← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 59

Sashe 47

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙe wa zumbur Safira ta yi cike da farin ciki ta ce". Wow!, thank you so much, I can't even describe how happy I am. Very soon, I'll be heading to America." Ta faɗa tana mai katse wayar.

Da sauri ta fita parlour ciki sa'a ta tarar da su Mom a parlour, nan ta sanar musu abin da ya faru. Babu wanda bai yi farin ciki ba amma Mom samm ba ta so hakan ba domin ba ta som ta yi nisa da Æ´arta.

A gurguje Safira ta koma ɗaki kana ta shirya kanta da kayanta. Bayan ta gama shirya kayanta a travelling box. Ta saka kaya masu kyau riga da wando sannan ta saka ɗan ƙaramin veil sannan ta ɗora kimono a kan riga da wandon.

Fitowa ta yi da box É—in sannan ta nufi hanyar waje. Bakwana suka yi da kowa na gidan yayin da Daddy ya shiga saka mata albarka. Mom kuwa shiru ta yi domin gaba É—aya hankalinta ba'a kwance yake ba, ji take kamar wani abu na shirin faruwa da Æ´arta.

Kallon Safira ta yi ta ce. "Safira, ni da za ki ji ta baki na kiyi zamanki kawai, idan ya so idan za mu koma America sai kiyi komai, wallahi hankali na ya kasa kwanciya, tsoro na shi ne kada wani abu ya same ki".

Murmushi Safira ta yi ta ce. "Kada ki damu Mom babu abin da zai same ni da izinin Allah".

Daidai lokacin suka jiyo horn ɗin mota a waje. Bye-bye tayi musu kana daga bisani ta fice daga gidan. Fitowa driver ɗin motan ya yi sannan ya karɓi box ɗin kayanta tare da saka su a bayan mota. Shiga cikin motan ta yi kana daga bisani driver ya ja mota suka bar wajan.

Sosai Safira ke farin ciki yayin da take gani kamar cewa ta riga ta zama lawyer.

Kallon driver É—in ta yi ta ce. "Yanzu hanyar airport zamu wuce ko?".

Shiru driver É—in ya yi mata bai ko tanka mata ba.

Mamaki ne ya kamata ganin bai amsa ba, hakan ya sa ta yi tunanin ko bai ji ba ne.

Hankalinta bai tashi ba sai sanda ta ga anyi wani kwana da ita ana shiga cikin dajin.

Nan take gabanta ya tsananta faɗuwa. Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Kai driver ina ka ke ƙoƙarin kai ni?, ba airport ka ce zamu je ba, ni ka ga just take me back home please".

Ganin ko kulata bai yi ba ya sa hankalinta ya ƙara tashi.

Addu'a ta shiga yi tana mai neman kariyar Ubangiji. Yayin da hawaye ya fara sauka kan ƙuncinta tana mai nadama kan me ya sa ta biyo wanda ba ta sani ba, kuma saida Mom ta faɗa mata cewa kada taje ta bari idan za su koma America.

Saida suka je chan cikin tsakiyar daji. Sannan driver ɗin ya tsagaita da tafiya. Parking ya yi kusa da sauran kidnapper's ɗin sannan ya fito daga mota. Buɗe mata ƙofa ya yi kana ya dube ta ya ce. "Duk abinda haka faɗa miki a waya to ƙarya ne. A halin yanzu dai kina ƙarƙashin mu ne, kuma idan muka gadama za mu kashe ki har lahira, ina son ki bamu haɗin kai idan ba haka ba ki mutu".

FaÉ—uwa gaban Safira ta yi sannan ta ce. "Dan Allah ku faÉ—a min mene ne na aikata muku?, sannan wane ne ya turo ku sace ni?".

Murmushi mutumin ya saki sannan ya ce. "Kina son sanin wane ne?".

Girgiza kai Safira ta yi alamun eh.

Amsa mutumin ya bata da cewa. "To Aliyu ne".

Rass! gabanta ya buga da mugun ƙarfi. Kallon mutumin ta yi ta ce. Wane Aliyu?, Aliyu wanda zan aura?".

Amsa suka bata da cewa. "Ƙwarai kuwa da gaske".

Kallon su Safira ta yi cikin rashin yarda ta ce. "Ƙarya ku ke, samm Aliyu ba zai sa a sace ni ba, saboda me zai yi hakan?, ni ce fa wacce zai aura. Kunga ku faɗa min gaskiyar cewa ba Aliyu ba ne, domin na yarda da shi ba zai taɓa sace ni ba, kuma mene ne ribarsa ma idan ya sace ni?, me zai samu?".

Dariya gaba É—aya suka kwashe da shi sannan suka ce. "Kina son sanin me zai samu?. To ki baza kunnuwanki kiji, zai samu kuÉ—aÉ—e ne, dubbunan kuÉ—aÉ—e, Aliyu samm ba sanki yake ba illa dukiyar ki, kuma dai Aliyu shi ne ba wani ba. Idan baki yarda ba duba nan ki gani".

Mutumin ya faÉ—a yana mai nuna mata wayarsa. Nan ta ga Aliyu tare da mutanen wajan suna raba kuÉ—i a tsakanin su, yayin da suke maganar yadda suka sace Amrah, gashi za su sace Safira.

Jikin Safira ne ya mutu, yayin da takaici ya ana ta kasa cewa ƙala. Hawaye ne ya fara gangaro wa bisa ƙuncinta. Ta ce. "Ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba Aliyu, me ya sa zai aikata min haka?, da na yanke cewa zan amince na aure sa domin ya nuna min cewa yana so na sannan kuma yana da nutsuwa da sanin ya kamata, ashe duk ƙarya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai fashe wa da kuka.

