← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 59

Sashe 26

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Grandma ta yi tare da janyo Safeera jikinta ta ce. "Aba Zainab me ya sa za ki mare ta?, yi haƙuri jinki jikata, zamu yi maganin ta. Maza ku tawo mu shiga daga ciki.

Shiga ciki suka yi yayin da suka samu guri a parlour kowa ya zauna. Nan suka shiga yin labarai na yaushe rabo. Suna yi suna dariya abun gwanin burgewa. Dubansu mahaifin Aliyu ya yi ya ce. "Me ku ke so a kawo muku?, zansa su Zuwaira su kawo muku".

Nan take wasu kyawawan ƴan mata guda uku suka fito daga cikin kitchen hannun kowannensu riƙe da abinci. Nan take suka ajiye abincin da lemukan hannayensu tare da fara serving ɗin su Daddy.

"Zuwaira ki miƙa wa Safeera nata ta ci". Cewar Abba wato mahaifin Aliyu.

"Tom Abba bara na zuba mata". Zuwaira ta faɗa tana mai ƙoƙarin zuba abinci a plate.

Kawar da kai gefe Safeera ta yi ta ce. "Bana son, ba zanci wannan ƙazamin abincin naku ba".

Kallon ta kowa ya yi cike da mamaki ganin irin hali na Safeera. Abba ne ya ce. "Ke kuwa ki ɗanɗana ki ci za ki ji daɗin sa fa, shi iyayen ki suke ci kafin su tafi ƙasar America, tuwo da miyan taushe gashi ya ji kayan haɗi maza ki sauko m muci".

"Bana so kuci kayan ku". Ta faÉ—a tare da kwanta kan kafaÉ—ar grandma ta ce. "Grandma É—ita ce kawai mai mutunci a cikin ku gaba É—aya baku da mutunci, ita ce kawai ta yi min maraba da zuwa. Ku kuma kamar baku san da halitta ba , karo na farko kunga yarinyar É—an ahalin nan maimakon kuyi farin ciki da hakan sai ku wani yi kamar baku ga mutum ba, hakan me zanci abinci".

Dafe kansa Abba da sauran mutanen parlourn suka yi sannan Grandpa ya ce. "Kiyi haƙuri shalele mun san mun aikata kuskure a gafarce mu ko".

Ƙura mata ido Abba ya yi ya ga suna matuƙar kama da ƙanwar sa Laila.

"Laaa Baba ka ga abin mamaki, ƴar Ibrahim tana matuƙar kama da Laila sosai ku duba ku gani".

Nan take gaba É—aya suka maida idanuwansu kan Safeera yayin da Safeera ta yi baki tana kallonsu a ranta tana cewa. "Wace ce kuma Laila?".

Zumbur Grandpa ya É—ago idanuwansa tare da gyara zamansa a kan wheel chair É—in sa sannan ya ce. "Kada ku sake kawo min maganar Laila a in da nake na ga muku, ita ce silar faÉ—a wa ta cikin wannan yanayin, na tsane ta" .

Shiru Grandma ta yi damuwa É—auke kan fuskarta ta ce. "Allah muna yi masa laifi ya yafe mana ballantana mu Æ´an adam, ya kamata a ce komai ya riga ya wuce mai gida".

******
Da gudu su Khairiya suka fito tare da su Ramlat da Usman. Tsayawa suka yi chakk ganin Umar da yarinyar jeji.

Kallon Amrah Khairiya ta yi ta ce. "Yahya wannan fa daga ina?".

Kallonsu Umar ya yi gaba ɗaya ya ce. "She is your new sister, ina son ku ɗauke ta matsayin ƴar uwarku, bana son naji abu wanda ya saɓa wa hakan ba. Ku kaita part ɗinku ku chanza mata kaya sannan kusa ta yi wanka tare da yi mata kwalliya kunji ni ko. Ita ma daga yanzu a nan zata dinga zama".

"Wow yahya she is so amazing she looks pretty and cute, oh m God green even ne da ita". Ramlat ta faÉ—a tana mai jan hannun Amrah suka shigar da ita part É—in ta.

**************
"Kai ku dakata me ku ke shirin aikata wa?". Zahra ta faÉ—a tana mai ja da baya.

Dariya Æ´an daban suka kwashe da shi sannan É—aya daga cikin su ya ce. "Za ki iya dakatar da mu ne?, muna so ne mu haÉ—a da ke, Æ´ar cika kamar ki kice ba zamu yi miki komai ba". Ya faÉ—a yana mai babbakewa da dariya.

Cikin ɓacin rai Zahra ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku samm bakua daraja mace ne?, idan baku saki ƴan matan nan kun basu haƙuri ba saina yi maganin ku baki ɗaya".

Dubanta ƴan daban suka yi suka ce. "Sarkin yawa yafi ƙarfin sarki, ta kanki zamu fara". Suna kaiwa nan suka sa hannu tare da jan Zahra.

Nan take Zahra ta kurma ihuu!, yayin da ta yi nasarar ƙwace kanta. Daga nesa ta hangi wata ajajjiyar bulala. Da sauri ta nufi in da bulalar take tareda ɗauka sannan ta nufi in da suke. Bata yi wata-wata ba ta fara zuba musu bulala a jiki.

Ihuuu ƴan shaye-shayen suka fara yi suna mai ƙoƙarin guduwa.

"Ina za ku je?, baku tsageru ba, nafi ku tsageranci, shashashu Æ´an iska kawai marasa É—a'a. Saina yi maganin ku, idan gomnati bata É—auki mataki a kan mutane ire-iren ku ba mu zamu É—auka". Da sauri ta yi wa matan alama da su fita daga cikin wajan.

