← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 59

Sashe 33

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***********************
Cikin rashin fahimta Safeera ta dubi Umar ta ce. "I don't understand what you are talking about, wace ce kuma mai green eyes?, ni a ina na sanka ma da za ka ce wai ni mai green eyes?. Kodai kana imagination ne?, ya kamata ka je asibiti a duba ka".

Ta faÉ—a tare da juya wa ta yi tafiyar ta.

Baki sake Umar ya bita da kallo sannan ya ji zuciyar shi nayi masa zugi. Baiyi aune ba ya ga Safeera ta ɓa ce masa daga gani.

Ɓangaren Aliyu kuwa gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi yayin da ya rasa me zai yi domin tabbatar da cewa wannan Safeera ce ko ba ita ba ce. Yana tsaka da tunani ne kwatsam ya ji wayarsa ta fara ringing.

Nan hankalin sa ya É—auke daga kan Amrah izuwa wayarsa. ÆŠaukar wayar sa ya yi ganin sunan wanda ke bayyane kan screen É—in wayar ya sa shi saurin É—aga wayar.

Juya wa Amrah ta yi tare da barin wajan sannan ta nufi É—ayan sashen da Umar yake. Dai-dai lokacin da Safeera ke yowa wajan. Kai tsaye in da Aliyu yake ta nufa ba tare da sun haÉ—u da Amrah ba.

"Hello your excellence fatan komai lafiya".
Cewar Aliyu wanda waya ke maƙale kan kunnensa alamun yana waya.

Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa Muhammad ya ce. "Aliyu ina so kayi min wani aiki".

"Okay". Aliyu ya ce yana mai jiran mai Gov. Musa zai fada masa.

Magana Gov. Musa ya fara yi kamar haka. "Ina son ka bincika min wane ne ya kuɓutar da Lailah harta gudu daga asibiti a wannan lokacin".

Cikin rashin fahimta Aliyu ya ce. "Ban fahimci me ka ke faɗa ba yallaɓai, kamar ya na bincika waye ya taimaka mata. Ita ɗin fa ta riga da ta bar wannan duniya, kuma ko ba komai ita ɗin kamar ƴar uwa take a waje na ko kuma na ce tamkar uwa take a waje na a kan me ya sa za ka ce na bincika waye ya taimaka mata. Gaskiya ba zan iya yin wannan aikin ba sai dai ka saka wani ya yi maka". Yana kaiwa nan ya katse wayar.

Ɓangaren Gov. Musa Muhammad kuwa idan ranshi ya kai dubu to ya ɓaci!, cikin hassala ya ce. "Lallai ma aliyu, mun daɗe cikin harkar nan tare da kai shi ne kuma yanzu ka ke ƙoƙarin juya min baya na san ta yadda zan ɓullo maka".

Kiran wasu daga cikin body guards É—insa ya yi tare da faÉ—a musu cewa su binciko wacce ta taimaka wa Laila ta gudu a asibiti.

Kamar yadda ya umarce su haka suka fice suka fara yawo a gari domin neman wace ce ta taimaka wa mrs Laila Abdullahi.

***************
Bayan Aliyu ya sauke wayan ne ya ci karo da Safeera a tsaye sai binshi da idanuwa take.

Binta ya yi da kallo sannan ya ce. "Wato yanzu ma kin kuma sauya shiga kenen kuma ƙwayar idanunki kin mayar da su yadda duke da sannu da ƙokari kinji".

Cikin rashin fahimta Safira ta dube shi ta ce. "Ni fa ban gane abin da ka ke magana a kai ba".

"Koma dai mene ne ke ki ka sani, maza tawo mu tafi idan kuma baki gama ba ni na tafi na barki a nan". Ya ƙarashe maganar yana mai fice wa daga wajan. Ganin yana ƙoƙarin ya tafi ya barta ne ya sa ta yi saurin bin bayansa.

Suna isa waje suka tadda jami'ai zagaye ta ko ina. Mamaki ne ya kama su. Simi-simi Aliyu ya nufi in da ya ajiye motar sa tare da shiga ciki nan ita ma Safeera ta shiga cikin mota. Tada mota Aliyu ya yi sannan suka bar harabar wajan.

Ɓangaren Amrah kuwa kai tsaye wajan Umar ta nufa. Nan Umar ya shiga binta da kallo yayin da ya rasa a mafarki yake ko zahiri. Ya shiga cikin ruɗani. Su Khairiya kuwa bayan sun gama siyayya ne suka nufi wajan su Umar.

Kallon Umar suka yi ganin gaba ki É—aya yanayin shi ya chanza ya sa Ramlat faÉ—in. "Yahya meya faru?". Ta faÉ—a da alamar tambaya.

Girgiza kai kawai Umar ya yi sannan ya ce. "Babu komai mu tafi". Ya faÉ—a yana mai jan hannun Amrah suka fice daga cikin wajan.

Nan ya ga jami'an da ya kira har sun iso harabar wajan. Sara masa jami'an suka shiga yi a sa'inda suka buÉ—e musu kofofin mota suka shiga. Gaba É—aya yanayin Umar ya sauya ba kamar yadda suka sanshi ba. Binsa da kallo kawai Amrah ke yi ganin dan murmushin nan da yake mata baya yi hakan ya sa ta cikin wani irin yanayi na damuwa.

Tada mota jami'ai suka yi tare da barin wajan baji É—aya.

*****************
Zahra da Mami na fita kuwa suka tarar da ƴan aiki tare da su Gimbiya Saratu da Talatu tare da su Samira a zazzau ne gaba ɗaya sun ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Ƙarasawa wajan su Zahra ta yi sannan ta ce. "Gani na zo me ya faru?". Ta faɗa idanunta a kan Junaid.

