← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 59

Sashe 28

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "To kuyi mata mana a hankali bawai sai kun dinga janta ba, yanzu da wannan mahaifiyar wani a cikin ku ne za ku ji dad'i ku ga wani yana janta a ƙasa kamar kayan wanki?. Maza ku cika ta kafin na ɓata muku rai". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.

💃💃💃💃💃💃💃💃

COMMENTS, LIKE, AND SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)

https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣9️⃣▶️3️⃣0️⃣
*_________________________________________________*
"Kinga malama muna kan aikin mu ne, ita ɗin mara lafiya ce kuma nauyin kula da lafiyarta yana rataye a wayar mu ne , don aka Please ki bar mu muyi aikin mu. Ke mene ne ma naki a cikin tun da ita ɗin ba ɗaya daga cikin dangin ki ba ce ko ko kuma ince ita ɗin ba mahaifiyar ki bace don aka ki ƙyale mu". Ɗaya daga cikin su ya faɗa yayin da suka fitar da ita daga ɗakin.

Ajiyan zuciya Zahra ta sauke!, sannan ta ce. "Kuma fa maganar sa aka ne, me ya sa nake nuna damuwa ta sosai a kan matar?, sa'anan kuma me ya sa naji ta shiga raina sosai?". Basar wa ta yi sannan ta ce. "Ki basar kawai, naji ta shiga raina ne kawai". Aka ta cigaba da magana ita É—aya.

Miƙe wa tsaye ta yi tare da fizge drip ɗin da aka saka mata. Ya mutse fuska ta yi ganin yadda jini ke fita a saitin in da ta fizge drip ɗin. Sannan ta ɗauki cotton wool da ke ajiye kan table ta saka a wajan. Kallon taga ta yi ta waje ta ga mutane na fice da shige.

"Ya kamata na tafi daga nan". Ta faÉ—a tana mai dafa cikin ta da sauri jin yadda yake murÉ—a mata.

"Wayyo ni Fatima Zahra, yanzu me zan ci?, gashi ko biyar bana magani, ya kamata na tafi daga nan wajan". Ta faÉ—a tana mai fice wa daga cikin É—akin.

***************
Cikin masarauta kuwa, ko ina ka kalla tarin jama'a ne, tare da fadawa a tsatsaye. Yayin da kowa ke riƙe da kwanon abincin. Junaid ne zaune gefe ɗaya yayin da gefensa kuwa tarin buhun shinkafa. Babu abin da yake sai faman miƙa wa jama'a kayan abinci. Al'adar masarautar kenen a duk wata ana sadakar avinci tare da kuɗaɗe ga talakawa marasa ƙarfi.

Fitowa mai martaba ya yi. Nan take mutane suka fara kwasar gaisuwa tare da yi masa kirari. Zama ya yi kan kujera kusa da Junaid yayin da ya cigaba da zuba ido ga abin da Junaid yake yi don ya sanshi da albazaranci.

***********
Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Au aba da gaske?, sune za su kawo ƙarshen nawa?, gaskiya kina da abin dariya. To ki sani kafin ma su san cewa ni ne na wargaza su nayi sanadin rabuwarsu izuwa gurare daban-daban zan gama da su. Don aka ba zan kashe ku ba yanzu, domin idanuwan ku ya gane muku abin da zan aikata, zan sa ne a fitar min da ku daga wannan ƙasar gaba ɗaya". Ya ƙarashe maganar yana mai kallon ɗaya daga cikin yaran nasa sannan ya ce. "Maza ku saka su a mota ku tafi da su, ni yanzu zan wuce gida".

"Done". Suka furta gaba É—aya.

Shiga cikin motarsa Gov. Musa Muhammad ya yi yayin da jami'an sa suka ja mota tare da barin cikin dajin baki É—aya.

********
"Habib wai me yake damun yarinyar ka Safeera ne?". Cewar Grandpa.

Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Wallahi Abba nima ban sani ba, na rasa me yake damunta, aka ma lokacin da muke a America ta faÉ—i kasa saida muka zo nan Nigeria sannan ta buÉ—e idanuwanta. Aliyu ya ce min ko Aljanu ne da ita, amma ni samm ban yarda Æ´ata tana da aljanu ba, ban san mene ne abin yi ba".

Sauke ajiyan zuciya gaba ki ɗaya suka yi sannan suka ce. "Dole dai akwai wani abu a ƙasa, babu ta yadda za ta dinga faɗuwa aka kurun ba tare da wani ya yi mata abu ba". Cewar Grandma.

Gyara zamansa Grandpa ya yi kan wheel chair sannan ya ce. "Maza ku zo muje wajan wani tsohon aboki na a chan wani ƙauye, shi ɗin babban malamin ruƙiya ne, aljanu, mayu da sheɗanu tsoronsa suke dole muje mu kawo sa da kannu domin ya duba ta. na san shi zai san koma mene ne yake damunta". Grandpa ya faɗa tare da ƙwalla wa Aliyu kira. Nan Aliyu ya fito daga ɗakin.

Kallon Aliyu Grandpa ya yi sannan ya ce. "Aliyu zamu fita yanzu, zamu je mu ɗauko maganin ruƙiya mu kawo domin sanin meke damun Safeera. Don aka ka zauna ka kula da Safeera mu zamu je mu dawo, su Zuwaira basua nan sun tafi makaranta don aka na baka amanar Safeera idan ka ɓata mata rai sai nayi maganinka".

