← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 59

Sashe 44

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Share hawayenta Hajiya Binta ta yi tana mak maida kallonta kan Dpo sannan ta ce. "Ai don saboda ba ƴar ka bace shi ya sa ka ke faɗin hakan, akwai kundin littafin da mrs Laila ta bani kafin ta tafi, ta ce idan Zahra ta kai lokacin da ta mallaki hankalin kanta na ba ta wannan littafin. Kuma gashi Zahra ta kai minzalin da zan ba ta wannan littafin gashi kuma an rasa in da ta shiga. Banason wani abu ya faru da ita saboda idan wani abu ya same ta ba zan yafe wa kaina ba". Ta faɗa tare da miƙe wa tsaye ta shige ciki.

Shiru Dpo ya yi a sa'inda gaba É—aya jikinsa suka yi sanyi.

______________________
Ganin Zahra ta shiga ciki ya sanya Sooraj maida kallonsa kan Junaid sannan ya ce. "Junaid ka sa ido kan wannan yarinyar ni sam ban yarda da ita ba, ina son zan fita naje wani wuri ne".

Girgiza kai Junaid ya yi ya ce. "Tom yaya in sha Allah, amma dai dakarai ne za su kai ka ko?".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a ni kaÉ—ai nake son zuwa bana son kowa ya bini".

Ya faÉ—a yana mai wuce wa wajan parking space, nan take Æ´an aiki suka fara kwasar gaisuwa, yayin da dakarai suka nufo in da yake.

Dakatar da su ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kuyi zaman ku bana da buƙatar ku".

Ya faɗa yana mai buɗe mota ƙirar ferari tare da shiga. Nan take ya zura maƙulli sannan ya tada motar yana mai barin harabar masarautar sannan ya fice daga masarautar baki ɗaya.

Bai zarce ko ina ba sai asibiti.

Lokaci ƙalilan ya ɗauke shi ya isa asibiti.

Ganin motar wanda ya yi parking ya sa likitoci suka fara nufar in da yake.

Suna mai gaida shi. Fito wa ya yi daga motan yana mai amsa gaisuwar sannan ya dube su ya ce. "Where is she?".

Nuni É—aya daga likitocin ya yi masa da cewa tana cikin room.

Nufar wajan ya yi bai tsaya ba har saida ya isa bakin ɗakin sannan ya kai hannunsa kan handle tare da murɗa handle ɗin ƙofan sannan ya ƙusa kai ciki.

Yana shiga ya tarar da ita kan kujerar mara sa lafiya ta yi ruff da ciki sai kuka take.

Nan take idanuwansa suka kaÉ—a suka yi jajir, zuwa ya yi daff da ita sannan ya zauna kusada ita ya ce. "Me ya sa ki ke kuka eh mrs Laila?".

Ɗago da rinannun idanuwanta Mrs Laila ta yi tare da ɗora wa kan Sooraj. cikin dashashiyar muryar ta tace. "Me ya sa ba zan yi kuka ba Sooraj?, yarana duk na rasa su ban sani ba ko suna raye ko Allah ya amshe kayansa. Na rabu da ƴaƴa na tun kafin su san ciwon kansu, yanzu ban sani ba ko suna raye ko A'a, sannan miji na bai damu ta nemi in da suke ba, ƴan uwana basu neme su ba, ni haka tawa kaddarar take". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka.

Furzar da iska mai zafi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kada ki damu na dawo Nigeria ne duk saboda na nemo in da suke, kuma naje chan ne domin neman maganin ki. Zan ƙoƙarta wajan ganin kin samu lafiya sannan anbi miki haƙƙin ki da na yaranki".

ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)

*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️

WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️*
(We stand together)
🤝🤝🤝

بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!

*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣ 3️⃣➡️4️⃣4️⃣
*___________________________________________*
Sooraj ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye. Sannan ya juya da zimmar tafiya.

Saurin riƙe hannunsa Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai Sooraj, ban san da mai zan iya saka maka ba, da a ce ƴaƴana suna nan da na aura maka ɗaya daga cikin su tunda baka da aure".

Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Aba ke kuwa suma ai kamar Æ´an uwa na suke, sannan na sha gaya miki cewa ki daina min wannan godiyar kinji. Ni yanzu zan tafi, zan sa likitocin su cigaba da kula da ke, sannan kuma na manta ban faÉ—a miki ba, akwai wani abun mamaki da ta faru a dawowar nan nawa. Na dawo na ga an shiga wannan É—akin ajiyar sannan kuma sunanki ne password É—in wannan É—akin, amma abin da ya bani mamaki wata Æ´ar aiki a cikin masarautar mu ta iya gano password É—in sannan kuma ta buÉ—e bayan kuma babu wanda ya san wannan password É—in daga ni sai mahallici na".

Girgiza kai kawau Mrs Laila ta yi ta ce. "Zai iya kasancewa kawai canka ta yi bawai ta sani ba, ko kuma wani ne ya faɗa mata. Yanzu dai ya kamata ka tafi, saboda bana son maƙiyana su san cewa ina raye ".

Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, zan tafi yanzu kamar yadda ki ka buƙata". Ya faɗa yana mai kiran likitoci. Cikin mintuna ƙalilan suka bayyana a wajan. Nan ya faɗa musu cewa su cigaba da kula da ita sannan duk abin da take da buƙata su bata ba tare da sun tambayi umarnin sa ba.