Da sauri matan suka tashi tsaye tare da fita daga cikin kangon suka bar Zahra da Æ´an shaye-shayen.

Cikin rashin sa'a ta ji saukar naushi kan cikin ta. Nan take ta kurma wani azababbiyar ƙara!.

Su Daddy da ke zaune babu zato suka ji Safeera ta kurma wani irin razananniyar ƙara! Mai matuƙar firgitarwa.

Ɓangaren Amrah ma haka ƙara ta saki tare da fusge hannunta daga na Ramlat. Nan take jami'an gidan suka nufo in da suka jiyo ƙaran yayin da shima Umar ya sauko daga kan upstairs da sauri.

"Me ku ka yi mata?".

Girgiza kai kowanensu ya yi ya ce. "Wallahi babu abin da muka yi mata kawai muna cikin tafiya muka ga ta kurma ihuu".

*****
Safeera what's going on?, me ya faru?". Daddy ya tambaye ta.

Kuka Safeera ta fara yi hannunta dafe da cikinta ta ce. "My stomach, ciki na wayyo ciki na!".

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*NI FA ƳAN UKUN NAN LAMARIN KU SAI AN HANKALI🧐😏😏. DA ZARAR ABU YA SAMI ƊAYA SAI SAURAN SUNJI A JIKIN SU🧐. MUJE DAI ZUWA*.

KADA KU MANTA DA LIKING DA KUMA SHARE TARE DA COMMENTS PLEASE DOMIN ALLAH 🙏🙏🙏

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar Jajirtattu)

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣7️⃣▶️2️⃣8️⃣
*_________________________________________________*
Hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Safeera ke birgima s ƙasa tana ihuun cikin ta.

Da sauri Aliyu ya É—auki waya tare da kiran family Doctor É—in su.

ÆŠaukar Safeera Aliyu ya yi tsreda shigar da ita cikin É—aki sannan ya kwantar da ita a kan gado.

Cikin lokaci ƙalilan likitan su ya zo tare da fara duba Safeera. Yayin da gaba ɗaya family ɗin suka kasa zaune sai kai kawo suke a cikin gidan.

*****
Ɓangaren Amrah kuwa. Ɗaukarta Umar ya yi sannan ya nufi part ɗin sa da ita yayin da su Khairiya da Usman suka bi bayan shi.

Yana zuwa É—akin shi ya kwantar da ita kan gado yayin da ya sa su Khairiya suje su haÉ—a mata shayi mai kauri. Fita suka yi suka bar Umar da Amrah a cikin É—akin. Tashi Umar ya yi tare da fita domi ya je pharmacy domin siyo maganin ciwon ciki.

****
Kwashe wa da dariya Æ´an shaye-shayen suka yi yayin da suka dubi Zahra wacce ke kwance cikin mawuyacin hali sannan suka ce. "Ke ba Æ´ar ranin wayo ba, yanzu zamu yi duk abin da muke sonyi da ke ba tare da wani ya dakatar da mu ba". Suna kaiwa nan suka nufi kanta.

Nan take suka ji karan motocin Æ´an sanda. Da mugun gudu suka fice daga cikin kangon yayin da suka bar Zahra ita m É—aya a cikin wajan.

Shiga cikin kangon suka yi tare da matan da suka fita daga cikin kangon É—azu.

Nan suka tarar da Zahra kwance cikin mawuyacin hali.

Kallon Æ´an sandan matan suka yi sannan suka ce. "Yauwa ita ce ta cece mu daga wajan Æ´an daban dan Allah ku taimaka ku kaita asibiti".

"Shi ke nen". Ɗaya daga cikin ƴan sandan ya faɗa. Kana ya saka mata ƴan sanda suka cinciɓi Zahra, basu zarce ko ina ba sai asibiti.

Shigar da ita ciki asibitin suka yi. Nan take nurse's suka fito da gado tare da karɓar ta sannan suka shige da ita cikin asibitin.

Nan take suka fara ba ta taimakon gaggawa.

*********
Bayan su DPO sun isa garin Jigawa ya sa suka wuce magarƙama kai tsaye.

Suna zuwa ya fito yayin ya tarar da Hajiya Binta ta yi tagumi.

Zuwa ya yi daff da ita. Ganin su ya sa Hajiya Binta saurin miƙe wa sannan ta ce. "DPO ina Zahra take?".

Kallonta DPO ya yi tare da ba ta amsa da cewa. "Ƴarki ta gudu daga sjaan mu, yanzu haka tana Kano bamu san in da take".

Gaban Hajiya Binta ne ya yanke ya faɗi!, cikin tashin hankali ta dubi DPO ta ce. "Kamar ya baku ganta ba?, aba DPO kaima fa ka san Zahra amanarta aka damƙa min, mene ya sa baku nemo ta, na dai san aikin ku ne yin hakan. Kuma kai da kanka ka san babu in da ta sani a wannan garin balle a ce garin Kano wanda ba ta ma taɓa zuwa ba sai a wannan karan. Ni dai gaskiya ka sa a nemo ta in ba haka ba zan sa a kai ƙarar ku wajan shugaban ƴan sanda".

Ajiyan zuciya Dpo ya sauke!, sannan ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Binta, ina da tabbacin cewa Zahra za ta iya kula da kanta domin kuwa ba shiru-shiru bace, kai kanki kin san fitinanniya ce ba ta jin magana, ita ce ta gudu daga hannun mu. Karki damu zan saka a nemo ta duk in da take kuma za ta dawo da izinin Allah".

*************
*ƘASAR CHINA*
"Hello MK, da gaske ne cewar matata tana raye tare da Æ´aÆ´anta?".
Chapter 26 · 0% Book details