← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 59

Sashe 39

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tashi muje zamu kaiki in da ƴan uwanki suke". Jin abin da Umar ya faɗa, hakan ya sa Amrah saurin miƙe wa tare da sakin murmushi. Juyawa suka yi gaba ɗaya suka nufi wajan parking space, ganin hakan ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansu. Shiga cikin motan ɗaya Usman da su Khairiya yayin da Usman ya tada mota, tare da fice wa daga gidan. Buɗe wa Amrah ƙofa Umar ya yi ta shiga sannan ya sauke mata glass ɗin motan ƙasa. Sannan ya tada motan tare da barin harabar gidan.

Daga bisani suka nufi hanyar garin Kano.

*To kafin mu cigaba dai muna son sani wane ne asalin Umar? sanann wane ne asalin gov. Musa Muhammad*.

Alhaji Muhammad shi ne asalin mahaifin Musa Muhammad. Alhaji Muhammad ya kasance mutum tawakali da kuma sanin ya kamata, ya kasance mutum bai bin ƙa'ida. Matar sa Halima ta rasu ne a lokacin da take naƙudan ƴar su ta biyu wacce ta ci suna A'isha. Musa ya kasance ɗa na fari a wajan mahaifin sa sai kuma A'isha. Musa ya taso tun yana ƙarami da burin zama ɗan siyasa domin shi gaba ɗaya a tunanin shi babu komai a cikin yin harkar siyasa sai kuɗi. Hakan ya sa ya ƙudiri niyar zama ɗan siyasa. Alhaji Muhammad ya tura musa karatu domin ya yi karatun Engineering, sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne Musa ya chanza course ɗin da mahaifin nasa ya zaɓa masa izuwa Political science. Musa ya gama diploma sa ne yana da shekaru talatin shif. A wannan lokacin A'isha ta kammala HND ɗin ta. yayin da ta fito da wanda take so wato ɗan sarkin garin Kano. Bayan an ɗaura musu aure shima Musa ya auri matarsa Khadija wanda suka haɗu da ita a University ɗin da ya yi.

Haka ya cigaba da sha'awar zama É—an siyasa ba tare da mahaifin ko matar sa ta sani ba.

Khadija ta kasance mace mai riƙo da addini, tana ƙoƙarin gujewa duk abin da zai ɓata wa mijin ta rai. Bayan shekara ɗaya ta haifo santalelen ɗanta wanda ya ci suna Umar.

Farin ciki wajan waÉ—an nan ma'auratan ba zai misaltu ba.

Ana tsaka da aka, Musa ya je ya bayyana wa mahaifin sa abin da ya karanta a jami'a. Hakan ya sa ran mahaifin sa ya yi matuƙar ɓaci. Yayin da mahaifin sa ya ƙudiri niyar cewa muddin yana da rai ba zai bari ya zama ɗan siyasa ba. Jin furucin da ya fito daga bakin mahaifin nasa ya sa Musa ya tunzura sannan ya yi tafiyarsa sai bayan wasu lokaci ya dawo wajan mahaifin sa, sai dai a wannan karan bai dawo domin neman yafiyar mahaifin sa ba, ya dawi ne domin ya ɗauki ran mahaifin sa.

Bayan isarsa chan ne ya tara Æ´an daba suka zagaye gidan a yayin da ya sa a É—aukar masa video ta yadda zai kashe mahaifin na shi. Alhaji Muhammad na kwance cikin jinya da tsananin ciwo Musa ya shiga É—akin nasa. Ganin yana kwance ya sa shi sakin murmushi ba tare da imani ko tausayawa ba ya samu pillow ya danne fuskar mahaifin nasa da shi. Haka Alhaji Muhammad ya dinga kuruwa har rai ya fita daga jikin shi. Musa bai sake shi ba saida ya tabbatar da baya da sauran numfashi. Hakan ya sa shi farin ciki a sa'inda ya dinga ganin kansa matsayin govnor domin kuwa tunda mahaifin nasa ya mutu babu wanda zai ana shi zama govnor.

Jama'a sun yi kuka na rashin Alhaji Muhammad da suka yi, yayin da ita ma Khadija ta ci kukan ta har ta gode wa Allah.

Musa ya fara neman takara shida babban Abokin sa wato Abdullahi wanda suka taso tun suna ƙanana har izuwa girmansu tare suke. Hakan ya sa kowanensu yake da burin zama ɗan siyasa. amma sai dai shi musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karɓe sa hannu biyu. A yayin da Abdullahi ya zama babban ɗan siyasa ya yi alƙawarin gyara ƙasar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya ɗora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta.

Umar yana da shekaru biyar a duniya Khadija ta kuma haifo santalelen ɗanta saidai yaron bai zo da rai ba. Bayan wasu shekaru Khadija ta sake haifo namiji wanda ya ci suna Usman, Sannan Ramlat sai kuma ta ƙarshe Khairiya wanda su ukun gaba ɗaya shekara ɗaɗɗaya ne a tsakani.