Sauke ajiyan zuciya Junaid ya sauke!, kana ya ce. "Maza ki durƙusa ki bawa Samira haƙuri tare da sauran domin yin hakan ne kaɗai zai sa ki zauna lafiya a cikin masarautar nan".

Jin maganar Zahra ta yi tamkar saukar aradu. Ƙasa da kai ta yi yayin da ta ji wani zuciyan ya ce mata kawai ta bawa Gimbiya Saratu da Talatu haƙuri domin a haifa sun haife ta.

Dubansu ta yi kana ta ce. "Shi ke nen tun da abin da ku ke buƙata kenen zan yi. Amma Gimbiya Saratu da Talatu kawai zan bawa haƙuri Samira kuwa laifi ta yi don haka ba zan iya ba ta haƙuri ba".

Miƙe wa tsaye Gimbiya Talatu ta yi sannan ta ce. "To idan ba za ki iya ba ta haƙuri ba muma bamua da buƙatar haƙurin ki, in dai kina son mu yafe miki kuma keda wannan matsiyaciyar Mamin ku zauna lafiya cikin fadan nan to dole sai Mami ta durƙusa har ƙasa ta bawa Samira haƙuri".

Nan take jinin Zahra ya fara tafarfasa yayin da ta ji wani irin ɓacin rai ya ziyarce ta. Nan take ta dubi Gimbiya Talatu ta ce. "A kan me ya sa za ta ba ta haƙuri?, ni ce da laifi ba ita ba, kuma ita ta kawo ni masarauta nan ba ku ba, ya kamata ku san irin furucin da za ku dinga furta wa domin ita ɗin ba sa'ar ku ba ce ba".

Duban Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Aba ke kuwa Zahra wannan ba shi ba ne karo na farko da zan fara basu haƙuri ba wannan abu mai sauki ne. Ki bari kawai na ba ta haƙuri ". Ta faɗa hawaye na gangaro wa kan fuskarta yayin da ta fara yinƙurin durƙusa wa kan gwiwowinta.

Da sauri Zahra ta riƙe ta sannan ta ce. "Aba Mami, sai dai idan bani da rai shi ne kawai zan barki ki durƙusa a wajan nan amma muddin da numfashi na to babu abin da zai sa ki durƙusa mata".

Maida kallonta ta yi kansu sannan ta ce. "Na san Mai martaba bai san duk abin da ku ke yiwa Mami ba to a yau duk zan tona muku asiri domin saina faɗa masa komai". Ta faɗa tana mai yinƙurin fita.

Take suka ci karo da mai martaba a hanyar ta na fita. Hamdala Zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba dama ina so na faÉ—a maka abu ne sai kuma gashi Allah ya kawo ka, dama.......

Zahra ba ya kai ga ta idda maganarta ba suka ji Gimbiya Saratu da Talatu sun fashe da kuka.

Maida kallonsa Mai martaba ya yi kansu Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Me ya faru?".

Cikin kuka Gimbiya Talatu ta ce. "Mai martaba uwar gidan ka ce ta kawo sabuwar Æ´ar aiki take yi mana rashin kunya harda zagin uwata. Sannan kuma uwar gidan ka ta saka Æ´ar aiki ta mari Samira sannan kuma ta zage mu".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai faɗin. "Innalilahi wa innahilahir rajihun, wannan wane irin sharri ne, ku sani cewa ramin ƙarya ƙurarre ne".

Kallon Mami Kai martaba ya yi sannan ya ce. "A'isha maganar su Talatu gaskiya ne?".

Sunkuyar da kai Mami ta yi hawaye na sauka kan fuskar ta. Kallonta mai martaba ya sake yi a karo na biyu sannan ya ce. "A'isha da ke nake fa, na ce maganar su Talatu gaskiya ne ko ƙarya?".

Girgiza kai Mami ta yi tare da share hawayenta sannan ta ce. "Eh gaskiya ne".

Kallon juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da sakin murmushin mugunta.

Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Aba Mami me ya sa za ki É—ora laifin da ba naki ba a kanki?, me ya sa za ki amsa abin da ki ka san baki yi ba? ta ya ya za ki ce da gaske ne bayan kuma sam ba haka ba ne ba".

"Yi min shiru!!". Mai martaba ya faɗa a matuƙar tsawa ce.

Shiru Zahra ta yi tana mai maida kanta gefe tare da dunƙule hannunta na dama kana ta cije leɓenta cikin tsananin ɓacin rai da zafin zuciya.

Kallon kowanensu mai martaba ya yi sannan ya maida kallonsa kan Mami ya ce. "Na yarda da ke A'isha na san ba za ki iya aikata abin da suka faÉ—a ba, don haka ki koma part É—in ki".

Nan take farin ciki ya ziyarci zuciyar Zahra. Jiki a sanyaye Mami ta koma part É—in ta.

Maida kallonsa mai martaba ya yi kan Zahra sannan ya ce. "Ke kuma, tun da ki ka iya É—ora hannunki kan Samira kuma ki ka iya zagin gimbiyoyi dole ki fuskanci hukunci. Don haka hukuncin shi ne dole ki dinga share gaba ki É—aya masarautar nan har na tsawon sati É—aya".

Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin abin da Mai martaba ya faÉ—a.

Nan take Zahra ta durƙusa kan gwiwowinta sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce. "Ranka shi daɗe ka gafarce ni, dan Allah na yarda ayi min wani hukuncin amma banda wannan, na san kai ɗin mai tausayi ne kuma mai fahimta. Don Allah a sassauta min".
Chapter 33 · 0% Book details