Bayan ya gama yi musu bayani, ya miƙe tsaye tare da barin room ɗin sannan ya nufi wajan parking space. Bai yi aune ba ya ga ya taka ƙafar mutum. Da sauri ya ɗago da idanuwansa tare da ɗora wa kan wanda ya taka.

*******
Ɓangaren su Amrah kuwa, basu zarce ko ina ba sai wani babban gida wanda ke cikin layin darmanawa, fitowa Usman ya yi daga cikin mota sannan ya buɗe gate ɗin domin kuwa babu kowa a cikin wannan gida.

Shiga ciki gaba É—aya suka yi yayin da Usman ya koma tare da rufe gate É—in.

Fitowa Amrah ta yi daga cikin mota, kallo É—aya za ka mata kasan cewa samm ba ta farin ciki. Maida kallonta ta yi kan Umar wanda ko inda take bai kalla ba saima fitowa da ya yi daga cikin mota sannan ya shiga cikin gidan.

Jan hannun Amrah su Khairiya suka yi tare da shigar da ita ciki gidan.

Suna shiga suka tadda ƙawataccen parlour mai matuƙar kyau. Zama suka yi a matuƙar gajiye. Yayin da suka miƙe suka bar Amrah a zaune tare da shiga ɗaki suka ɗauro alwala domin gabatar da sallah da ake binsu.

Bayan su gama alwalan ne suka fito daga cikin É—akin tare da nufar inda Amrah take suka ce ta tashi ta yi alwala. Binsu kawai take sannan daga bisani ta kawar da kai daga kallonsu.

Kallon juna Khairiya da Ramlat suka yi mamaki bayyane kan fuskokin su sannan suka ƙara cewa. "Amrah ki tashi kiyi alwala mu haɗa jam'i tare. Jin shiru kamar ma bata san suna magana ba ya sanya su jan hannun ta tare da yi yi mata alwala ba dan tana so ba ta tsaya suka fara nuna mata yadda za ta yi alwala bayan sun gama ne, suka sanya mata hijabi sannan suka ɗauko sallaya daga cikin wardrobe suka shimfiɗa a ƙasa. Sannan suka tada sallah. Kamar yadda ta ga suna yi haka ita ma Amrah ta yi. Sannan ta bi bakinsu da kallo ganin bakin nasu na motsi ba tare da sanin me suke cewa ba.

Haka dai suka yi har suka idar da sallah.

Azkhar suka yi sannan Ramlat ta miƙe tsaye nufi hanyar kitchen domin dafa indomie da ƙwai.

Mintuna ƙalilan ya ɗauketa ta gama girka indomie sannan ta soya ƙwai tare da zuba su a kan indomie.

Chan kan dining ta nufa da abincin a sa'inda ta ƙwalla wa su Umar da su Khairiya kira.

Cikin ƙanƙanuwar lokaci gaba ɗaya suka bayyana a wajan. Zama Umar ya yi kan kujera dining table sannan ya ɗibi abinci sannan ya yi bissmillah ya fara ci.

Daidai wannan lokacin su Amrah da Khairiya ke fitowa. Zaunar da Amrah Khairiya ta yi kan kujera dining sannan ta zuba mata indomie ɗin tare da saka mata chokali a ciki. Maida kallonta Khairiya ta yi kan Amrah sannan ta ce. "Amrah kici wannan indomie, tunda ki ka zo gidan mu kayan marmari kawai kike sha. Bakya cin abinci, kuma ya kamata ki dinga cin abinci wanda za su ƙara miki lafiya".

Kallon abincin Amrah ta yi sannan ta kawar da idanuwanta tare da cewa. "Ni bana ci wannan ƙazamin abun"

Maida kallonsu gaba É—aya suka yi kanta. A sa'inda Ramlat ta ce. "ke kuwa Amrah ki É—auka kici mana".

Kallon indomie ɗin Amrah ta yi tare da buge shi gefe harta kai ga ya zube a ƙasa. Yayin da kwanon da aka zuba indomie a ciki ya fashe.

A matuƙar fusa ce Umar ya miƙe tsaye sannan ya ɗaga hannu tare da wanka mata mari.

Dafe ƙuncinta Amrah ta yi da zallar mamaki.

Mamaki ne ya kama kowanne a cikin su.

"Kinyi hauka ne?, tayaya za ki zubar da abinci bayan wasu suna chan basu samu ba?, ke naga alamun idan mutum ya biki ta lallami kike yi masa iskanci. To ki tsaya ki saurare ni ba zaki yi wannan shashanci da ni ba. Idan nace ina sonki bawai hakan yana nufin kiyi abinda kika gadama ba, dan kawai kinga ana rarrashin ki shi ne za ki dinga yi wa mutane hauka tsewwn!" ya faÉ—a yana mai jan tsaki sannan ya bar dining É—in gaba É—aya.

Ja da baya Amrah ta yi yayin da jikinta suka fara kakkarwa. Kallonta su Ramlat suka yi sannan suka shiga bata haƙuri. Da sauri Amrah ta nufi hanyar waje tare da ƙoƙarin fita daga gidan. Ganin hakan ya sa suka bi bayanta nan suka shiga dakatar da ita, amma ko sauraransu ba ta yi ba.

Da sauri Usman ya koma ciki domin sanar da Umar halin da ake ciki.

******
"Grandma wai wace ce wannan matar da nake gani a photon da Grandpa ya ce a ƙona?".
Chapter 44 · 0% Book details