Girgiza kai Aliyu kawai ya yi sannan ya ce. "Tom shi ke nen Kaka sai kun dawo". Ya faÉ—a yana mai koma wa É—aki da Safeera take.

Fita su grandma suka yi tare da shirya wa suka shiga cikin motocin gidan sannan suka fice daga gidan. Kai tsaye suka nufi hanyar Gujingu.

********
Koma wa Aliyu ya yi kan kujerar da ke fuskantar Safeera sannan ya cigaba da zuba mata idanuwansa.

A hankali Safeera ta fara buɗe idanuwanta a yayin da a ƙarshe ta yi nasarar buɗe su bako ɗaya tare da sauke su kan Aliyu wanda ya zuba mata idanuwa sai kallonta yake kamar wani maye.

Zumbur ta miƙe zaune sannan ta ce. "Ya dai mene ne ka ke yi tare da ni?, where is my Mom?".

Furzar da iska Aliyu ya yi ya ce. "Sun tafi wajan malamin ruƙiya domin a kawo shi ya yi miki ruƙiya aljanun da ke jikin ki su fita".

Nan take ran Safeera ya ɓaci ta ce. "Kamar ya Aljanu?, ni ce mai aljanu?, koda yake ba laifin ku ba ne ba".

Taɓe baki Aliyu ya yi ya ce. "Ke Safra ki ke da suna ko me, ki dinga sarrafa harshen ki domin ni hannu na rawa yake zan iya bugar bakin ki da shi".

Cikin jin haushi Safeera ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Ka ga malam sunana Safeera ne ba Safra ba idan ba za ka iya cewa Safeera ba ka kira ni da nickname ɗina wato Diana. Sannan kuma da ka ke cewa za ka buge baki na kai a waye za ka ce za ka buge baki na?, wallahi ka fita daga cikin harka ta na gaya maka. Kuma wallahi su Mom na dawo wa zamu tattara komai namu mu bar gidan nan, dan ni gaskiya ba zan iya rayuwar wannan ƙasar ba".

Ta faɗa tana mai ƙoƙarin fita daga cikin. Da sauri Aliyu ya fizgo ta jikinsa tare da matse ta ya ce. "Kada ki manta ni da ke ne kaɗai a gidan nan, idan ki ka yi min rashin kunya zan zane ki kuma na zane banzam sannan shi wannan ƙasar da ki ka ce bakya so na ga dai iyayen ki ƴan nan ne ba'a ƴan chan ƙasar ba, don aka makntain your word's okay".

Cire jikinta ta yi daga na shi sannan ta ce. "Kada ka sake É—ora hannun ka a jiki na, domin kai É—in ba miji na ba ne okay, you don't have the right to touch a responsible lady like me okay, please don't add to my anger this afternoon".

Murmushi Aliyu ya yi tare da janyo ta sannan ya samu bakinta tare da kama wa ya fara murɗawa. Nan take ta saki ɗan ƙaramin ƙara na raɗaɗi!.

"Leave me alone". Ta faɗa hawaye na bin ƙuncinta.

Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "In fa ki ka ce za ki yi jayayya da ni sai dai kici wuya, kuma da ki ke wani ikirarin cewa ni ba mijin ki ba ne, na san da hakan ai amma kuma an your future husband so ya kamata tun yanzu na fara saita ki kafin ki shiga gida na". Ya faɗa tare da sakin leɓenta wanda suka ƙara rinewa suka yi jajir saboda jan da Aliyu ya yi musu.

Riƙe leɓenta Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi Allah ya kiyaye na zamo matar ka, kuma in dai suka dawo saina faɗa wa Grandma abin da kayo min kuma wallahi bashi ka ɗauka domi saina rama". Ta faɗa tare da fice wa daga ciki ɗakin.

Chan ta samu guri a parlour ta zauna tare da kunna tashar Bollywood ta fara kallo. Saida ta É—au lokaci sosai tana kallonta cikin nishaÉ—i hankalinta kwance take kallon abinta.
Fitowa Aliyu ya yi tare da samun guri ya zauna a parlourn sannan ya É—auki remote tare da chanza tashar izuwa tashar Ball.

Nan take ran Safeera ya ɓaci dubansa ta yi ta ce. "A kan mene ne za ka zo ka wani chanza min channel ɗin da nake kallo?, maza ka maida min abuna. Kai na fahimci cewa baka son zaman lafiya kuma ni ma zan nuna maka cewa nafi ka rashin son zaman lafiya, maza ka mayar min".

Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "To Mama É—anki zai yi kamar yadda ki ka ce". Ya faÉ—a tare da sakin wani killer smile sannan ya ce. "Nan É—in ba gidan ku ba ne balle ki saka wani doka ko order okay, nan É—in gidan mu ne, don aka be careful".

**************
Jan kumatun Amrah Khairiya ta yi sannan ta ja hannunta suka shigar da su part ɗin su. Nan suka cire mata grasses ɗin jikin ta tare da ɗaura mata towel sannan suka nufi toilet da ita. Nan suka shiga wanke mata gashin kanta wanda suka kwanta har gadon bayanta. da hair oils masu ƙamshi.
Chapter 28 · 0% Book details