɗora wa kan gas cooker. Dafe kanta ta yi tana mai nazarin mene ne abu na gaba da za ta yi. Nan ta ɗauki man gyaɗa tare da zuba wa cikin tukunyar sannan ta zuba kayan haɗi da wanda ta san mene ne da wanda ba ta san mene ne ba duk ta zuba tare da zuba yaji mai matuƙar yawan gaske, sannan ta yanka albasa ta zuba a ciki tare da kwara wa man gyaɗa ɗin ruwa. Take tukunyar ta kama ci da wuta mai matuƙar ƙarfi.

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai ƙoƙarin rage gas ɗin amma ina wutan ba zai ba ta damar kai hannunta wajan gas cooker domin ta rage ba.

"Yanzu ya zan yi na rage wutan nan?, ko na zuba masa ruwa ne?". Ta tambayi kanta.

Girgiza kai kawai ta yi tare da cewa. "Kawai bara na rage da kai na". Ta faɗa tana mai kai hannunta wajan gas ɗin. Haka ta naji tana gani ta ƙusa hannunta wajan wutan tare da rage gas ɗin. Da mamakin ta kuwa ta ga samm wutan bai yi mata komai ba. Basar wa ta yi kana ta cigaba da yin hayyukan. Ta fara shirye-shiryen kunun aya da coslow saidai duk ba ta iya ba. Gashi kitchen ɗin duk ya yi kaca-kaca ruwan da ta ɗora ya tafasa har ya fara zuba a ƙasa.

Zama ta yi cikin gajiya ta ce. "Gaskiya ba zan iya ba, ina ga guduwa kawai zan yi, shi ne zai fi min sauƙi. Haka kurum za'a bunne ni da raina, chabb ina naga ta zama".

Ta faɗa tana mai waige-waige. Leƙo da kanta ta yi wajen kitchen ɗin ganin ƴan aiki da su Samrah basua nan ya sa ta sakin ajiyan zuciya sannan ta cire takalman ƙafarta ta riƙe su a hannu kana ta fara tafiya cikin sanɗa tare da saurin bin hanyar backyard.

Saida ta tabbatar da ta fita daga ciki sannan hankalinta ya kwanta. Nan ta fara nufar wajan garden domin kada wani ya ganta.

Haka ta cigaba da tafiya da tafiya ba tare da kowa ya lura da ita ba.

Ganin babu kowa a wajan ya sa ta fara gudu saida ta je daff da za ta fita daga garden É—in taci karo da Sooraj tare da Junaid.

Nan take ta yi saurin jan burki. Ba ta yi aune ba ta ji zufa ya fara ƙeto mata ta kowane sashe na jikinta.

"Ina kuma za ki je?, ko dai ba za ki iya ba ne shi ne ki ka yi tunanin guduwa?". Cewar Sooraj.

Nuna kanta Zahra ta yi ta ce. "Ni!, nayi maka kala da wacce za ta gudu?, ka san kuwa wace ce Zahra?, zahra ba ta taɓa guduwa sai dai a gudan mata, ba guduwa zan yi ba naga baku da albasa ne a kitchen shi ne na fito tsinka". Ta faɗa tare da kawar da kanta gefe sannan zuciyarta ya shiga dukan uku-uku!.

"Junaid dama muna da shukar albasa a masarautar nan?". Cewar Sooraj.

Dariya Junaid ya yo ya ce. "A'a yaya, ina ga ita ce ta shuka shi ne ta zo tsinka. Don mu dai bamu da wani shukan albasa a nan wajan".

Maida kallonsa Sooraj ya yi kanta sannan ya ce. "Kinji dai ko, babu albasa nan gwara ki lallaɓa ki koma ki cigaba da abin da ki ke yi".

Sunkuyar da kai Zahra ta yi sannan ta girgiza kai ta ce. "Shi ke nen".

Ta faÉ—a tana mai koma wa ciki.

_______________________
"Safira yanzu kin ji dai-dai?". Cewar Mom.

Girgiza kai ta yi ta ce. "Eh Mom naji dai-dai, Mom dan Allah ku barni na koma America, mun kusan fara exam É—in mu na Law, kuma shi ne exam na tantance wa, ya kamata ku barni na tafi".