**********
Zahra na zaune ta ga ƴar aiki ta shigo sallama riƙe a bakin ta. Amsa sallamar Zahra ta yi ta ce. "Mene ne ya faru?".

Amsa Æ´ar aiki ta bata da cewa. "Yarima Sooraj ne ya ce na kira wo masa ke, kuma ya ce ki zo cikin gaggawa".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Allah ko?". Sannan ya ƙara da cewa. "To ki koma ki gaya masa cewa ba zan zo ɗin ba, idan zai iya zuwa ya tafi da ni chan ya zo ya ɗauke ni, sannan kice mai tunda shi ne yake buƙata ya zo da ƙafarsa amma ba dai ni na je ba, ni Mami kawai nake yi wa aiki bawai shi ba, ita kaɗai ce za ta sani aiki nayi ki gaya masa hakan". Ta faɗa tana mai koma wa tare da kwanciya.

Fita ƴar aikin ta yi sannan ta nufi part ɗin Sooraj ta zayyane masa duk abin da Zahra ta faɗa. Nan take ran Sooraj ya ƙara ɓaci. "Ni ce zan kira ta tace wai ba zata zo ba sai dai ni da kaina naje?, za ta gane kuranta". Maida kallonsa ya yi kan ƴar aikin ya ce. "Jeki na san yadda zan yi da ita".

Jin hakan ya sa Æ´ar aikin ta bar masa part É—in sa.

******
Zahra na kwance taji an banƙo mata ƙofa. A matuƙar razane ta miƙe tsaye. Su Gimbiya Saratu ne tare da su Fasma.

Rufe ɗakin suka yi sannan suka saka maƙulli suka rufe.

Murɗa hannayensu suka yi a ƙirji sannan Gimbiya Talatu da su Samira suka fara karkaɗa ɗuwawu.

Kallonta Yusra ta yi ta ce. "Wati ke kin cika ƴar iska da har za ki iya sa mu ci wannan ƙazamin abincin naki".

Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Naji ƙazami ne, amma dai koba komai kunci abincin. Tukun na ma me ya kawo ku ɗaki na?".

Amsa Gimbiya Saratu ta bata da cewa. "Munzo mu nakaÉ—a miki na jaki ne, duka zamu yi miki".

Babu zato Zahra ta kwashe da dariya. Kallon juna su Gimbiya Saratu suka yi ganin tana dariya ya sa abin ya basu mamaki.

Saida Zahra ta yi mai isarta sannan ta ce. "Wai da gaske duka na ku ka zo yi?. To masha Allah maraba da zuwa, me ku ke so na kawo muku, tuwo ko shinkafa?, kun san ana son mutun kafin ya fara dambe ya fara cin abinci mai lafiya ta yadda zai samu ƙarfin yin duka sosai".

Kallon juna suka yi gaba É—aya suka yi ganin tana neman shashantar da su ya sasu cewa. "Da gaske fa muke ba wasa ba".

Jin hakan ya sa Zahra ta haɗe ranta sannan ta ce. "Zan baku shawara kyauta ba tare da ko sisin ku ba, kuyi wa kanku faɗa ku koma, domin idan na fara dukan ku karku zo kuna bani haƙuri naƙi hakura, ku yanke shawara a tsakanin ku tun kafin a fara".

Kallonta Samira ta yi ta ce. "Kin ɗauka za ki iya dukan mu ne?, ko kin manta cewa sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi?, to ba za mu fita ɗin ba kiyi abin da ki ke ganin za ki yi" .

Jin hakan ya sa Zahra miƙe wa sannan ta nufi hanyar waje ta ƙara rufe ƙofar sosai sannan ta cire ki ɗin tare da saka wa a ciki kayanta wanda yake doguwar riga atamfa mai aljihu.

Koma wa ta yi ta zauna kan gado ta ce. "Ta kan wa za'a fara?, ku gimbiyoyi ku koma ku zauna ku ga idan yaranku suna da ƙarfi ko basu da shi".

Kamar yadda ta faÉ—a aka gimbiya Saratu da Talatu suka koma suka zauna, yayin da suke jiran kawai suka yaran nasu sun fara jibgar Zahra.

Take Samira ta kaiwa Zahra naushi a fuska. Da sauri Zahra ta kawar da kai sannan ta kama kan Samira da Fasma ta gwara su guri É—aya.

Nan take suka saki wata iriyar azababbiyar ƙara!. Ƙaran da suka saki ya janyo hankulan su Junaid da na so Sooraj ɗakin. Da sauri suka nufi hanyar ɗakin Zahra tare da bubbuga ƙofan.

Ɓangare Zahra kuwa ɗaukar dorina ta yi ta fata shauɗa musu babu gaggauta wa. Ihuu suke suna neman a kawo musu agaji . Ganin ba za su iya cigaba da jure wa ganin Zahra na dukan musu yara ba ya sa su miƙe wa suka fara rirriƙe hannun Zahra.

Ɗaga hannu Zahra ta yi zata zuba wa wanda ya riƙe ta dorina. Chak da dakata ganin su Gimbiya Saratu ne. Wafce jikinta ta yi daga nasu ta ce. "Ba zan iya dukan ku ba, domin kuwa kuma a matsayin iyaye na ku ke, dan haka ba zan taɓa iya ɗora hannu na a kanku ba". Ta faɗa tare da koma wa ta zauna.

Miƙe wa su Samira suka yi suna hawaye, yayin da su Gimbiya Saratu suka shiga rarrashin su gani yadda jikinsu ya yi jajir yayin da satin bulalan Zahra duk ya fito jikinsu.

Kallon Zahra Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ki bamu maƙulli mu fita".
Chapter 47 · 0% Book details