Sashe 55
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamaki ne ya kama Umar ganin nurse ɗin kwanaki da ya taɓa kai Amrah wajanta lokacin da ta suma.
"Kamar ke ce wannan Nurse É—in ko wanda na baki amanar Amrah a asibiti lokacin muna Jigawa?". Umar ya tambaya.
Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske ni ce nan ba wata ba, Mahaifin ka ya yi sanadiyar tarwatsa rayukan mutane babu adadi, shi ya yi sanadiyar rabuwar uwa da yaranta duk dan saboda abin duniya. Mahaifin ka ya kasance ya na aikata laifuka ne tun kafin ya zama Govnor, shi ɗin babban mara imani ne, ya ƙala wa baiwar Allah sharri wacce bata ji ba bata gani ba, ya sa kuma iyayen ta sun tsane ta dangint mijinta duk sun ƙi ta, sannan kuma duk da hakan bai rabu da ita ba, yana neman dukiyarta wanda ke a ɓoyayyen, wanda babu mai zuwa sai ita ko yaranta, gashi ya kashe ta, yaran ma bamu san inda suke ba. Shin mahaifinka baya tunanin shima wata rana zai koma ga ubangijin sa?, baya tunanin ta yadda zai fara sauke nauyin haƙƙin mutane da ya ci bayan ya mutu?".
Shiru Umar ya yi yayin da ya rasa ta cewa. Ji yake dama ba ta hanyar mahaifin shi ya zo duniya ba, nan take ya ji tsanar mahaifin na shi ya cikashe zuciyarsa baki É—aya.
*********
"Safira ya ishe ki aka, kina ta tsawatar min ina yin shiru, na riga na gaya miki cewa zan faɗa miki komai daga baya amma kin ƙi saurare na, me ki ke so nayi miki. Kin san dai ina sonki kuma ina ƙaunar ki, ta ya ya zan iya cutar da wanda nake so har cikin raina?, ya kamata ki fahimce ni, duk abinda ki ka ga ina yi, to ina yi ne ba dan komai ba sai dan saboda ke, ina san na bayyana miki wata gaskiya, kuma bana don na bayyana miki wannan gaskiyar ta baki na fison na bayyana miki ki gani da kanki".
Tashi tsaye Safira ta yi ta ce. "Bana da buƙata, ni kawai ka mayar da ni gida. Kai ɗin macuci ne, da a ganka a ga maciji, gwanda a fara kashe ka kafin a kashe wannan macijin, domin kai kafi maciji cutarwa".
Jin takum takalman mutane ya sanya Aliyu saurin riƙe hannun Safira sannan ya fara gudu da ita. Ƙoƙarin wafce hannunta take amma hakan ya cutura.
Kuka Safira ta fara yi ganin yadda Aliyu ya matse mata hannu yana gudu da ita.
Aliyu bai tsaya ba saida ya isa bayan kangon babban gidan da su Umar suke sannan ya dakata yayin da ya ja hannunta tare da shigar da su domin su ɓuya.
****
Mutanen Gov. Musa kuwa suna zuwa wajan, suka tarar ba kowa, hakan ya sanya su koma wa inda suke.
Ajiyan zuciya Safira ta shiga jera wa tana mai kallon hannunta da Aliyu ya riƙe. Gani ta yi guri ya kaɗa ya yi jajir. Nan da nan hawaye suka fara bin ƙuncinta.
"Yi haƙuri Safira duk abinda ki ka ga ina yi duk saboda ke ne". Aliyu ya faɗa murya a ƙasa.
*************
Ɗaki mai num105 na hango hajiya Binta ta yi tagumi idanuwanta a kan littafin da mrs Lailah ta bata, yayin da take tunano maganar da Mrs Lailah ta faɗa mata kafin su rabu. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ya ke".
Share hawayen da ke shirin zubo mata Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Yanzu Zahra ta kai minzalin sanin wace ce ita tare da sanin inda mahaifinta yake, na san dai ba iya ita É—aya Lailah ta haifa ba. Ina son na bawa Zahra wannan littafin amma ban san ta ya ya zan bata ba".
Daga nesa ta hango wata warder. Nan ta miƙe tsaye kana ta fara takawa izuwa inda wannan warder ɗin take.
Kallonta warder É—in ta yi ta ce. "Ya aka yi?, me ya sa baki ke kinyi cutting grass É—in da aka sanya ki ba".
Shiru Hajiya Binta ta yi ta ce. "Taimako nake so kiyi min, maganar cutting grass, zanyi shi, dan Allah wannan littafin nake son ki bawa DPO, kice idan ya ga MK ya ba shi wannan littafin, na san Mk zai iya sanin inda Zahra take. Ya bata littafin, gaba É—aya tarihin mahaifiyar su yana ciki".
Turnuƙe fuska warder ɗin ta yi ta ce. "Ba zan kaiba maxa kije kiyi aikin ki".
"Dan Allah kiyi haƙuri ki karɓa, dan Allah". Ta faɗa hawaye kan fuskarta.
Ganin hakan ya sa warder ɗin karɓar littafin sannan ta jaddada mata cewa zata bawa DPO. Jin hakan ya sanya Hajiya Binta yin farin ciki sannan ta koma inda take.
***********************
Bayan fitar Zahra ne ta saki murmushi yayin da ta fara jin son Sooraj ya fara shiga zuciyarta.
Chan ta hango Mami zaune tana shan lemo a parlour.
Da sauri Zahra ta yi fuska tare da ƙoƙarin wuce wa dan kada Mami ta ganta.