Murmushi Mom ta yi sannan ta ce. "Amma na tambaye ki wani abu?".

Girgiza kai Safira ta yi alamun eh.

Kallonta Mom ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke son zama lawyer bayan akwai wasu courses É—in da yawa bayan shi?, sannan so ki ke kiyi ne don kuÉ—i ko don kare al'ummar da aka zalunta?".

Murmushi Safira ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da juya wa mahaifiyartata baya ta ce. "Ina son na zama lawyer ne domin kare haƙƙin al'umma sannan duk wanda aka zalunta nayi ƙoƙarin tsaya masa har saina ga an ƙwatar masa haƙƙin sa, ina son nayi law ne domi bayar da adalci tare da gaskiya, ban taɓa jin ina son yin aikin Law saboda kuɗi ba, ina son ne nayi domin tsaya wa tsayin daka domin kare haƙƙin ɗan adam. Idan tsanani ya kai maƙurar tsananta to adalci ne kaɗai yake iya maganinta. Sannan ina ji a jiki na kamar an taɓa zalunta ta a baya, shi ya sa nake son nayi wannan aikin. Dan Allah Mom karki ce A'a".

Ɗan jimm Mom ta yi sannan ta ce. "yanzu misali na tambaye ki, idan wani talaka ya zo domin ki tsaya masa a shari'a saboda na cuce shi, sai wanda ya cuce shi ɗin ya kawo miki maƙudan kuɗaɗe da kiyi shari'ar ƙarya kan wanda ya nemi taimakon ki idan ba haka ba zai kashe ki. To a wannan lokacin mene ne za ki yi?".

Murmushi Safira ta yi sannan ta ce. "Farko zan amince masa sannan na karɓi kuɗin, a yayin da muka je kotu zan tsaya wa wanda aka cuta naga an ba shi gaskiya sannan kuma shi wancan a yanke masa hukuncin kuma baya sannan a gaban idanuwan shi zan ɗauki ƙuɗaɗen da ya bani sannan na bawa wannan talakan, yayin da shi kuma kotu ta yanke masa hukunci".

Girgiza kai Mom ta yi sannan ta ce. "Kinga kenan maganganun da aka faÉ—a kan lauyoyi na cewa suna da baki biyu gaskiya ce. Farko kin gaya wa mugun cewa kin amince sannan bayan kinje kotu kuma ki ka faÉ—i wani abun da ban ba wanda ku ka shirya da shi ba, kinga hakan yana nufin kinci amanarsa kenen. Ke za ki iya gani cewa ta hanya mara kyau hakan iya samar da gaskiya da adalci. Amma asalin hanya ita ce ka bi ta hanya madaidaiciya domin samar da adalci wannan shi ne. Kinga kenen ba za ki iya aikin Law ba".

Saukar da ajiyan zuciya Safira ta yi sannan ta ce. "No Mom, I can do it. Ina da tabbacin cewa zan iya wannan aikin kuma ki zuba ido ki gani. Nan gaba za ki yi alfahari da ni".

________________________
"Wannan wane irin shashanci ne?, ta ya ya za ku ce Amrah ta gagare ku kun kasa kamata?, yanzu kenen duk plans ɗina za su tafi a banza?. To wallahi na baku 24hours ku sace ta, idan kuma ba haka ba zan sa a gama mun da ku". Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki sannan ya kashe wayar.

Wurgar da wayar ya yi sannan ya ce. "I have to make another plan, in ba haka ba, duk wahala na za su tafi a banza".

********
Zama Nurse Nadiya ta yi kan gadon kwanciyar ta sannan ta ce. "Na kasa gane me yake faruwa, me ya sa waÉ—an can mutane suka sace ni?, me ya sa suke tambaya ta mrs Laila, ko dai Mrs Laila har yanzu tana raye ne?, ya kamata na fara bincike kan wannan lamarin, idan ina son sanin gaskiya dole naje prison É—in da take domin sanin asalin labari".

*********
"Hajiya Binta ki daina kuka, Zahra fa ba yarinya bace, ba za ta ɓata ba, ita ɗin ma ƴar iskar kanta ce, kin ga za ta iya kare kanta ba tare da taimakon kowa ba".
Chapter 43 · 0% Book details