Haka rayuwa ta cigaba wataran da dad'i wataran kuma godiyar Allah. Ana tsaka da haka wata rana Khadija na gyara ɗakin Mijin ta, nan ta tarar da wani caset. Ɗaukar caset ɗin ta yi sannan zuciyar ta tace da ita ta saka caset ɗin a tv ta ga ko film ne. Bayan ta saka caset ɗin ne a tv ta ga abin da ya yi matuƙar firgita tunaninta. Mijinta ta gani ya kashe mahaifin sa da hannunsa . Hakan ya sa ta ji dana sanin auran sa. A dai-dai wannan lokacin kuma Musa ya shigo ya tarar da ita a ɗakin tana kuka. Nan dai ya gano cewa ta gano shi ne wanda ya kashe mahaifin sa. Ganin hakan ya sa Musa ya fara roƙon matar sa da ta rufa masa asiri. Amma ita kuma Khadija taƙi amincewa sannan ta ce dole ta sanar da ƴan sanda ko wane ne mijinta domin ba za ta iya take gaskiya ba. Ganin dai taƙi bashi haɗin kai ne ya sa ya ɗauki glass cup sannan ya rotsa wa kanta. Nan take kanta ya fara fidda jini yayin da ta faɗi ƙasa mutacciya. A dai-dai wannan lokacin Umar ya dawo daga makaranta sannan ya shiga cikin ɗakin nan ya tarar da gawar mahaifiyarsa a kwance. Hakan ya sashi sakin ƙara yayin da ya faɗi ƙasa sumamme.

Ganin hakan ya sa Musa ya goge kowane sheda da Æ´an sanda za su bi domin gano makashin.

Bayan nan ne ƴan sanda suka zo suka yi ƙaraci binciken su basu samu komai ba. Hakan ya sa haka rufe case ɗin.

Bayan wasu kwanaki ne Umar ya dawo cikin hayyacinsa a yayin da yake mafarkin mahaifiyar sa sannan ya ƙudiri niyar dole ya zamo jami'i, domin ya san wanda ya kashe mahaifiyar sa sannan kuma ya kare ƙasar sa daga sheɗanun mutane irin mahaifinsa. Umar ya fara jin tsanar mahaifinsa ne tun lokacin ya ga mahaifin sa da wasu karuwai a gidan su. Daga wannan rana Umar ya tsani mahaifin sa.

Bayan Umar ya yi karatun sa na boko da na addini ne ya shiga training school na jami'ai. Hakan ya sa ya fara gudanar da al'amuran sa shi ɗaya. A sa'inda duk abin da ƙanensa suke da buƙata shi yake musu. Kan kace me Umar ya zama babban jami'i wanda gaba ɗaya ƙasa ke magana kan ƙwarewarsa domin kuwa duk wani mai laifi idan ya yi musu wahalan kama wa Umar shi ne wanda ake bawa wannan aikin kuma duk in da wannan mai laifi yake zai nemo shi sannan ya tabbatar da an hukunta shi. Aka ya cigaba da bincike domin gano makashin mahaifiyar sa, sai dai har izuwa wannan lokacin bai gano ko wane ne ba kuma bai san irin aikin mahaifin sa ba.

A ɓangare guda kuma shima Musa ya zama ɗan siyasa ba tare da an san ta wace hanya ya bi ya samu wannan takara ba.

*Amma idan ta yi tsami zamu ji ta yadda ya samu takara shiga siyasa*

Haka su Khairiya suma suka taso cike da ƙaunar juna. Yanzu dai Usman ya gama karatun sa yana aiki a office. Sai kuma Ramlat wacce ke University level 300 tana karatun Optometrist. Da kuma Khairiya wacce ke 100 level tana karatun biology.

*Wannan dai shi ne takamaiman tarihin Umar*

___________________
Shigowa da motoci masu tsaron govnor Musa suka yi. Fitowa Gov. Musa ya yi daga cikin mota ganin babu motoci guda biyu a gidan hakan ya nuna masa alamun cewa tabbas Umar ya fita.

Kallon masu tsaron gidan ya yi ya ce. "Where's Umar?".

Amsa É—aya daga cikin masu gadin ya bashi da cewa. "Yanzu suka fita".

Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Kun san in da suka je?".

Amsa suka ba shi da cewa. "A'a, amma mun ji kamar suna zancen za su je Kano".

"Kano!". Gov. Musa ya maimaita sunan. "Shi ke nen". Kawai ya ce sannan ya shiga part É—in shi. Yana shiga ya yi saurin É—aukar wayarsa sannan ya lalubo number Aliyu tare da danna mai kira.

______
Aliyu da ke zaune sai faman kallon Safira yake yana murmushi ne ya ji wayar sa na ruri. Maida kallonsa ya yi kan wayar. Ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin ne ya sa shi miƙe wa sannan ya bar cikin parlour ɗin daba bisani ya ɗaga kiran. Ya ce. "Salamu alaikum".

Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa ya amsa sallamar sannan ya ce. "Aliyu ina da buƙatar taimakon ka yanzu dan Allah, ɗa na da ƙannensa su tafi hanyar Kano, yanzu haka na san sun kusa isa chan, ina son ka bibiyar mun su bana son ya gano gaskiyar ko ni wane ne, sannan kuma bayan nan akwai yarinyar Mrs Laila a Kano ina son ka bincika min duk in da take ka sa a sace ta. Dan Allah ba dan ni ba Please, zan tura maka duk kuɗin da ka ke da buƙata".

ÆŠan jimm Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen naji, million goma shi ne kuÉ—in aiki na, kuma cash nake so ba transfer ba".

"Shi ke nen Aliyu, ni zan ma ƙara maka ya zama twenty ni dai kawai buri na shi ne ka dakatar da su sannan ka nemo in da yarinyar Lailah take".

"Kada ka samu damuwa wannan abu ne mai sauƙi, nan da sati ɗaya zan nemo duk in da take, kai dai kawai ka shirya min kuɗaɗe na". Cewar Aliyu.

"Angama". Gov. Musa ya faÉ—a tare da katse wayar yana mai maida numfashi.
Chapter 39 · 0% Book details