Cikin rashin sa'a ta ji Mami ta ce. "Zahra zo nan".
A kunya ce Zahra ta ƙarasa inda take tare da gaishe ta.
Amsa wa Mami ta yi murmushi kan fuskarta ta ce. "Zahra kenen, da fuska za ki yi ki wuce ko?".
Sosa kai Zahra ta yi ta ce. "A'a Mami, ai ban isa ba".
Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Wai me ke tsakanin ki keda Sooraj, naga yanzu kuna shiri ba kamar da ba, sannan naga har fita kunyi tare, yanzu ma naga kin fito daga ɗakin sa, faɗa min meke faruwa, kodai akwai wata a ƙasa" .
A kunya ce Zahra ta sa hijabin ta tana mai rufe fuska sannan ta girgiza.
Murmushi Mami ta yi ta ce. "Mene kuma na jin kunya, ki faÉ—a min gaskiya, nimai sa sarki ne ya je a neman miki auren ki wajan iyayen ki".
ÆŠago kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni bani uwa ko uba, amma ina da Hajiya Binta wacce ta maye min gurbin uwa".
"Ohh Allah sarki, ban san baki da iyaye ba, Allah y a jiƙan su ya yi musu rahama".
Amsa wa Zahra ta yi da "Ameen". Sannan ta ƙara da cewa. "Ni bani nake nani ƙewa yahya Sooraj ba, shi yake naniƙe min kinga kuwa shine yake sona, kuma nima na san yana sona kawai ɓoye min yake, bai san na sani ba". Ta faɗa tana mai yin dariya.
Girgiza kai Mami ta yi tare da miƙe wa sannan ta ce. "Na manta ban baki kyautar da na siyo miki ba, bara naje na dauko min, ki jire min lemo na".
GyaÉ—a kai Zahra ta yi ta ce. "Tom zan jire miki".
Jin hakan ya sa Mami barin parlourn tare da shiga part É—in ta.
Duk abinda suke yi a gaban idanuwansu Gimbiya saratu da yaransu.
Tashi Zahra ta yi jin wani ƙishin ruwa ya dame ta ya sata nufar hanyar kitchen domin samo ruwa.
Miƙa wa Samira ƙullin magani Gimbiya saratu ta yi ta ce. "Kije ki zuba wannan garin maganin a cikin lemon nan kafin wan can sheɗaniyar yarinyar ta dawo daga kitchen, maza-maza, ina son A'isha ta mutu idan ta sha maganin nan.
Da sauri Samira ta karɓa tare da zuwa inda lemon Mami yake sannan ta fara zazzaga maganin a ciki.
Dai-dai lokacin Junaid ya shigo da sauri ya ɓuya sakamakon harba da ya yi da Samira. Bai yi dogon tunani ba, ya fara yin video sannan ya yi saurin juyawa.
Dai-dai lokacin Zahra ta shigo cikin parlourn yayin da idanuwanta ya sauka kan abinda Samira ke aikata wa.
"Kuttmelesi!, me nake gani haka, guba za ki saka wa Mami a lemo".
A razane Samira ta dube ta kana ta karkaÉ—e hannunta ta ce. "Toh ina ruwan ki?, waya gaya miki guba nake saka mata, na É—anÉ—ana lemon ne naji ba zagi shi ne na saka mata siga saboda ya yi daÉ—i".
"Ƙarya ki ke munafuka". Cewar Zahra sannan ta ƙara da cewa. "Lemon haɗi ne da zai buqaci siga?, wannan lemon roba ne, ki faɗa min gaskiya me ki ka saka a ciki, ko na danne ki a nan wajan nayi miki duka".
Dai-dai lokacin Mami ta shigo parlourn. Ganin Mami na zuwa ya sa Samira ta yi saurin wurga wa Zahra ƙullin maganin tare da fasa ihuu.
Nan da nan mutane suka cika cikin parlourn. Kallonta Mami ta yi ta ce. "Samira me ya sa za ki kurma ihu aka?".
Amsa Samira ta bata da cewa. "Zahra na gani tana saka miki guba a cikin lemo".
Take gaban Zahra ya faÉ—i. "Ni kuma?, hakan me ya sa za ki yi min sharri?, ba ke na kama ba kina saka mata guba".
Dai-dai lokacin Sooraj ke fitowa daga part É—in shi.
Nan ya yi kicubus da su Mami tare da su Gimbiya saratu a tsatsaye. Mamaki ne ya kama shi.
Ƙarasa wa inda suke ya yi ya ce. "Me yake faruwa?".
Amsa Samira ta bashi da cewa. "Zahra muka gani tana zuba wa Mami guba a cikin lemo".
"What!, no wannan ƙarya ne, saboda me za ta aikata hakan".
Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra da gaske ne abinda Samira ta faÉ—a?".
Girgiza kai Zahra ta yi ƙwallah fal idanuwanta ta ce. "Wallahi bani bace ba, ita na gani tana saka wa Mami guba shi ne ita kuma ta ƙala min sharri".
"Ƙarya kike muma mun ganki lokacin da ki ke saka wa". Cewar Gimbiya Talatu.
Zuciya a rauna ce Mami ta ce. "Zahra ki rasa da me za ki saka min da shi sai sanya min guba cikin abin sha na?, Why Zahra why?, ga kyautar sarƙar da na siya miki nake shirin baki amma ki ka ɓata wayon ki ta hanyar wannan hanyar da ki ka biyo".
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami bani bace. Yahya Sooraj tunda Mami bata yarda da ni ba kai ka yarda da ni, samm ba zan iya aikata hakan ba".